← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 54

Sashe 40

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dina na kicin tana hada musu abincin dare, a yayin da su kuma suke baje a falon suna aikin takardunsu cikin systems.
Kallo daya Habibu ya yi mishi ya tabbatar yana cikin wani bacin rai mai zurfi, ya yi tambayar duniyar nan amma zurfin ciki irin na Amiru ya hana shi fadar abin da ke damunsa.
Shi kuma Habibun ya takura sai ya ji, daga karshe ya yanke shawarar fada mishi ko da kuwa zai yi mishi dariyar ne, akalla ya samu rangwamen radadin da zuciyarshi ke yi da nauyin da ya danne ta.
Habibu ya yi shiru, can kuma ya ce
"Ban yi mamaki ba. Shi arne wannan (adultery) a wajenshi ai ba wani abu ba ne extraordinary. Sai a yi hattara, Allah Ya kara tserar da mu daga kutungwila da kaidin ZUCIYA.
Amma ni a ganina wannan ba wani abu ba ne da zaka sanya shi a ranka har ya haifar maka da hawan jini, tunda ka san abin da ka aura ai ka aura din. Sannan sabawa mahaifa ai ba abin da ba zai janyo mana ba mu 'yan Adam, don haka sai mu yi fatan Allah Ya kiyaye gaba, Ya sa mu gama da duniya lafiya".
Ya ce.
"Ina son farantawa Mairo Habibu, kamar yadda ta ke haifar min da nau'o'in farin ciki a kullum. Don haka nake ganin zata dawo nan ta karasa karatunta kamar yadda ta faro shi cikin nasara.
Ba zan bari ya kasance ni din na yi silar rabata da burin rayuwarta ba, da tubalin da ka jima kafin ka assasa. Don ko a yanzu na fita na dawo kullum sai na ganta tana bitar littafanta, duk da cewa bata taba yi min korafi akan hakan ba. Ni da na yi mata na ga farin cikinta fiye da kullum, tayi min abinda bata taba yi ba, idan na samu sarari zan dinga lekowa akai-akai insha Allahu".
Habibu ya ji dadin wannan karamci da Amiru ya yi mishi, don shi ma abin yana damunshi, don bai san tsarin sa bane shi yasa tun farko bai neme shi da zancen ba. Don haka a washegari suka nufi Michigan State University tare don gyara mata registration dinta.
Ya rage saura kwana uku Amiru ya dawo, Hajiya ta yi kiran Mairo, ta hadata da wasu jarkokin magani da zuma roba guda da Mairo ba ta san ko na mene ne ba. Ta ce, ta je ta yi ta kwankwada, ta kawo mata jarkokin kafin kwana uku.
Ta bi umarnin Hajiyar don tasan ba zata ba ta abin da zai cuce ta ba, bare wannan magani mai shegen dadi da zaki.
A'ah! Ai tun a washegari ta ji yanayin jikinta na sauyawa, ba abin da ta ke bukata sai dawowar Ameeeru, da yake saukar karfe shidda na yamma za su yi, don haka tun safe tana kicin dinta tana hada abincin tarbar angon nata.
Da taimakon daya daga cikin masu aikin Hajiya da Hajiyar ta bata don su Sabah duk sun koma makaranta, komai ya hadu.
Babu yadda Hajiya ba ta yi ba ta je airport ta tarbo shi ba, amma kunya ta hanata. Wannan na daga cikin halayen yarinyar da suke kara mata kaunarta.
Ta lura bayan kunya, tasan mutumcin kanta, kuma ta iya zama da kowa da wata mu'amala ko ya ya ta hadata da shi.
Tana sassan Hajiya suna sauraron labaran MBC a lokacin da ya iso, daga bakin kofa ya tsaya, ya tokare kofar da hannunshi na dama yayin da na hagun ke dauke da falmarar din ‘Italian suit’ ruwan toka, wato 'grey' da ke jikinshi.
Ya rausayar da kai yana kallonta, da kyawawan idanunshi, ba tare da ita din ta sani ba. Sassanyan kamshin 'miyaki' da ya bakunci hancinta shi ya ankarar da ita tsayuwarshi a bakin kofar n wasu mintuna.
Ji ta yi kamar an yi mata gafara sabida farin cikin dawowarsa cikin koshin lafiya. Ta lumshe ido ba tare da tasan lokacin da ta yi hakan ba. Hajiya tana ta magana, amma ba ta ji Mairo ta bata amsa, sun yi nisa a kallon junansu kamar yau suka fara ganin juna.
Ta juyo don ta dubi Mairo, a sannan ne ta ankara da inda Mairon ta kafa wa ido. Ta ce "Au, ashe mijinki kika gani kika manta da ni nake ta sambatu ni kadai?".
Ya yi dariya ya idasa shigowa dakin. Ita kuwa don kunya sai ta zame ta gudu gidanta ba ta kara lekowa sassan Hajiya ba.
Tana shafa a gaban mudubi, ga dukkan alamu daga wanka ta fito. Daure da tawul iya cinyoyinta. Ya bude kofar ya shigo cikin bakaken pyjamas, tana hango shi ta cikin mudubin a lokacin da ya iso gare ta. Ya dora kai a hankali kan kafadunta ta baya, kyawawan fuskokinsu suka bayyana cikin mudubin a jere, a hankali ya sanyata cikin jikinshi ya lullube da hannayenshi, yana shakan sassanyan 'bathrobb' dinta na ‘rasasi’ yana lumshe ido. Ya ce
"Tell me how much you misses me, ko ba ki yi kewata ba ne Mairo? Don na ga ke har wata kiba kika kara abunki, ni kuwa ina can tunaninki ya hana ni sukuni".
Murmushi kawai ta yi har 'beauty point' din mai kara mata kyau ya lotsa ciki sosai. Ya sumbuci wajen with a very warm kiss, kana a hankali ya soma warware mata tawul din suka soma aikin lada.

***

Wata guda da dawowarshi, suka yi shiri suka nufo Kano don yi wa Baffa sallama, kasancewar a cikin satin ne zata koma Michigan. Su Habiba an shiga makarantar ta nutsu don yanzu Mairon da suke wulakantawa ta zame musu uwargijiya da bazarsu suke rawa.
(To ina ruwan Allah!)
Tuni aka sa Lawan ya gyare musu dakin baki, ya kunna 'burner'. Abinci kam sai wanda suka zaba. Baffa ya ji dadin ganin yanayin da Mairon shi ke ciki, ta cika ta yi bul, ta zama babbar mace, kamar kajin Agric jawur da ita.
Ya tarasu duka ita da Amirun ya yi musu kyawawan nasihohi akan rayuwa, da kuma yadda za a yi a ci ribarta. Ya kare da yi masu nasiha akan muhimmancin riko da sallah akan lokacinta.
“Ita ce idan ta yi kyau dukkan ayyuka za su kyautata”. Amiru na son Baffan Mairo, sabida sauran mazan jiya ne ba na yau ba, irin wadanda kyale-kyalen duniya ba sa gabansu. Ya cika su da alheri duk gidan, a washegari suka nufo Michigan.

Dina ce ta zo ta tarbe su, domin Habibu ya yi balaguro zuwa New-Jersey. Mairo ta rungume 'ya'yanta kamar ta tsaga kirjinta ta sanya su. Suna fada mata,
"Mun yi missing dinki Anti Mairo, da gaske ne da Daddy ya ce anyi miki aure da Uncle Amiru???" Inji Bedi.
Murmushi ta yi, cikin matsanancin nishadi tana shafa kan yaron, amma ba ta amsa musu tambayar ba. Amirun ne ya ji, ya juyo daga maganar da suke yi da Dina ya bashi amsa cikin daga gira.
“yes Muhammad da gaske ne, Daddy is absolutely right! Har ma ta kusa ta kawo wa little Mairo kanwa, nan da wasu watanni kadan”. Da sauri Mairo ta bace a wurin.

A ranar Amiru ya juya Washigton don karasa wasu hidimominsa tare da jaddawa Dina amanar rayuwarsa, wato Mairon da ta dusar da hasken sauran matan duniya baki daya daga idanunshi.
Sun kulle a daki ita da Dina ana labarin bayan rabo. Dina ta kura mata ido ta ce
"Anya Mairo? Jikin nan naki babu bayani? Irin wannan fari da kyau haka sai ka ce mai shafe-shafe? Ko dai kwanan nan za fara goyo ne? Naji Amiru na fadawa yara dazu na dauka wasa yake"
Mairo ta rufe fuska da tafukan hannunta, ta ce "Kai Anti Dina, wallahi ba ni da komi. Karewa ma yanzu haka period nakeyi. Ni fa tunda na je gidan dakina daban nashi daban. Kuma ba sai ana kwana daki daya ne ake yin cikin ba?". Dina ta kyalkyale da dariya ta ce.
"Amirun? To abar kazar cikin gashinta tunda ba kya son a fige ta kada in zama babbar banza".
Ta jawo lokarta ta soma fiddo mata magungunan mata masu kyau da tsada 'yan Indonesia data ke saya tana yi mata bayanin tsarin shan su.
Mairo ta ce
"Maganin mene ne?"
Dina ta murmusa, ta ce, "Maganin basir ne, ke dai ki dinga sha don da alama akwai basir a jikinki tunda ga shi nan duk kin yi fari".
Mairo ta yi dariya. Ta rasa dalilin da yasa kullum Dina ke treating dinta yarinya kamar Little Mairo.
Idan dai wadannan magangunan ne ai tunda ta zo gidan ta ke ganin Dinan na shansu, sai dai ba ta taba tambayarta ko na mene ne ba. Amma yanzu ai ta yi girma da hankalin da zata san amfaninsu.
Daga baya ko me Dinan ta tuna? Ta zaro ido ta ce "Ke! Bani magungunan nan bai kamata ki fara amfani da su ba, sai mun je asibiti anyi checking dinki don ban yarda da ke ba. Mai juna biyu ba ta amfani da irinsu".
Mairo ta bata fuska kamar ta yi kuka, don gani ta ke kamar Dinan na kallon abin da ta ke yi a goshinta. Ta tashi gudu tayi dakinta.
Dina sai ta yi dariya, kuruciyar Mairo da halayenta na alkunya suna burge ta matuka.
Chapter 40 · 0% Book details