← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 54

Sashe 23

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ta kai bakin kofa zata fita, Hajiyar ta kirata jikinta a sanyaye, don daga dukkan alamu akwai abin da ke damun wannan yarinya, ta ce "Har za ki tafi, ba ki gaya min sunanki ba, idan Ilham din ta yi waya in gaya mata". Mairo ta ce "Ki ce mata Maryam ce". "Maryam-Maryam!" Tana ji a bakin su Ilham, amma a wannan karon Allah bai bata ikon ganewa ba. Har yarinyar ta fita, ba ta motsa daga inda ta ke ba, ta dade tana tunanin inda tasan yarinyar. Mai yasa ba ta tambaye ta daga inda ta ke ba? To akan me zata tambaye ta? Don kwaita zo wajen Ilham? Amsar shi ne, don zuciyarta tana sonta. Ta koma falon ta zauna cike da tunani. Sai ana kiran isha'i ta iso gida, Baffa na alwalar sallah a nan kofar gida, ta tube takalminta sannan ta wuce shi, zuciyarta cike da jin haushin dadewar da ta yi. Ya ce "Ban ce kada ki kai dare ba Mairo?" Cikin matsanancin ladabi ta rausayar da kai tace "Ka yi hakuri Baffa, mota ce ban samu da wuri ba". Ya ce "Ni dai duk inda za a je aje ido na ganin ido, amma bana son ayi dare. Idan kin shiga ki turo min Lawan". Ta ce "To". Habiba na kwasar tuwon dare sanda ta shigo, ta dago kai ta dube ta a ranta ta ce, "Kai wannan yarinya da kashin arziki ta ke, kullum ta fita ba ta dawowa haka nan, sai bakin jini har yau babu wanda ya taba sallama da ita, duk kyawun nan nata. Ladidi kuwa kullum idan mutum biyu ba su yi sallama da ita ba, hudu za su yi". Ta dubi Lawan wanda ke bin ledar hannunta da kallo, ta ce "Ka je Baffa na kira". Ya ce "In an ki fa?" Ba ta yi magana ba ta wuce wajen Habiba ta durkusa ta ce "Mama Na dawo, sannunku da aiki". Lawan ya ce "Wani feleke wai 'Baffa', mu 'Baba' mu ke cewa Babanmu, ba wani Baffa ba. Wai mama yarinyar nan ta fara bin maza ne ta ke shigowa gidan nan da manyan ledoji?" Habiba ta ce "Idan ta bi sun ina ruwanka, ko mace ba don namiji aka halicceta ba? Me muka samu ne Mairo? Miko nan in gani". Ta mika mata ledar ta tusa karkashin kujerar da ta ke zaune kada Hajara ta fito ta gani, ta ce sai an raba da ita. Ta dauki tuwon da ta saka mata a wani kwano duk lamba, ta zuba miyar karkashi akai ta mika mata. Ta karba ta wuce daki cike da takaici. Ashe wani takaicin ke jiranta. Tana sanya kai dakin wani mugun karni ya dake ta. Ladidi ta kelaya amai tun daga bakin kofa har bakin katifarsu. Tana kwance a katifa tana barci kamar mushe ba abin da ya dame ta. Ta fita ta dauko tsintsiya da abin kwashewa ta soma aikin aman kamar zuciyarta ta yo waje don bakin ciki. Tuwon da ba ta iya ci ba ke nan sabida karnin da dakin ke yi, haka ta kwana da yunwa. Washegari Ladidi da kanta abin duniya ya ishe ta, ta rarrafa katifar Mairo ta tashe ta, misalin karfe bakwai na safe. Mairo ta bude ido tana kallonta, yawu ya ciko mata baki ta juya bayan kofa ta tsartar ta ce "Zo ki raka ni asibitin don Allah, na kasa gane abin da ke damuna, amma da gaske ba ni da lafiya". Sai Mairon ta ce "Ki fara zuwa ki tambayo mama tukunna, idan ta amince sai na rakaki". Ta ce "Rabu da ita kawai, zo mu fice tana daki". Mairo ta ce "A'ah, ba za a yi haka da ni ba". Ba da son ran Ladidin ba ta fita ta tambayo Habiba za su je asibiti. Habiba ta dubi diyarta ta ce "Bana so ku dinga jerawa ne kada a ga muninki". Ladidin ta kyabe baki, ta ce "Lallai ma Mama, ni ce ma mummunar?" Habiba ta ce "Sai idan ba ku jera da wannan mai kama da aljannun ba". Ladidi ta ce "Ke wannan ya dama, ni da munin nawa dai ai na fi ta farin jini, kin taba jin ko bera ya aiko yana sallama da ita?" Ta ce "Haka kuwa, ku je sai kun dawo". Suna tafe a gefen hanya har asibitin Murtala, Mairo ta yanko mata kati suka hau layi. Suna nan zaune har aka kirasu 7/30/21, 10:24 PM - Kawata: 98 Likitan yana rubuce-rubuce a file lokacin da suka shiga, Mairo ta tsaya ta harde hannuwa a kirji a bakin kofa. Ladidi ta karasa ta zauna a kujerar da marasa lafiya suke zama. Ya gama ya dube ta ta karkashin gilashinsa ya ce "Me ke damunki?" Ta ce "Ina fama da haraswa, zazzabi da ciwon kai mai tsanani, ga wani yawu da yake taruwar min a baki, bana jin dadin bakina". Likitan ya dau abin awonsu ya sanya a hannunta yana sauraro, sannan ya yi rubutu a wata 'yar takarda ya ce, su je laboratory su kawo masa result. Suka fita suka tambayi lab aka nuna musu. Nan aka bai wa Ladidi robar fitsari aka ce ta je toilet ta yi ta kawo. Nan da nan result ya fito suka koma ofishin likita. Ita dai Mairo tunda ta ga an rubuta positibe hankalinta yai matukar tashi. Likitan ya dube su bayan ya duba takardar ya ce da Ladidi, "Ina mijinki?" Ladidi ta ce "Ba ni da aure". Ya kura mata ido na 'yan sakonni ya ce, "Amma you are pragnant,(kinada juna biyu) watanni biyu cif?" Ladidi ta fiddo 'yan idanunta gaba daya suka yi kuru-kuru, wannan bai damu likitan ba ya ci gaba da aikin da ke gabansa bayan ya rubuta mata magani a wata 'yar takarda. Suka fito jikin Mairo har rawa yake, saboda dimuwa da razana, ita kuwa Ladidi in banda kuka ba abin da ta ke, wai likitan sharri yai mata, duk girman kan nan ta sauke shi tana rokon Mairo wai su je wani asibitin a sake dubawa. Mairo ta sa mata ido, ta ce "Wannan asibitin specialist ne, duk Kano daga Aminu Kano sai shi, hakikanin gaskiya suka gaya miki. Don haka ni babu inda zan kuma zuwa". Ta yi shiru hawaye na zubar mata. Ba tausayin Ladidi ta ke ji ba, tausayin Alhaji Abbas ne, bawan Allah, Baffa bai cancanci 'ya'ya irin wadannan ba. Sun kusa Yakasai Ladidi ta ce "Wallahi Mairo duk abin da kike so zan baki, ki rakani a zubar min da cikin, in Baba ya ji wallahi-wallahi kashe ni zai yi". Mairo ta ce "Ni kuwa mai za ki ba ni Ladidi in rakaki a kashe rai? Tukunna ma ni ban san inda ake zubar da ciki ba. Kin bata wayonki! Amma bana tausayinki, Baffa nake tausayawa. Iyakacin tarbiyya da ilmi ya baku, daga boko har na Arabiyyah, ya tsare muku cinku da shanku, da suttura dai-dai karfinshi. Bai cancanci wannan sakayyar daga gare ku ba….." Ta kai gefen mayafinta ta share hawaye, ta fyace majina, ta ce "Ladidi ke kuwa mai ya kai ki ga yin haka? Idan aure kike so mai yasa ba ki tsayar da daya cikin tulin samarin naki kin aura ba? Mai za ki ce da Baffa ranar da ya gane kin yi cikin shege?" Ladidi ta kufula wai Mairo ta ce ta yi cikin shege, ta ce "Kinga malama bana son wani dogon Turanci, idan ba zaki rakani ba ne mu raba hanya, wancan karon ma da aka ce na yi cikin ai nasan inda na je aka kwakule shi. Ko ance da ke kowa ma kidahumi ne, bakauye irinki? Mtsew!!!" Ta yayyaga takardar likitan da takardar maganin, ta ce "Ki je ki gayawa Baffan naki ya yi duk abin da zai yi kada ya barni da rai idan shi ne..........." Mairo ta sanya 'yan yatsu ta toshe kunnenta, ita kuma Ladidi ta tare dan A dai-daita sahu ta shige, ta ce, ya kai ta Sabon Gari. Tana shigowa gida Habiba ta ce "Ina kika baro Ladidin?" Ba tare da ta dubeta ba ta ce "Tana zuwa yanzu". Ta shige dakinsu ta danno kofa. Ta rasa inda zata sa kanta da tausayin Baffa. Ta soma kuka kamar ita ce abin ya faru a kanta. Wani sassanyan kamshi ya doki hancinta, irin wanda ba ta taba ji ba a rayuwarta. Daga nan ta jiyo muryar Baffa yana salati, yana sallamewa. Ta sake saurarawa sosai sai ta ji ya ce "HABIBU? Wa nake gani kamar Habibu?" Tamkar wadda aka cakawa mashi. Ta ji wani kululun bakin ciki ya taso ya soketa a kahon zucci. Amma hakan bai hanata mikewa ta fito ba, don gasgata kunnuwanta. Wani magidanci ne dan kimanin shekaru talatin da takwas, wankan tarwada, mai zarkadeden dogon karan hanci da yalwar idanu farare kal. Da ganin fuskarshi ka ga Malam Bedi, ta wani fannin kuma Alhaji Abbas sak! Yana sanye da kaftan na shadda Getzner kar-kar da ita, baka wul! Dinkin tazarce, sumar kansa a kwance luf baka sidik, kasancewar ba hula a kansa. Da gani babu tambaya, ka ga mutum da ya dama, ya kutsa cikin ilmummuka daban-daban. Wasu kyawawan yara guda uku, maza biyu da mace daya, sai rarraba ido suke na rashin sabo. Mairo dai tana nan rike da labule tana kallonsu, wasu irin hawaye suka zubo mata, ta yi saurin sakin labulen ganin zai juyo sashen da ta ke. Tana ji su Hajara duk suka firfito suna ta karadi da sallallami, ita kuwa ba ta kara lekowa ba. Mai ya dawo da shi cikin rayuwarsu yanzun? Bayan masu bukatarshi sun shude a doron kasa? Mai zai ce, mai zai yi, ya wanke mugun tabon da ya yi mata a zuciyarta? Mairo kuka ta ke tamkar ranta zai fita, ba ta son ganin Habibu ko kadan a rayuwarta. Gara ta bar gidan, kada ace da shi yana da 'yar uwa, mai zai yi mata wanda ALLAH da UNCLE JUNAID ba su yi mata ba? Ta soma harhada kayanta cikin jakarta da sauri-da-sauri, tana yi tana fyace hanci da hawaye duka. Ba ta ankara ba sai ji ta yi Baffa na kwala mata kira daga tsakar gida "Mairo! Mairo!! Ko Mairo ba ta nan ne?" Ta yi bakam, ta ki
Chapter 23 · 0% Book details