Sashe 45
Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta murda kofar ta shigo cikin sallama cikin sassalkar doguwar riga baka sid, kirar Dammam, fararen duwarwatsu na ta walwali a jikinta, sannan ni'imtaccen kamshinta na din-din-din ya doki hancinsa.
A kwance yake 'flat' bisa makeken gadonsu ya lumshe ido kamar mai barci. Har ta zauna gefen kafafunshi ta soma ja mishi yatsu bai juyo ba. Haka nan ya samu kanshi da jin haushinta babu gaira babu dalili. Ta yi kiranshi cikin tattausar murya, amma bai bude idonshi ya dubeta ba.
Karewa ma kara runtse idonshi ya yi, tareda janye kafarshi dake ciin hannunta, don ba ya son ganinta, ba ya son kamshin turarenta.
Ta yi wa kanta kyakkyawan matsugunni a kirjinshi, ji ya yi kamar ta dosana masa wuta. Ya yi azamar angijita ya ce
"Leave me alone, please!"
Cikin mamaki ta ke dubanshi, idanuwanshi sun hargitse kamar ba Amirun nata ba. Ta ja gefe ta zauna jikinta yana rawa, don ko kadan bai taba yi mata magana cikin tsawa irin haka ba, sannan ita a rayuwarta ba ta iya tashin hankali ba.
Zuwa can kuma ya mike ya soma shiri, ya dan juyo a kai-kaice ya kalle ta.
"Ki shirya, asibiti za mu".
Ta yi ta maza cikin sanyi ta ce.
"Waye ba lafiya?"
"Idon matambayi ne".
Abin da ya ce da ita ke nan.
Kamar ta ce, 'to ba zani ba', amma kwarjinin Amirun da kimarshi dake cikin idanunta ya hana. Soyayyar da ta ke mishi wata kaddara ce daga Allah da ita kanta bata san adadin ta ba. Ta yadda ba ta iya fushi da duk abin da ya yi mata. To balle ma bai taba yin ba. Idan haka ne ya dace ta yi mishi uzuri, ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba.
Suna tafe a motar amma ba mai ce da dan uwansa uffan, kowanne abin da yake sakawa a zuciyarsa daban ne da na dan uwansa.
Tunanin Mairo shi ne, shin laifin me ta yi wa Amiru haka da zafi, da har ba zai iya budar baki ya fada mata ba don ta gyara?
Shi kansa Amirun ya rasa laifin da ta yi mishi ya ke ganinta bakikkirin da jin zafinta babu gaira babu dalili. Amma ransa na gaya masa rashin haihuwar tane, yazo wani limit na kasa jurewa. Har suka iso babban asibitin Abuja, kalma daya ba ta hada su ba.
Kai tsaye ofishin Dr. Fredrick suka nufa, Amiru ya ce da shi.
"Doctor mun zo ne yau ka duba mana dalilin rashin haihuwarmu, al'amarin ya fara damuna. Sannan Hajiya ta tada hankalinta, idan ba asibitin nan muka zo ba, ba zata barni na zaun lafiya ba".
Sai a sannan ne Mairo ta cira ido ta dube shi. Yanzu ne ta gano dalilin bacin ranshi. Wato sun fara damuwa da rashin haihuwarta, wanda ita ba ta isa ta bai wa kanta ba.
Dr. Fredrick ya hada su da Gynaec Doctor da za su gani, wato Dr. Ma'u. Bincike iri-iri Dr. Ma'u ta yi amma ba ta gano wata matsala a tare da Amiru ba. Da ta zo kan Mairo, sakamako ya nuna cewa, ita ce bakin mahaifarta yake a tsuke sosai. Idan har tana son haihuwa, dole sai an yi mata aiki, an bude bakin mahaifar.
Ya roki Dr. Fredrick da Dr. Ma'u lokacin da Mairo ta nufi mota cewa su taimake shi su bar wannan sirrin a tsakaninsu, ba ya son Hajiya ta ji.
Dr. Ma'u ta ce da shi.
"Ai ko ba ka ce ba, amana ce tsakanin likita da 'patient' dinsa, insha Allahu ba za a fada mata ba".
Ya yi godiya ya barsu da alkawarin idan sun dai-daita ranar da za a yi mata aikin za su dawo.
Mairo ta shiga cikin tsananin damuwa. Tashin hankali da rudani. Yadda farat daya Ameeru ya sauya mata. Kamar ba shi ba. Babu wannan murmushin, babu wannan soyayyar tashi mai kidimata. Kullum daga fada sai hantara. Duk ta bi ta kare a tsaye, ta soma samun tangarda a karatunta. Amma don zurfin ciki irin nata, ko Dina ba ta taba tunanin fadawa ba.
Hajiya ta samu yadda ta ke so, domin ta janye hankalin tilon danta kanta. Duk abin da ta ce da shi dashi ya ke amfani, jikin shi har rawa yake wajen bin umarnin ta, ta himmatu da yi wa surukarta karfar baka, mai wuyar magani, wadda ta fi kiyayyar zahiri lahani a zuciyar wanda ake mawa.
Duk yadda ya so ya lallame ta su koma asibiti a yi mata aikin amma Mairon ta ki. Idan ya takura mata da nacin maganar sai ta sa kuka. Ga shi shi kuma ba abin da ya tsana irin kukanta da ke soya zuciyarshi.
Ta dage akan cewa, ita Allah ne kawai bai nufe ta da samun cikin ba. Ranar da ya nufa Ya ga damar ba ta zata samu ne.
"Amma Shi Ya ce 'tashi in taimake ka. Sannan babu cutar da Ya saukar ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba.
Idan ke ba ki damu ba, ni ina son ganin dan kaina. Tun da rayuwar ba jiranmu ta ke ba, mu muke jiranta".
Tana so ta yi tsaki, amma kimarshi da martabarshi sun wuce hakan a idanunta. Dole ta maida tsakinta.
"Ni fa babu inda zan je".
Duk inda ranshi yake idan ya yi dubu, to ya baci. Ba ta taba yi mishi musu a rayuwarshi irin na wannan lokacin ba. Ya rasa abin da zai mata YA HUCE... Gaba daya ya soma tunanin bokon da ya barta tana yi ne ya sanya ta raina shi... Wannan ne karo na farko da ya kai kararta wajen Habibu tun bayan aurensu. Habibun ya ce, ya kawo mishi ita.
Daga ita sai Yaya Habibun a babban falonshi, don Amirun da ya kawota bai zauna ba ya wuce ofis wajen Daddy. Dina na kicin tana kacaniyar shirya abinci.
Habibu ya ce
"Mairo me nake ji haka? Wai mijinki bai isa ya sa ki abu ki yi ba?
Idan ke ba kya son 'ya'yan, to shi yana so. Muma muna so, me kike nufi da ba zaki yarda a yi miki aikin ba?"
Ta fashe da kuka, ta ce
"Da da ne ya ce na yi abin da yake so, ai zan yi ne, ba tare da kowa ya ji ba. Amma ni ma yanzu ban san me yake nufi da ni ba. Babu magana mai dadi tsakanina da shi sai hantara. Kuma yadda ya ke nunawa kamar ta karfi yake so na haifo mishi dan, sannan ni gaskiya tsoro nake ji, lafiyata kalau inje a jagwalgwala min mahaifa".
Habibu ya ce
"Likitoci ba za su yi miki karya ba Mairo. Maganar canzawarshi sai ki yi mishi uzuri, yanayin rayuwar kenan, wata rana a sha zuma, watarana a sha madaci! Ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba!".
Da kyar Habibun ya rarrashe ta, ta yarda za su je ayi aikin. Ranar litinin Dr. Ma'u ta yi mata aikin.
***
Tsawon shekara guda har da doriya, babu wani bayani, wato ba abin da ya sauya bayan yin aikin. Babu ciki ba alamarsa.
Dai-dai lokacin da ta kammala rubutun 'project' dinta na kwalin master, sabida kwazon da ta nuna kai tsaye suka ba ta gurbin zama daya daga cikin malamansu, wato 'lecturing' a jami'ar Abuja.
Mairo ta debi kudi masu yawa, ta dankawa Yaya Habibu aka soma ginin makarantar firamare da sakandire a kauyen Gurin-Gawa. Sannan ta dauki sauran gaba daya ta mallaka mishi halak-malak, bayan ta warewa Baffa nashi kason.
Habibu ya saida gidanshi na kasar America da wasu manyan kadarorinsa ya tada kafadar (Habib Bank) wanda ke gaf da durkushewa. Cikin taimakon Allah sai al'amuran suka soma dai-daita. Amma a ranshi ya dai karbi kudin Mairo ne kawai bai ce mata komi ba, sai dai cikin ranshi ya kudurce juya mata zai yi.
***
Hanan Abdulwahab, diyar kanin Hajiya ce, wato Uncle din Amiru da ke garin Gaya. 'Yar kimanin shekaru ashirin da hudu, kyakkyawa ce matuka, kuma tana da irin tsagin su Amiru a gefen hagu da dama na fuskarsu.
'Yan asalin garin Gaya ne su ma, don da Babanta da Hajiya ubansu daya. Mahaifinta tsohon soja ne, wanda ya rike manya-manyan mukamai a aikin soji, har zuwa matsayin da yake kai a yau, wato Major Genaral Abdulwahab Gaya.
Gaba dayan karatun Hanan tun daga firamare har jami'a ta yi shi ne a garin Lagos, inda mahaifinsu ya yi aiki a wancan lokacin. Daga baya da ya yi 'retire' suka dawo garin Kaduna da zama, inda suke zaune a halin yanzu.
Direban Hajiya Mr. Kademi ne ya je ya dauko Hanan daga filin jirgi, wadda ta sauka karfe hudu dai-dai na yammacin ranar ta Laraba.
Hajiya ta yi mata kyakkyawar tarba bayan ta rungumeta tana lale da diyarta. Kamar yadda Hajiyar ta nemi izinin mahaifin Hanan di n kan ya barta ta zo ta yi mata kwana biyu.