← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 54

Sashe 13

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uncle Junaidu ya yi mata halarcin da ba zata taba mantawa ba a rayuwarta. Tare da shi aka yi ta zaman makoki har tsayin kwanaki bakwai, mahaifiyarshi da kannenshi duka ya kawo su sun yi wa Inna Hure gaisuwa. Ranar da aka yi sadakar bakwai ya tura aka kira masa Mairo azure, ya kara yi mata ta'aziyya, ya kara da nasihu masu sanyaya rai da karfafa gwiwa. Ya ce ta daure sati mai zuwa ta dawo makaranta har zangon ya yi nisa ba tareda ita ba.
Ta rantse masa zata dawo amma tana tausayin Innarta, yadda zata barta cikin kewa. Ya ce "Wata rana aure zaki yi Maryama, ke da Inna sai gani da yawo, ita kanta tasan hakan. Don haka ki taimake ni in rike nauyin da marigayi ya aza mani akan karatunki".
Bayan tafiyarsa Mairo da Innarta idan ka gansu gwanin ban tausayi. Tunanin Mairo shi ne, wa zai dinga nomawa Innarta abin da zata ci? Idan wanda ke cikin rumbunsu ya kare? Allah maji kan bawa, washegari sai ga Alhaji Abbas niki-niki da kayan abinci ya kawo musu. Ya kuma ce, wannan nauyin ya dauke shi insha Allahu. Sai a nan hankalin Mairo ya dan kwanta duk da Innar ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Shi ma Alhajin ya yi mata zancen makaranta ta ce, insha Allah karshen wannan satin zata koma.
Hakan kuwa aka yi, ranar litinin ta yi shiri ta koma makaranta. Nabilah ta yi mata ta'aziyyar babanta wanda ta ji a bakin Uncle Junaidu.
Rayuwar Mairo ta sauya kwarai, ta zama babu walwala, akwai shakuwa da kauna mai tsanani tsakaninta da mahaifinta, don haka ta ke jin kanta tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai ta samu kanta da son yin abin da zai debe mata kewa, don haka ta fara tunanin yin RUBUTU.
Tana yi tana gutsirewa ta ajiye, idan ta ji bai yi mata ba. Kamar da wasa, ta fara rubutun labarai cikin harshen Turanci a kalla guda biyar tana yagawa. Lokacin da ta shiga aji biyar na babbar sakandire aka ba ta kallabin 'AMIRA' sabida hidimarta ga masallaci da kungiyar dalibai musulmai da Uncle Junaid ya sa ta. Haka nan ita ce ja gaba a club din Uncle, watau English club.
Kowa yasan Uncle Junaid a Minjibir, yasan shi tare da Maryam Bedi. Mairo ce mai rubutawa club din DRAMA Uncle ya yi gyara a gabatar da ita. Wannan wata hikima ce da Allah Ya yi mata wadda ke bai wa kowa mamaki. Sai dai iyaka kwakkwafinka da sa ido, haka nan so kulla karya da sharri, ba zaka ce akwai soyayya tsakanin Junaid da Mairo ba, sai mutunta juna.

A wannan hutun na zangonsu na biyun karshe a sakandire da Mairo ta zo gida. Ta tarar da ciwon kafar Inna ya yi tsanani. Ko bayan gida ba ta iya takawa sai dai ta ajiye (foo) a kusa da ita. Don haka Mairo ta kara kadewa ta rame, ta kuma soma tunanin jingine makaranta domin Innarta, tun tana tunanin Habibu har ta watsar ta hakura da shi, shi da ya ce shekaru shidda kacal zai yi.
Ta tabbata inda duk Habibu ya ke tunda ya iya ya yi shekaru takwas bai neme su ba, to babu shakka ya manta da su, ya samu sabuwar rayuwa a gaba. Ba zata taba amincewa da cewa wani mugun al'amari ne ya faru da shi ba, tunda kuwa lafiya ita ke buya, amma ba rashinta ba.
Cikin watan January ne sanyi ya yi tsanani, hazo ya mamaye sararin samaniya, wanda duk ya yi kuskuren fita babu shakka gashin ido dana girarsa fari fat za su koma. Mairo ta dawo daga wani chemist inda ta amsowa Inna maganin mura tana tafe yafe da mayafin gyauton atamfa, ta dunkule hannuwanta wuri guda.Tana ta sauri domin ta daura dafa-dukar taliya akan wuta, wadda zata bai wa Innar, kasancewar ba komi ta ke iya ci ba, sai abu mai laushi, kuma mai dan ruwa-ruwa, duka Mairo na kokari a kai. Ta kada ta raya da Innar ta kai ta asibiti, amma Innar ta ki, ta ce, ciwon kafa ba a kanta tsoffi suka fara shi ba.
Ta doso zauren gidansu ke nan ta hange shi, tsaye a kofar gidansu. Sanye yake da farar shirt (Armani) da dogon bakin wandon jeans ya daura jibgegiyar rigar sanyi mai hade da hula bisa. Duk hazo ya ba ta tsararren gashin idonsa, girarsa da sajensa. Mairo ta ce a ranta, Allah Sarki Uncle! Cikin wannan sanyin ya taho tun daga Minjibir sabida rashin komawata makaranta.
Tun daga nesa ta ke yi masa murmushi amma shi fushi yake sosai. Ta kariso cikin nutsuwa, tana karasowa ta russuna tana gayas da shi ya ce "Ni bana son wata gaisuwarki, kawai shiga ciki ki hado kayanki ki zo mu tafi".
Ta girgiza kai kamin ta wuce cikin gidan ya bi ta a baya. Ta fara da sauke tukunyar daga kan wuta, kana suka karasa dakin Innan da sallama. Shi kansa ya girgiza da ganin ramar da Innar ta yi, tana kwance bisa katifar auduga ta amsa sallamar su. Nan ya gano amsarsa ta rashin komowar Mairo makaranta.
Jikinsa ya yi sanyi, ya daga manyan idanunsa ya dube ta suka yi wa juna kuri da ido.

Wani irin tausayinta ke ratsa zuciyarshi, wani sabon feelings ya shiga ratsa kowannensu. A yanzu kam ji ta ke ba ta da kowa sai Uncle, babu wanda ya damu da rayuwarta sai shi. Duk da Alhaji Abbas na iya kokarinshi akansu. Ta sauke kwayar idonta kasa a hankali, hawaye na disa bisa tafukanta. Ya sauke nasa idon akan Innan cikin matsananciyar damuwa, ya ce "Sannunku da jiki Inna, amma ya dace ki daure yanzun nan mu tafi asibiti".
Ta ce "Kayya Junaidu, wadannan kafafun bana jin za su kuma takawa a doron kasa. Akwai likitan da ya isa ya raba tsoho da ciwon kafa? Sai Allah!"
Ya ce "Inna ku daina fidda rai da rahmar Ubangiji, babu ciwon da Allah Ya saukar, ba tare da ya saukar dashi tare da maganinsa ba".
Ta ce "Ai ana shan maganin Junaidu. Watakila abin da nake gudu ne, dole sai ya faru…….."
Cikin matsananciyar damuwa ya ce "Wane abu ne kike gudu Inna?"
Ta ce
"Zaman Mairo da Iyalan Abbas". Daga haka ta yi shiru.

Daga shi har Mairo su ma shirun suka yi. Mairo ta rasa dalilin da ya sa Inna ta tsani iyalan Alhaji Abbas, abin kam ya wuce na cewa wai don sun so su dauke ta ne. Watakila dai akwai wani boyayyen abun don yadda ba ta sonsu ba ta shiga shirginsu, haka su ma.
Tun tasowarta ba ta taba ganin wata cikin matan Alhaji Abbas a gidansu ba, haka ita ma Innar ba ta taba zuwa ba. Ita duk ba wannan ya dame ta ba, illa samun lafiyar Innarta. Ba ta son jin irin maganganun da Innan ke yi a kullum suna kara tayar mata da hankali.
Junaid ya yi musu sallama ya tafi, washegari sai ga shi ya zo da likita har kauyen wanda likitan gidan su ne. Ya dade yana duba kafafun Innar, ya rubuta magunguna masu inganci da allurai ya ba Junaidu.
Ranar litinin ya dawo da magungunan ya nunawa Mairo tsarin shan su dalla-dalla. Ya je babban dakin shan magani na kauyen ya tattauna da nurse da kullum zata zo har gida ta dinga yi wa Innan allura.
Cikin sati guda kafafun Inna sun yi kyau, har tana iya zagayawa bayan gida. Ranar wata alhamis da daddare suna kwance ta ce "Mairo”, tace “Na’am Inna” “ ni ko ba don wani abu ba, da na ce Junaidu YA AURE KI".

Gaban Mairo ya fadi damm! Ta dade bata saisaita tunaninta ba, cikin dabarbarcewa ta ce "Inna ke ko mai yasa kika yi wannan tunanin?
Uncle Junaidu Yayana ne, yadda na dauki Yaya Habibu haka na dauki Uncle, babu wani tunani na daban ko ya ya game da shi a zuciyata.
Allah ne Ya hada mu, Ya hada zumunci mai karfi a zuciyoyinmu. Babu wani abu makamancin wannan, sai mutunta juna".
Inna ta yi murmushi ta ce "Wannan zuciyar Mairo ce kike gaya mini, ba ta Junaid ba. Kin taba ganin inda namiji zai yi ta wahala da mace da iyayenta babu gaira babu dalili? Idan kin ga kare na sunsunar takalmi, wallahi dauka zai yi. Har yanzu ke yarinya ce da sauranki. In gaya miki gaskiya na hango miki abin da ke ba ki hango ba, cikin kwayar idon Junaidu.
Na hango miki abubuwa da dama, wadanda a shekarunki bazaki iya hango su ba. Babu komai cikin kwayar idanunsa sai sonki da kaunarki, ke ma sai dai ki karyata zuciyarki da gan-gan, amma kina son Junaidu. Adadin soyayyarka da mutum, yana da nasaba da yawan ambatonsa. To gaya min tun haduwarki da shi, wace rana ce ba ki ambace shi ba?
Ni ba wani abu na ce ba, kawai ina gano miki dacewar hakan. Ina gano miki mutumin da zai rike ki da kauna ta gaskiya, har zuwa karshen rayuwarki. Wanda kuma shi ne wannan Junaidun. Duk runtsi, duk wahala da tsanani kada ki bari a rabaku. Zan iya rantsuwa in fada miki Junaidu sonki yake yi, idan kuma ba ki yarda ba, ki jira LOKACI ya fada miki……."
Cikin gundura da zancen ta ce "Na ji Inna, amma don Allah don Annabi ki rufa min asiri kada ki ce wai ya aure ni, ai kin zubar min da aji, sai ka ce wata wadda kike neman yadda za ki yi da ita? Ni kam gare ni har gobe Uncle Junaidu Yayana ne".
Inna ta yi murmushi ta ce "Neman yarda zan alkinta rayuwarki nake yi mana, ga shi kuma ina hango inda za a alkinta min ke".
Ta ce (kamar ta yi kuka), "Ni dai don Allah Inna ki bari……..".
Ta ce "Na bari, amma wata rana idan kina shayar da jaririn Junaidu, ki tuna na gaya miki Junaidu na sonki, tun ba ki mallaki hankalin kanki ba".
Ta yi narai-narai da fuska, ta ce "Yanzu don Allah Inna ba zaki bar zancen nan ba?"
Ta ce "Na bari".
Chapter 13 · 0% Book details