← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 54

Sashe 22

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mairo tana tafe tana tunanin rigima irin tata, ya za a yi ta nemi gidansu Uncle alhalin ba tasan komi a kanshi ba? Ace ma ta sani, me zata je ta ce, kuma me zata je ta yi? Wata zuciyar ta ce "Gaida mahaifiyarsa kamar yadda yake gaida naki". Wannan tunani ne mai kyau.
Ta fito daga Yakasai zuwa Bakin Rimi, ta tari tasi ta ce "Galadanchi". Ya bude mata kofa ta shiga.
Ba a fi minti goma ba ya sauke ta a unguwar Galadanchi. Ta fito ta ba shi dari biyun Baffa ya ba ta canji, ta gangara dai-dai makarantar gidan Galadima ta tsaya nan tana rarraba ido, ta rasa wanda zata tambaya.
Daga can gefe wajen masallaci dandazon matasa ne a zaune suna haramar shiga sallar magriba, ba zata iya shiga cikin wadannan samarin ba don haka ta ci gaba da tsayuwa cikin rashin sanin abin yi. Tana nan tsaye wani saurayi ya zo gittawa ta gabanta ta yi mishi sallama, ya juyo ya amsa, ta ce "Don Allah Yayana tambaya nake".
Ya ce "Allah Ya sa na sani kanwata".
Ta ce "Gidan su Junaid nake tambaya".
Ya ce "Junaid? Ya ya sunan maigidan?"
"Gaskiya ban sani ba".
"Babba ne ko yaro ne?"
"Babba ne, don zai girme ka".
Ya yi dan tunani "Kwatanta min shi".
Nan ta shiga kwatanta mishi, ya ce "Ke ko gidan Justice Atiku kike tambaya?"
Kwarai ta taba jin sunan Chief Justice Atiku Galadanchi a bakin Kausar mai rasuwa, (Alkalin-alkalai) na Jihar Kano. Ta ce "Ina jin nan ne".
Ya ce "Mu je na nuna miki".
Abinka da karamar unguwa, kowa yasan kowa. Ya yi mata nuni da gida ginin manyan 'yan bokon da, mai malalen suminti, dakali biyu sun sa gidan a tsakiya, ko ina a share tas ko tsinke babu. Ta yi wa saurayin godiya ta sa kai zauren gidan.
Ashe yadda wajen yake ba haka cikin gidan yake ba, cikin gidan gini ne sosai na zamani, mai ban al'ajabi, sabida yadda aka kwalmada karfe da rodi aka yi irin wannan ginin ba kasafai ake samun irinshi cikin Nijeriya ba. Ko'ina gilashi sai daukar ido yake hatta kofar shiga falon gidan ta gilashi ce. Ta tsaya a kofar falon tana sallama.
Wata dattijuwa da alama mai aiki ce, ta fito tana mata kallon rashin sani. Mairo ta tsugunna ta gaishe ta, ta amsa, ta ce "Yammata wa kike nema?"
Ta ce "Babar su Ilham".
Ta bude mata kofar falon, ta ce "Zauna a nan, Hajiya tana zuwa yanzu".
Ba ta zauna a kujerar ba, a kan wani tattausan kilishi da ke tsakiyar dakin ta zauna. Talabijin na ta aiki cikin tasoshin tauraron dan Adam. In banda kamshin turaren wuta na (Bakhour) ba abin da ke tashi a falon, gauraye da ni'imtaccen sanyin na'urar sanyaya daki duk da sanyin da ake fama da shi kuwa.
Ta daga kai a hankali zuwa gabas maso kudu na dakin. Tangamemen hoton Uncle Junaidu ya yi mata sallama, yana murmushi. Wata matsananciyar faduwar gaba ta same ta, ta kura mishi ido ba ta ko kyaftawa. Dai-dai lokacin da ta ji muryar Hajiyar tana yi mata sallama.
Ta daga kai ta kai dubanta ga mahaifiyar Uncle Junaidu. Nan ta ga inda Junaid ya debo kyau, tsurarsa. Mace ce ma'abociyar zati da kamala gami da gogayya cikin zuzzurfan ilmin boko. A idanunta farin gilashi ne (medicated). A kiyasce zata yi shekaru hamsin. Amma a idaniyarka ba zata fi shekaru talatin da biyar ba.
Ta zauna a kujera fuska cike da annuri, Mairo ta duka tana gayas da ita. Ta amsa cikin murmushi ta ce, "Yammata daga ina? Ban gane ki ba".
Itama Mairon sai ta rasa abin da zata ce. Wata zuciyar ta ce "Akul! Kika ce danta kika zo nema, wannan ba mutumcin diya mace ba ne. Kin zo ki gaishe ta ne sabida Allah, da kuma soyayyar danta da Allah Ya dasa miki. Amma ba don kamun kafar neman soyayyar ba".
Hajiyar ta sa mata ido tana nazarinta, ta rasa inda ta san fuskar. Haka kawai Allah Ya sanya mata kaunar yarinyar a zuciyarta. Duk inda ake neman kyau da nutsuwa, haiba da kamala to wannan yarinyar ta zarce, ga shi da alamunta ilmi ya ratsata ta ko ina. Amma shirun da ta yi mata ya sanya ta diga mata ayar tambaya (kuestion mark?). Ta sake maimaita mata tambayarta "Yammata daga ina kike ban gane ki ba?"
A sannan ne Mairo ta cira kai, wasu irin fararen idanu, gauraye da wani irin blue-blue suka haske Hajiyar, ta yi wa Allah sarkin halitta tazbihi, ta tsarkake Shi, ta tsarkake iko da iyawarSa. Cikin sassanyan sautinta ta ce "Na zo wurin Ilham ne".
Ta ce "Ke kawarta ce halan? Don na ga kamar nasan fuskarki".
Ta ce "Eh". A takaice.
Ta ce "To amma kuwa na yi mamaki da ba ta kawo miki katin bikinta ba, an yi bikinta watanni uku da suka wuce. Suna zaune a Wales din kasar Ingila inda mijinta ke karatu".
Mairo ta ce "Allah Sarki, Allah Ya yi ba zamu hadu ba".
Ta sake juyawa ta dubi hoton Uncle. Ta sake juyowa ta dubi mahaifiyarsa, wata irin soyayya da kauna na sake mamayar zuciyarta. Ba ta ki ta zauna a nan tare da Hajiyar Junaidu ba, tana yi mata bauta, har karshen rayuwarta koda Junaid ba zai aure ta ba. Wannan ita ce kauna ta hakika, wadda ba a samunta a wannan zamanin. Da gaske Junaid ya yi mata nisan da ba tasan ranar da zata kamo shi ba.
Tsigar jikinta ya tashi, ganinta ya dushe, wani duhu ya gilma mata ta daina ganin abin da ke gabanta na wucin gadi.
Hajiyar ba ta lura ba, don a lokacin hankalinta ya tafi ga amsa kiran wayar da ya shigo mata yanzu-yanzu. Ta mike tana gyara lullubinta ayayinda ta fuskanci da Uncle Hajiyar ke magana. Hajiyar ta yi mata alama da hannu ta jirayeta. Sai da ta gama wayar ta ajiyeta akan centre table, ta ce da Mairo "dan jiraye ni ina zuwa".
Ta koma matattakalar da ta fito, jim kadan ta dawo da leda mai tambarin shagon country mall ta mika mata. Mairo ta girgiza kai alamar ba zata karba ba, don tasan ko ta karba rabon su Ladidi ne, dama ace za su gode ne, to a'a, zagi da bakar magana ne zai biyo baya.
Hajiyar ta ce "Ni ba babarki ba ce? Ba zan yi miki ihsani ki karba ba?"
Ta sake kai dubanta ga Uncle Junaid da ke cikin hoto yana murmushi. Sai ta ga kamar ya turbune mata fuska, cikin rashin jin dadi. Ta maido ga dubanta ga Hajiyar, kallonta ta ke tsakaninta da Allah da matsananciyar kauna cikin kwayar idanunta.
Ji ta yi kamar ta kwantar da kai a kafadunta ta yi kukan da ke cin ranta, ta gaya mata matsananciyar kaunar danta da Allah Ya dora mata. Ta ji dumin da Junaid ya ji, a jikin wannan nagartacciyar UWA, ganin hawaye na neman tona mata asiri ta yi hamzarin karba ta ce "Na gode".
Chapter 22 · 0% Book details