← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 54

Sashe 47

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy ya sake jinjina kalamanta, yayi mata godiya ya sallameta ta fita ta koma wurin Amiru. Inda aka baro su shida Habibu. Daddy ya dubi Hajiya cikin wani irin fushi da ‘anger’ da bata taba gani daga gareshi ba. Fuskar shi tayi jawur abinki da bafulatani, jijiyoyin kansa sun fito rada-rada, idanunshi sun canza launi daga farare sol zuwa jajaye. Jikinshi na tsuma, tsigar jikinshi na tashi yace
“A’isha! Hanan gaskiya ta fadi ko karya ne?”
Ta juya kai cikin tsoro da tashin hankali, nadama da yin kaico da kai, don bata taba ganin shi cikin wannan halin ba. Tace
“batayi karya ba anyi haka. Sai dai kuskure ne da ajizanci irin na kowanne dan adam. Na tuba Alhaji na bi Allah na bika. Sai dai komai ya faru ne da zuga da taimakon wadannan……….” Tana nuna Nina, Ni’ima da Khalisa.
“Su suke karbo komi a Lagos wallahi ban taba zuwa ba. Don nasan zuwa wajen irin wadannan mutanen haramun ne. Na roke ka, kada ka bari Habibu yaji wannan magana don GIRMA NA ZAI FADI A IDANUN SA don ba iyakarta kenan ba…….”
Cikin nishi Alh. Abdurrahman yace “sai kuma me?”
Ta yarfe hawaye da majina tace
“Na sanya shi ya janye hannun jarinsa daga bankinsu shida Habibu……duk takardun dukiyar shi suna hannu na yanzu, bari inje in dauko…”.
Tana shirin mikewa ya daga mata hannu “bayan Nina, Ni’ima da Khalisa sai kuma wa?” tace “sai mutanen Gaya. Su suke cewa “juya” ce. Don haka ne na kulla auren shi da Hanan don ya samu ‘ya’ya kawai wallahi, amma ba don in raba shi da matarsa ba….. kai shaida ne akan cewa tsakani da Allah ina son Mairo”.
Ya kalli Nina da Khalisa da suka yi tsuru-tsuru, jikinsu sai kyarma yake. Don sun gigice da ganin ‘tension’ din mahaifinsu mai son su da gudun bacin ransu, tareda kyautatawa rayuwarsu tun daga yarinta har girma. Rayyah tace “wallahi babu ruwana……” Sabah tace “wallahi babu hannu na…..” Mami tace.
“ni Daddy da ba a kasar nake ba, wallahi bani da masaniyar komai…….”.
Juyawa yayi gefensa ya fizgo wayar talbijin. Ya soma binsu yana tsula musu. Duka na tashin hankali. Da masu ruwan, da wadanda suka ce babu ruwan su. Yana hawaye yana tafkarsu, yace
“Kun yi asara! Kun kashe auren mutumci da amana da soyayya ta gaskiya!!
Bazan yi muku baki ba. Amma kuji tsoron hakki. Kuje duniya kadai ta isheku, tunda kuma mata ne kuma aure kuke kamar yadda Mairo ke zaman aure.
Sannan abinda kuka yiwa Mairo, kuka sa aka yi mata, zai iya faruwa da kowaccenku. Dan uwanku kuma idan yana da hakkinku Allah zai fitar masa, muddin ya mutu bai yafe muku ba.

Kuma sai kun maimaita wannan magana agaban Habibu, sai Habibu yaji wannan maganar.
Ke kuma Hajiya ki tattara ya-naki-ya-naki ki tafi Gaya, sai na nemeki…….bana bukatar ganin ki a cikin gidana yanzu……”. Kowa a falon kuka yake, yana rokon gafara. Basu kara tsananta kukansu ba, saida suka ji wannan danyen hukuncin da Daddy ya zartas akan Hajiya. Suka rirrike kafafun shi suna bashi hakuri yace
“ni baku yi min komai ba. Wadanda kuka yiwa su zaku nema gafara amma ba ni ba. Sannan bazan taba sanya baki Mairo ta dawo gidan dan uwanku ba. Tunda bakwa son ta.
Ku aura mishi duk wadda kuke so tazo ta cika muku gida da ‘ya’ya. Ko ya mutu, ko yayi rai, na barwa ALLAH! Ku bace min da gani dabbobin banza. Hajiya ina kara gaya miki, kada in dawo in ganki cikin gida na….”.

Ya yarda wayar ya fice, yana share hawayen da suka cika mishi ido.
***

Wasa-wasa sai da Mairo ta kwashe watanni uku cur cikin wannan halin, a lokacin cikin jikinta ya fito sosai, domin ya shiga cikin watanni na biyar.
Rannan daga ita sai Hajiyar Dutsinma a dakin, ta farka daga barci, ta kurawa silin ido, al'amuran suka soma dawo mata tar-tar.
Ta tuna wai Amiru ya sake ta, ba tareda ta yi mishi laifin komi ba, alhalin suna tsaka da son junansu. Bayan ta mallaka mishi duk wata soyayyarta.
Sannan ya auro Hanan, ba ta fita daga wannan bacin ran ba, ya dankara mata saki, ta tabbatar bisa tursasawar Hajiya ne, amma Amirun ba zai taba yi mata haka akan-kanshi ba, ko giyar wake ya sha.
Tana mai sa ran bada jimawa ba za su dai-daita da mijinta ya maida ita ta zauna lafiya da Hajiya Aisha, tunda abin da Hajiyar ta kwallafa rai, har ta tsane ta a kanshi, ga shi Allah Ya bayar.
Sai kuma ta tuno wai an fada mata ya kara kamuwa da ciwon zuciya irin wanda yayi a baya, aka samu rayuwarshi da kyar da taimakon ta. Gashi yanzu basa tare. Kai ita ji tayi ma kamar ance ya rasu! Daga bakin Hajiyar Dina da ba zai taba yi mata karya, ko zolaya ba.
Ta soma kuka a hankali, kukan sabo, soyayya, kauna da kewa. A tsayin zamansu na shekaru takwas, bai taba bata mata ba, sai bisa kuskure. Soyayyar da ya wanzar da rayuwarshi a nuna mata, wani abu ne da ba zai taba kankaruwa daga zuciyarta ba.
Tunda ya aure ta ya haramtawa kanshi sauran mata. Bai kara hada jiki da wata diya mace ba, bayan ita, har inda yau ke motsi. Har kuwa wadda ya aura da auren sunnah. Taji wannan a bakin Hanan ba a bakinsa ba. Duk da matakin rayuwa irin nashi, wannan bai shagaltar da shi daga rudin duniya ba.
Ta tabbata ta yi babban rashin da har abada ba zata mayar da makwafinsa ba.

Ta mika hannu ta shafi kasan mararta, inda babynshi ke kwance, yana wutsil-wutsil cikin koshin lafiya. Ta lumshe ido a hankali, hawaye masu dumi suna zirara ta gefen idonta suna shiga cikin kunnuwanta. Ba ta damu da ta share ba, haka zuciyarta ba ta daina kokawa ba.
A wannan halin Habibu ya tarar da ita. Ya ja kujera ya zauna yana fuskantarta. Ya ce.
"Mairo, Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu..."
Ga mamakinshi sai ta fado jikinshi tana kuka mai tsuma zuciya. Ta ce.
"Yaya Habibu da gaske mun rasa AMEERU?"
Ya ce
"Mun rasa auren shi dai Mairo, da gaske mun rasa auren mai kaunarmu da gaskiya da amana. Amma Ameeru yana nan a raye.
Duk wanda yace dake ya rasu, ya fada miki ne kawai don ya tayar da hankalinki. Ko kuma baki tsaya kin saurara dai-dai ba. Amma yana gida, kwance a dakin ki. Akan gadon ki.
Kwanciyar shi ciwo da rabuwar auren ku ya barni da kewa, da katoton gibi a zuciyata. Wanda mayar da shi wani abu ne da ba zai taba yiyuwa ba. Don haka ki dage da yi mishi addu’a. Allah ya bashi lafiya cikin gaggawa.
To lose a friend like him, will be the GREATEST lose of all losses. To lose a husband like him, is another GREAT loss. (rasa aboki kamar sa, ba karamar asara ba ce daga manyan asarori, kuma rasa miji kamar sa, shima babbar asara ce.) Sai dai mu cigaba da yi mishi addu'a. Allah ya bashi lafiya.
Wannan ne kadai babbar sakayyar da zamu yi wa masoyi irinshi. Amma ba da son ranshi ya sake ki ba.
A matsayinmu na musulmi, ma'abota imani da yarda da kaddara, muna da tabbacin cewa, duk abinda ya faru damu da sanin Allah. Shine mai sanya cuta, kuma shine mai yaye ta. Don haka muna da kyakkyawan zaton Zai tashi kafadar Amiru, a lokacinda ya so. Ya cigaba da gudanar da al’amuran kyakkyawar rayuwarshi. Inda rabon zaku komawa auren ku, to da yardar Allah zaku koma. Amir bai yi haka ba Mairo, sai bisa tirsasawa.
Ya kamo hannunta ya rike cikin nashi, ya ce.
"Mairo mun rasa Baba, mun rasa Inna, amma mun hakura kan ba yadda za mu yi. To haka da muka rasa auren Amiru, zamu yi hobbasar yin tawakkali. Mu ci gaba da jure jarrabawoyin da Ubangiji ke yi mana a rayuwa, har mu cinye jarrabawarmu.
Don haka ki yi hakuri kamar yadda na yi hakuri, iyayenshi da 'yan uwanshi suka yi, kan halinda yake ciki. Kuma Alhamdulillahi yana gane mutane yanzu saidai ya ki asibiti.
Hajiyar Amiru dasu Nina suna can suna ta nemanki, suna neman inda za su ganki su nemi gafarar ki sun rasa. Ta yi nadama/sunyi nadamar abin da suka yi mana.
Yafiyarki su ke nema Mairo. Afuwata suke nema da hawayensu. Sun gurfana kan gwiwoyin su a gabana don na yafe musu. Sannan sun samu Daddy sun bayyana mishi duk abinda suka yi mana, yayi mamaki nima nayi mamaki, ya saba musu sosai kuma sunyi nadama ta gaskiya akan ki Mairo. Yace dasu ai ga sakayya nan sun soma gani tun a duniya, tunda Amirun na neman rasa ransa a kanki. Wallahi Mairo tun bayan tafiyar ki ko kofar gida Amiru bai kara takawa ba, yana gidan ki, daga dakin ki sai falon ki.
Hajiya in kin ganta a halin yanzu dole ki tausaya mata, watanta daya a Gaya ya koreta, kiris ya rage ya saketa saida nasa baki tukunna ya hakura.
Ta ce ki yi wa Allah ki kula mata da abin da ke cikinki. Sabida na gayawa Daddy kina da ciki shikuma ya gaya musu.
Sabida haka ki kwantar da hankalinki, don a samu daidaituwar B.P dinki, don hawan jini hatsari ne ga mai juna biyu, kuma jininki ya hau, don haka ki taimake ni Mairo, kada kema na rasa ki……...bani da Uwa, bani da Uba, sai ke da abinda zaki haifa…."
Hawaye sharrr! Suka zubo daga idonsa.
Ta kai hannu tana share masa, ita ma nata suna zuba. Cikin rishin kuka ta ce.
"Ka daina kuka Yaya Habibu, na yi maka alkawarin zan kwantar da hankalina tunda yana raye".
Ya ce,
"To tashi ki ci abinci, ko dan cikinki ya samu. Bai kamata ki dinga zama da yunwa ba, plzzz... Mairona!".
Ta ce
"To ba ni in ci".

Ya bude kular da ke gabanta, ya zuba mata faten dankalin Turawa, wanda ya ji tsokar naman kaji ya yi lugub. Ya mika mata a faranti, ya cika tambulan da (fresh milk) mai sanyi ya mika mata. Ta karba ta soma ci sosai har tana taune harshenta sabida yunwa.
Chapter 47 · 0% Book details