← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 54

Sashe 25

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Baffa ya ce "Amma Habibu na yi mamaki da ka iya yin wadannan shekarun ba ka waiwayi gida ba, ko gaisuwa ce ai ka aiko mana, idan ba ka zo ba (a lokacin ba kowa ke da wayar hannu ba, sai wane da wane)".
Habibu ya ce "Kuskuren da na yi ke nan, amma kusan kullum ba a rasa masu zuwa Najeriya daga Malaysia. To sai dai ita kanta Maleshiyar na dade da barinta, tun bayan da na kammala karatun digirina na farko.
Dina abokiyar karatuna ce, diyar Ambassadan Nijeriya a kasar Maleshiya. Mun dade muna soyayya, mahaifinta ya so mu dawo gida ayi auren gaban iyayena, na nuna masa ni ba yanzu zan koma gida ba, ina da babban uzurin da ya rabo ni da gida, idan na koma mawuyaci ne Babana ya barni na dawo. Don haka ya tsaya tsayin daka har muka yi aure.
Da taimakon mahaifinta na samu aiki na wucin gadi (temporary) ina yi a wani kamfanin kera takalman fata. Na dade ina aiki a nan kuma na samu alheri yadda ba kwa zato. Daga baya wani abokina Amiru da taimakon mahaifinsa ya yi min hanyar da na samu gurbin karo karatu a Michigan din Amurka, akan kwamfuta da duk abin da ya shafe ta. Ina gamawa ba da jimawa ba na samu aiki a Bankin Barclays reshen kasar Amurka, don haka muka koma can. A can aka haifi Alhaji da Mairo, Muhd ne kadai aka haifa a Kuala-Lampur (Malaysia). To kun ji, don haka bazan dade ba, don wajen aikina suna bukatana, ina so zan tafi da Mairo".

Mairo ta yi azamar dago kai ta dube shi, da gaske ya ke ko wasa ya ke? Babu alamun wasa ko kankani a fuskar Habibun. Shi kuma ya kafa mata ido cike da tsoron, kada ta ce ba zata zauna da shi ba. Shi kam nan duniya bai ga abin da zai sake raba shi da 'yar uwarshi ba, wadda ta rage mishi kwal a duniya. Baffa ya ce, "Anya a yi haka? Ni dai na fi so inyi mata aure, hankalina zai fi kwanciya. In lissafina dai-dai ne shekarunta goma sha takwas cif, aure shi ne ya dace da ita".
Cikin murmushi Habibu ya ce "Ta fitar da mijin ne?" Ya fadi yana kallon Mairon, ta yi hamzarin sunkuyar da kanta. Baffa ya ce, "A'ah, ita ko zancen nan da samari irin na su Ladidi ba ta yi, idan ka ganta ta fita, to muhimmin abu ne ya fitar da ita. Amma akwai wani abokina Alh. Salisu da ya yi min maganarta tun wancan watan na ce ya dakace ni sai na yi shawara da ita tukunna".
Habibu ya ce "Har nawa Mairon ta ke? Ka yi hakuri Baffa ka ba ni ita makaranta zan sa ta, idan ta soma ko ba ta kare ba idan mijin ya fito sai a yi auren, amma Alh. Salisu ai ya yi mata tsufa".
Baffa ya ce "Ni ma abin da na yi la'akari dashi kenan, shi yasa ban baiwa zancen wani muhimmanci ba, sai ka yi mata fasfo ku tafi, Allah Ya sa hakan shi ne alkhairinta".
Habibu ya ce "Amin". Ya dubi Mairo ya ga ta sunkuyar da kai, ba ta dago ba ya ce "Mairo ko ba kya son zama da ni da 'ya'yanki?"
Ta yi murmushi ta ce "Mamarsu zata yarda?"
Shi ma ya tayata murmushin, ya ce "Kada ki damu. Dina mace ce mai fahimta, ga kirki da hankali. Na yi mata kyakkyawar shaida. Ta sanki, ta san labarinki ba tun yau ba. Ta fi ni damuwa da a dauko ki, ina gaya mata akwai lokacin da nake jiran isowarsa ga shi Allah Ya kawo".
Baffa ya ce "Ita tana ina?"
Ya ce "Tana garin Dutsinma, can home town dinsu, gobe insha Allah zan je na dauko ta".
Rahma diyar Hajara ta shigo da kular abinci da farantai ta aje ta fita, Mairo ta matso ta zubawa Habibu, ya karba yana cewa, "Yaushe rabona da cin dan wake?"
Baffa ya yi dariya ya ce "Ai ga Mairo nan sai ta dinga yi maka dan wake, idan matarka ba ta iya ba".
Ya ce, "Tana yi min na fulawa (gudun kurna), amma ba irin shi nake so ba, wannan da ake yi da rogo da kuka shi na fi so, don ya fi sulbi, yafi saukin wucewa a makogaro".
Mairo ta zuba filet daya da yaran ta ja su suna ci, Baffa na bai wa Habibu labarin bayan rabo. Habibu ya kammala ya ajiye farantin, ya tsiyayi ruwa a jug ya sha, ya ce "Na zo da ma'aikata Baffa, gobe insha Allahu za a rushe gidannan a yi ginin zamani yadda su Inna Habiba da sauran yara za su fi sakewa".
Baffa ya yi murmushi ya ce "Allah Ya ba da iko Habibu".
Ya juya ga Mairo ya ce "Je ki share min dakina na zaure, anan zan sauka zuwa gobe, yaran ki kwana da su, ni zan shiga cikin gari wajen tsoffin aminai, gobe idan Allah Ya kaimu sai mu je can immigration maganar fasfo".
Ta ce "Ita kuma Anti Dinan a ina zata sauka idan ta zo?"
Ya ce "Tana da inda ya fi nan ne? Duk nan zamu sauka".
Ta tasa yaran a gaba suka nufi cikin gida. Habiba da Hajara dai duk kunyar Habibu ta ishe su, sakamakon rashin arzikin da suka san suna yi wa Mairo. Ba su taba zaton Habibu zai dawo ba, ga wata irin galleliyar mota da ya iso da ita mai nuni da lallai Habibu ya kama kasa, ga 'ya'ya firda-firda kamar 'ya'yan kajin gidan gona, da gani babu tambaya iyayensu sun gama samun nasibin rayuwa.
Chapter 25 · 0% Book details