Sashe 27
Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mairo na gefe, harde da hannuwanta a kirji. Idanunta kur, akan kofar fitowa gidan, tana zuba idon ganin wace ce wannan Dina, da ta mamaye zuciyar Habibu haka?
Wace ce Allah Subhana Ya yiwa baiwar samun wannan Habibun? 'Yar Katsinawan sai ta fito, kyakkyawar fuskar fal far'a. Sanye da doguwar bakar riga da mayafinta kirar Bahrain. Fara ce, amma ba sol ba, ta ma fi dai-dai da a kirata choculate colour. Mai wadatar giran ido, gashin ido da sumar kai. Ba ta taba ganin mace mai kyawun fata irin matar Habibu ba. Gayun ne ya hadu da jin dadi, ya gauraya da hutu, ya cakude da wadataccen ilmi, sannan kwanciyar hankali da zaman kasar sanyi ya biyo baya. Suka yi wa juna wani irin sassanyar kallo ita da Habibu, sannan ta karaso ta rungume Mairo, tamkar ta tsaga kirjinta ta sanyata don kauna. Wani irin matsiyacin kamshi da Mairo ba ta taba ji ba ya ziyarci hancinta.
"Lallai wasu tun a duniya Allah Ya ke ba su Hurul'eeni". Mairo ta ce a zuciyarta.
Da tana ganin Dinan ce mai sa'a da ta samu Yaya Habibu, ashe shi ma Habibun mai sa'ar ne, don cikin mata dubu, da kyar zaka samu biyu irin Dina. Da tana ganin Nabilah 'yar gaye, ashe Nabilah 'yar dukununu ce. Ba ta gama zancen zucinta ba, tattausan hannun Dina kamar na jariri ya kama nata, ta ja ta cikin gida. Bayan ta bi 'ya'yanta daya bayan daya da kisses da runguma.
Wata dattijuwa ce tsohuwa tukuf, sanye da atamfa super holland zaune a can kuryar kayataccen falon bisa darduma tana lazimi. Da gani babu tambaya, ita ce uwar Baban Dina. Habibu da yaran suka zauna a kujera yayin da Dina da wata yarinya budurwa da alama mai aiki ce suka shiga hidimar fito da warmers, plates, da cokulla. Ba ta katse laziminta ba, shi ma Habibun fita ya yi don samun jam'in sallar la'asar. Mairo tana fashin sallah, don haka suka zauna ita da yaran da Dina suna cin abinci.
Dina ta rasa ina taka-saka-ina-taka-aje da Mairo? Soyayyar Habibu ta shafe ta. Ganinta ta ke tamkar kanwarta ta jini.
Sai wajejen karfe biyar Habibun ya shigo, lokacin Hajiya ta idar da laziminta, suka soma gaisawa da Habibu. Itama Mairo ta duka tana gaishe ta. Dina ta ja ta dakin da ta sauka, ta hada mata ruwan zafi a baf da turarukan wanka, ta ce ta shiga ta yi wanka. Mairo ta ce, "Ai na yi wanka da safe".
Ta yi murmushi, ta ce "Sakewa za ki yi, ita mace so ake ta yi wanka sau uku a rana. Idan hakan bai samu ba, ta yi sau biyu. Sannan na ji smelling din jikinki bai min yadda nake so ba".
Don haka Mairo ta hau wanka, cikin kwami da ruwa mai dumi, da kamshin bathrobb din desire-dunhill mai sanyaya zuciya da ni'imtata. Da sabulun da ko a mafarkinta ba ta taba gani ba, wanda in ka yi wanka da shi, ba sai ka shafa mai ba. Ta ji fatarta har wani santsi ta ke da sheki. Jikinta ya yi laushi tubus. Ta dauro alwala ta fito, ta samu Dina na jiranta zaune a bakin gado.
Ta zube mata kayan shafa da turarukanta, ta ce ta shafa, sannan ta dauko riga da siket masu kauri na Bersace ta ce ta sanya.
Ta zaunar da ita a gabanta ta sa dryer tana busar mata da gashi, sannan ta bi layi bayan layi na gashin ta shafe shi da Indian hemp ta taje ta matse da bound, ta bi jelar ta jere da ribbons kala uku masu taushi. Nan da nan sai ga Mairo ta fito kamar Sushmita Sen. Dina ta yi murmushi ta ce "Maryama, haka kike da kyau kamar Habibu?"
Mairo ta ji kunya, ta sunne kanta tana dariya, ta ce "Anti Dina ai ke kin fi Yaya Habibu kyau, fari kawai ya fi ki".
Ta ce "Allah Ya nuna min ranar da tawa Mairon, zata girma ta tashi kamar wannan Mairon. Kinga yadda na ganki yanzun nan, haka nake so kullum na ganki. Ita mace ba abin da ya fiye mata jikinta daraja. Idan ta gyara shi, to ta gyara martaba da mutumcinta, mijinta zai like mata tamkar kaska, ya ji ba abin da ya ke so ya kusanta a duniya sai ita.
Shi kamshi wata rahma ne da Allah Ya saukar mana mu mata, kuma shi ne babban sirrin rike da namiji. Kin ji ko Mairo?"
Mairo na dariya ta ce "To ai ni ba ni da mijin".
Ita ma ta tayata dariyar ta ce "Zai zo ne, gallele kuwa, ni na gaya miki".
Can dakin baki suka iske Habibu, shi ma ya sake fesa wanka, ya yi shiri cikin T. shirt din DKNY fara sol da ratsin jaja-jaja da wandon jeans kai ka ce saurayi ne dan shekaru ashirin da biyu, babu mai yarda ya aje 'ya'ya uku a duniya, ya bi Mairo da kallo don da fari bai ganeta ba, ya ce "Kai! Halitta!!"
Suka kyalkyale da dariya ita da Dina. Ya soma hararar Dinan cikin wata irin soyayyarta da ta kara ratsa zuciyarshi, ya ce "Shikenan kuma don kin yi kanwa ni kin yaye ni?"
Ta soma yi masa alama da ido, Mairo na jinsa. Itama Mairon juyawa ta yi ta fice a ranta tana ce, 'Ku cinye kanku da soyayyar".
Ai kuwa tana fita ya yi super ya suri Dinan yana cewa "Gaya min wanda ya ce da ke kanwa ta fi miji????"
Mairo wajen Hajiyar su Dina ta koma tana goga goro a magoginsu na tsoffi, da gani ka ga 'yar gatan tsohuwa da da ya hucewa takaicin duniya. Ga wasu mulmulallun awarwarayen zinari a hannunta guda uku, sai walwali suke, tufafin jikinta kadai, sun ishi karamin talaka jari. Ta zauna gefenta ta ce "Hajiya kawo goron in goga miki".
Ta mika mata dankwalelen goron fari sol da magogin ta soma gogawa, in ya taru ta mika mata ta hambuda a baki. Tana bai wa Mairo labarin Dina.
Ta ce "Kin ganta nan, duk cikin jikoki na ashirin da biyar na fi sonta. Sabida halayenta na kwarai da rashin daukar rayuwa da fadi. Babanta shine da na biyar cikin 'ya'ya biyar da na haifa suna mutuwa, shi kadai ya tsaya. Kuma daga shi Allah bai kara ba ni da namiji ba, sai kannensa mata guda biyar.
Ita ce 'yarsa ta fari, sai tarin kanne guda bakwai. Ta kawo Yayanki dalibi da ba shi da komai ta ce ita shi ta ke so ta aura. Da fari ba mu yarda ba, tunda ba mu ga iyayenshi ba, shi kuma ya ce, ba zai koma gida a wancan lokacin ba.
Ya fito neman ilmi da arziki ne sai Allah Ya yi mishi zai koma, don haka muka saduda muka yi musu aure. Da ya ke abokiyar arzikinshi ce ga shi Allah Ya azurta su, da 'ya'ya da dukiya. Allah Sarki, ashe iyayen da ya nema don su huta, kamar yadda nake hutawa a tsufana, Allah bai yi za su mori arzikinsa ba.
Ki saki jikinki, ki kwantar da hankalinki da Dina, zata zame miki uwa, abokiya, kuma Yayar kwarai, kin ji Maryamu?"
Ta girgiza kai, ta ce "Na ji Hajiya, Yaya Habibu ma ya gaya mini".
Dina da Habibu suka shigo, sun jero, tsawonsu daya, takunsu iri daya, sai annuri ke fita daga fuskokinsu, ga dukkan alamu an ci soyayya an koshi. Ta dubi Hajiya da Mairo da ta takarkare sai nika goro ta ke yi, ta yi dariya ta ce "kawa da kawa, hirar me ake yi?"
Hajiya ta ce "Ina ruwanki da hirarmu? Ko mu mun tambaye ki hirar me kika je taya mijinki?"
Habibu ya nitse cikin leather yana amsa waya da thuraya dinsa, cikin wani dan bantan uban Turanci kamar Karl Mad sabida yadda Turancinshi ke fita tar-tar irin wanda Mairo ba ta taba ji ba. A da, tana tsammanin a duniya babu wanda ya iya Turanci irin Uncle Junaidu, ashe Junaid rarrafe yake yi, ga wadanda suka mike suke dabo, suka tsaya da kafafunsu.
Kwanansu uku a Dutsinma suka tattaro suka yo Kano, Mairo dai kamar ba zata tafi ba sabida jin dadin zama da Hajiya, har hawaye ta ke da suka fito za su tafi, Habibu da Dina na mata dariya.
Hajiya ta cika mata Bacco fal da atamfofin edclusibes irin wadanda 'ya'yanta ke kawo mata, don ta dinka, amma ta tattara ta bai wa Mairo. Wannan a jinin Mairon yake, FARIN JINI da shiga zucci. Idan ka zauna da ita yini guda, zaka so ka kwana da ita. Idan ka kwana da ita, zaka so kayi wata tare da ita, idan ka yi wata tare da ita zaka so ka yi zaman shekara da ita, haka idan ka yi shekara da ita, zaka so ka zauna da ita har zuwa karshen rayuwarka.