← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 54

Sashe 44

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Habibu ya yi shiru, domin Amiru ke da kaso 60% wanda hakan ke nufin durkushewar bankin da ya faro da nasara cikin shekaru biyu kacal da kafuwarshi, wanda ke nufin shi kadai (Habibun) ba zai iya 'running' bankin ba.
Ya tabbatar makiya sun shigo cikin al'amarinsu, amma bai ga laèèifin Amirun ba, wanda da gani kasan tursasa zuciyarshi yakeyi, wajen furta kalaminshi.
Ya ce "Idan don wannan ne, ai babu damuwa Amiru. Idan har hakan zai samar maka kwanciyar hankali, ka ba ni kwana goma, insha Allahu komai naka zai dawo hannunka. Sai dai ina so ka samu lauya, wani daban, ba Dina lauyar bankinmu ba".
Ya ce
"Ni ba ni da wani lauya".
Habibu ya ce
"Dole sai ka nemo".
Ya juyar da kai yana kwararar da hawaye, ya ce
"Daga yau ba zan kara neman kudi ba, tunda su din fitina ne. Ta yadda har wasu suke ganin su din (kudi) sun fi mutumci da amana, Ya Allah Ka tsiyata ni……….."
A gaggauce Habibu ya toshe masa baki.
"Kana hauka ne?
Kada 'frustration' (bacin rai) ya sanyaka fita daga imaninka. Ka je ka samo lauya, mu yi abin da zai kwantar maka da hankali".
"Ni na ce da kai hakan kwanciyar hankalina ne?"
"Ba ka ce ba, don haka abar kazar cikin gashinta ba sai an fiffigeta ba".
Cikin satin Habibu, tare da taimakon Barrister Dalha wani abokin aikin Dina daya daga cikin lauyoyin 'CBN' da Barrister Mujahid lauyan 'starling' sun hattama komi na dukiyar Amiru, ta koma hannunshi da sunanshi da sanya hannunshi.
Ya kwashi takardu cikin 'briefcase' ya yi sallama a dakin Hajiya. Kallo daya ta yi mishi ta ga yadda ya zabge, ya yi zuru-zuru sai karan hancin da idandanun kadai, amma hakan bai sa ko kadan zuciyarta ta russuna ba, da dai ta kyale Habibu da kanwarshi su yi galaba a kanta. Tunda sanda ta ke nakudar abinta bayan rainonshi cikin mahaifarta, har wata tara da dawainiyarshi zuwa girmanshi, ai ba su zo sun tayata ba.
Don haka ta kudure sun daina cin arzikin Amiru, kowa ya ci gashin kansa.
Ya zauna a kujerar da ke fuskantarta, kwakwalwarshi na juyawa. Ya mika mata 'briefcase' ba tare da ya iya hada ido da ita ba.

Ta bude ta zaro takardun ciki ta sanya 'medicated glass' dinta tana dubawa daya bayan daya. Ita kanta ta razana da ganin abin da Amirun ya mallaka a 'yan kananan shekarunshi.
Bayan ta gamsu da ingancinsu, ta maida su inda suke tana murmushi, ta ce.
"To ko kai fa?
Ba ga shi ba yanzu sai yasan zafin nema ba ya tashi daga cima-zaune? Yanzu wane kasuwanci zaka soma da wadannan din?"
Ya kalle ta kawai bai yi magana ba. Ta dauka bai ji ba ne, don haka ta sake maimaitawa.
Ya ce ba tareda ya dubeta ba,
"Sadakar da su zan yi".
"Au fushi ka yi, sabida ina yi maka gata Amiru?"
Ya ce
"Ya ya za a yi na yi fushi da ke Hajiya? Ina juya su, kin ce in kawo miki. Na kawo miki kuma ki ce me zan yi da su?
Ban iya wani kasuwanci ba, bayan wanda nakeyi, ni ma'aikaci ne. Aikin banki shi ne wanda na iya tsawon shekaru goma.
A yau kin ce na barshi, don kada Habibu ya samu dan wani abu a jikina, wanda bai taka kara ya karya ba. Bayan kin san duniyar cudarni in cudeka ce, kuma shi ma ba matsiyaci ba ne, yana da rufin asirinshi wanda da kadan ne bai kai nawa ba.
Haba Hajiya! Shekarata nawa da Habibu bai cuce nin ba sai yanzu da muka zama daya?"
Hajiya ta ce
"Rabi (half) kuka zama ba daya ba, sallamamme, bawan mace. Tunda ba ka so ka yi zuciya har kana cewa sadakarwa zaka yi, ni ina so, zan yi maka sadakar, amma ba duk ba. Ranar da tsiya ta isheka ka waiwaye su, nima ina da 'account' din da zan adana maka su su hayayyafa ba Habibu ne kadai ya iya juya sisi ya koma kwabo ba".

Duk abin nan da ake Daddy bai sani ba, don shi ba mazauni ba ne, sannan ko da wasa Hajiya ba ta yi gigin sanar da shi abin da ta yi ba, don tasan bazai goyi bayanta ba. Sai su Khalisa da Nina wadda ke aure a Lagos sune 'yan abi yarima a sha kida, duk suka yi ta tsalle.
Nina ta ce
"Mun gama da wannan, saura 'yar kauyen Gurin-Gawa, don Allah Hajiyarmu ki yi mana waje-road da ita".
Hajiya ta ce
"Ku barni da su, duk na ishe su, ko ba ta yi waje ba, ai ta yi zaman boranci idan na aura mishi wadda zata cika min gida da 'ya'ya".
*****÷
8/6/21, 5:15 PM - Kawata: F
An debi watanni biyu kwarara, Hajiya na tarairayar danta don dai ta wanke dattin ta dake idanunshi, tana kuma nuna kulawarta akan Mairo, wadda ita kuma ba ta san tana yi ba, karatunta kawai ta sa a gaba.
An yi bikin su Sabah tun shekarar da ta gabata, bayan sun kare karatunsu. Don haka yanzu sassan Hajiya babu kowa, daga ita sai 'yan aiki. Watakila hakan ne ya sa ta kwallafa ranta ga son ganin 'ya'yan Amirun, tunda sauran jikokinta iyayensu maza ba za su ba ta ba.

Yau da ya shigo gaishe ta da safe, cikin sakin fuska ta amsa. Bayan sun gaisa ta janyo wata dirkekiyar jarka irin wadda ake zuwa da zam-zam daga Saudiyyah din nan, cike ta ke taf da ruwan rubutu bakikirin da shi ta girgiza ta tsiyayo a kofi ta mika mishi.
"Ungo shanye ka ba ni kofin".
Ya ce
"Na mene ne Hajiya?"
"Maganin sammu da tsarin jiki ne, ko ba zaka sha ba? Idan ka shanye shi duk wani makaru da ke jikinka zai karye, don haka shanye ka ba ni kofin".
Bai yi musu ba ya karba ya soma sha a kyankyame, don kam shi Amiru tun fil'azal mutum ne mai kyankyami matuka, ko (spring water) ba kowanne ya ke sha ba.
Tun yana kyankyami har ya zamo masa jiki. Don ka'ida ne kullum ta Allah ya zo gaishe ta, sai ta cika kofi ta ba shi tsawon sati biyu suna hakan. Ya ji ya fara jin wasu sauye-sauye a zuciyarshi akan Mairo, sai dai ko kusa bai alakanta hakan da cewa rubutun da Hajiya ta ke daddaka masa ba ne.
Yau da yamma da ya dawo daga ofishin Daddy inda ya koma zuwa yana taya shi da wasu ayyukan, sabida nauyin Habibu da yake ji ya sanya alakarsu yanzu ta ja baya.
Duk da cewa shi Habibun a nashi bangaren, ya maida komi ba komi ba, amma Amirun gani yake Hajiya ta riga ta gama tozarta shi a idon Habibu, ta yadda har abada ba zasu koma kamar da ba.
Ya yi sallama Hajiya da ke harde cikin kushin tana sauraron labaran Al-Jazeera ta amsa mishi. Ya samu kujera mai fuskantarta ya zauna. Ya dan zamo daga cikin kujerar yana gaishe ta.
Ta amsa mishi da sakakkiyar murya, can kuma ta ce.
"Anya Amiru, rayuwa zata yiwu da hakan? Ace mutum ya yi ta zama, ba ya tunanin samun dan kansa, duk tsararrakinka daga masu 'ya'ya uku sai masu hudu amma kai ba abin da ya dame ka, sabida idonka ya rufe da son matarka. Alhalin kuma ba zata iya ba ka sanyin idanu ba, sai dai a cika maka masai da kashi, to wallahi bazan yarda da wannan ba".
Ya dago idanunshi a kankance ya dubeta.
"Hajiya mun isa mu ba wa kanmu abin da Allah bai ba mu ba ne? Sannan ba ki san matsalar nan daga gare ni take, ko daga gare ta ba? Don haka bai kamata ki dau zafi akan al'amarin ba, don Allah Hajiyata".
Ta ja dogon tsaki tsiiit!
"To ku je asibiti mana? Ko haka za mu yi ta zama cikin jiran gawon shanu? Ai gara a banbance, don a san matakin dauka".
Da wannan tunanin na maganganun Hajiya ya kwana, har ya soma jin kamshin gaskiya a cikinsu. A shekarunshi ya ci ace shi ma ya aje masu yi mishi addu'a. Har ya soma zargin Mairo ko tana amfani da 'contraception'. Tunda dama ai tun farko ba sonshi ta ke yi ba.
Ya yi gaggawar kwabar zuciyarshi daga wannan mummunan zargin da ta darsa mishi. Ya yarda da matarsa 100% (Azzannu zambun, wa lau kana hakkun), sai dai rashin damuwarta akan al'amarin ma ai abin dubawa ne, bokonta kawai ta sa a gaba, da son ganin kwalayen ilimi, tare da son hango kololuwar biro da takarda.
Chapter 44 · 0% Book details