← Book details Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 54

Sashe 49

Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Habibu ya cika alkawari, ya sake diban Amir da Habib da Esta ya zuba su a mota zai fita da niyyar kaisu office din Amiru suyi sallama kamar yadda yayi alkawari. Yana kokarin tada mota Amiru na sanyo hancin motarsa ‘camero’ cikin get din Habibun. Don haka Habibun ya dakata har ya bude motar ya fito.
Ya karbi ‘ya’yansa ya soma ‘kissing’ kamar bazai bari ba.
Daga can saman bene Mairo ta yaye labulen dakinta don iska ta shigo. Nan ta hango su. Ta kurawa Amir ido. Bayan muguwar ramar da yayi, ya bar lallausar kasumba mara tsari ta cika fuskarshi, abinki da mai yawan gargasa. Sannan ya saya kwayar idon shi cikin ‘dark-spaces’ wanda ya hana mata gano halin da kwayar idanun shi ke ciki.
Karan hancin ya kara fitowa, zirit, kamar karas. Wani irin so na fizgarta. Ta saki labulen a hankali ta koma da baya ta fada a gadonta. Tana mai fidda numfashi da sauri-da-sauri. INAMA ACE…….hannun agogo zai dawo baya???
***

Washegari suka koma Malaysia. Mairo ta fara karatunta cikin nasara, tana barin yaran a gida wurin mai rainonsu da yake an fara ba su madara. Kafin su cika watanni tara suna gudunsu ko'ina, musamman Alh. Abdurrahman ya bude mata 'account' a nan ‘Kuala-Lampur' duk wata yana sako mata makudan kudi na fita hankali, don lalurorinta da kula da ‘yan jikokinsa.
Bayan kuma ba abin da Ambassada ya rage su da shi, ga na Yaya Habibu. Gaba da baya gata ya lullube Mairo da 'ya'yanta, abin sai godiyar Allah.
Shekaru ukku cif, wadanda suka yi dai-dai da cikarta shekaru talatin a duniya, da kwalin digiri, master, da digiri na kololuwa.

Dr. Maryam Muhammad Bedi, ta tattaro ta dawo gida Najeriya a garin Abuja, zuwa lokacin Habibu ya yi ficce, bankin ‘Habib Bank’ ya samu habaka zuwa 'branches' a dukkan 'thirty six states' da muke da su a gida Najeriya, kamar yadda Amiru Abdurrahman ya yi fata. Yau ga ci gaban ya samu, ba tare da Amiru ba.

A wannan ranar da ake (ten-year anniversary) na cikar bankin shekaru goma da kafuwa, Habibu kuka yake, maimakon ya yi farin ciki.
A yayin da al'ummar taron suka dauka kukan farin ciki yake yi, amma shi kadai yasan dalilin kukansa, wanda bai wuce na alhinin samuwar cigaban shikadai, ba tare da Amiru ba.
A kalaminshi na karshe, bayan ya yiwa mahalarta taron godiya mara iyaka. Ya ce,
"Ya tafi ya bar bankin da kewa, bayan shi ya kirkireshi. Ya bar bankin da babban gibin da har gobe bai cike ba. Na kuma tabbata har abada ba zai cike ba. Sakamakon dumbin ALHERINSA gare ni. A yau na tashi daga mamallakin ‘Habib Bank’, na kyautar da shi ga 'ya'yan AMEERU ABDURRAHMAN GAYA".

Amiru ya daga ido yana kallon shi, extremely puzzled! To haka Alh. Abdurrahman. Ashe wannan shine kudurin da Habibu yace yana dashi kenan akan bankin, ya ki yarda amaida hannun jarin Amiru cikin bankin?
Ya sanya hannu cikin takardu, lauyoyi suka diba, su ma suka rattaba hannu. Sannan ya ce,
“as a servant, zan ci gaba da juya musu dukiyarsu har zuwa girmansu”.
Hajiya ma ta dauko duk takardun dukiyar Amiru dake tare da ita, ta danka mishi. Ya hada dana wajen Habibu ya adana a bankin. A wannan ranar Habibu yayi kuka, kawai sabida tausayin AMEERU. Don gabadaya rayuwarshi ta canza ‘completely’ ta zama ‘no meaning…’ kamar yadda ya fadawa Mairo a baya.

“My life has no meaning......idan ba tareda ke ba”.
***

Habibu ya watsa mata takardun neman aiki, a manyan jami'o'inmu, tun daga Ile-Ife, Ahmadu Bello, Nsukka, Bayero, Lasu da sauransu, ba don neman kudi ba, sai don al'ummar Najeriya su amfana da ilimin da ta wanzar da rayuwarta tana nema, don su amfana.
Ba da jimawa ba jami'o'i har biyar suka dauke ta, ciki kuwa har da jami'ar Abuja, wadanda ta bari a baya. Amma ta zabi BAYERO domin a ganinta al'ummar Kano su ne al'ummarta.
Habibu bai takura mata da zancen aure ba, ko tayin ta koma gidan Amiru. Sai dai shima yana ganin lokacin yayi daya kamata a maidawa Amiru matarsa sabida yadda zawarawa manya-manyan kusoshi ke yi mishi rubdugu, a gida ne ko ofis. Alh. Abdurrahman ya fara tsawatar mata da cewa, ba zata koma Kano ba har sai ta fidda miji ta yi aure.
Sai ta sa musu kuka tana rokonsu, kada su kara yi mata zancen aure, idan ba so suke ita ma CIWON ZUCIYAr ya kamata ba. Me zata yi da wani da namiji ba Amiru ba? Me zata nema a jikin wani namiji bayan Amiru? Amiru yasa ta raina sauran maza, ta yadda har basa burgeta, duk ilminsu da mukamin su kuwa.
Gashi da alama Daddy baya son komen nasu. Tunda koda wasa bai taba furtawa ba. Ya kama Mairo da Habibu ya rungume kamar shi ya haife su, ya jibanci dukkan al’amuransu, amma baya ko son kallon Mairo da sunan matar Amiru. Itama kuma tunda hakane bazata taba nuna tana son komawar ba, koda hakan na nufin ta auri wani ne ba shi ba!
Alh. Abdurrahman ya ce,
"Aure ya zama dole Mairo, domin shi ne cikar kima, mutumci da darajar diya mace. Duka wadannan kwalayen naki aikin banza ne idan babu aure".
Ta yi masa alkawarin su barta ta fara aikinta, a hankali za ta zabi wanda hankalinta ya kwanta da shi. Ya so ya karbe yaran, amma ta roke shi ya bar mata, zuwa wani dan lokaci kalilan, don suna debe mata kewa.

Gida guda suka bata cikin 'new site', suka tare ita da 'ya'yanta da mai rainonsu, mai suna Lami. A lokacin Lawan da Ahmad 'ya'yan Baffa suna karatu a Bayeron, sai suma suka dawo gidan suna zaune a baskwata.
Baffa yana zuwa duba su akai-akai, su ma suna zuwa idan sun sami lokaci. Mairo ta fara 'lecturing' a 'department of sociology' cikin nasara da sanin makamar aiki. Ta sanya yaranta a 'staff-school' kullum su Lawan suna kaisu su dauko su, da yamma kuma su kaisu islamiyya da ke nan cikin 'New-site'.
Ta dade da fara rubuce-rubuce tun tana Malaya akan fannin da ta ke karantarwa, wanda ya kaita ga matakin zama 'proffessor' cikin dan lokaci kalilan.
Kyawunta, zurfin iliminta, sakin fuskarta da yawan taimakonta ga dalibanta, ya sanya ta zamo abar so ga dalibanta. Sai dai fa kowa yana bin kwakkwafi ya yi mamaki idan aka ce ba ta da aure. Sukan ce kyakkyawar mace kamar wannan ace ba ta da aure, ai abin mamaki ne sosai. Sannan kallo daya zaka yi mata ka tabbatar ba da wannan aikin ta ke cin abinci ba. Tana dai yi ne don ra'ayi, amma ba don neman wani abu wai shi 'kudi' ba.

Proffessor Maryam Muhammad Bedi, ta zamo daya daga cikin malaman da ake ji da su a jami'ar Bayero, ko sabida karyayyen harshenta na Turawan America zallah. Don haka da yawa suke bin kwakkwafi akan rayuwarta, har su san inda ta samo wannan 'background' din. Wani dalibinta ya soma rubutu a kanta, sai dai duk yadda ya so ya ji tana da aure ko ba ta da shi, ba ta bada wannan damar ba.
Dr. Mairo ta shiryawa dalibanta masu fita a wannan shekarar 'conference' mai taken, “YADDA ZA A GYARA AL'ADA TA YI DAI-DAI DA ADDINI” Wanda take so Mai girma sabon V.C ya halarta. Don haka ta je ta nemi 'appointment' na ganin V.C a ofishinsa. Aka sanya ta cikin jerin wadanda za su ga V.C a safiyar washegari.
Da ta dawo gida ta tarar Lawan ya dawo da su Habib, Amir yana kwance shiru cikin kujera ba kamar yadda ya ke ba. Ta dora hannu a kanshi, zafi rau, Lawan ya ce.
"Amir ba ya jin dadi tunda safe".
Ta ce
"Za mu je asibiti da safe, idan na ba shi 'paracetamol' zazzabin bai sauka ba".
Ta dauko 'paracetamol' cikin 'first-aid box' dinta ta ba shi da dan kankanin cokali. Har zuwa washegari zazzabin bai sauka ba. Ga shi kuma tana da 'appointment' na ganin V.C, don haka ta sa yaran a bayan mota suka nufi cikin makaranta da zummar idan ta ga V.C sai ta wuce da su asibiti, don mawuyaci ne daya ya yi ciwo dan uwansa bai kama ba.
Ba ta barsu a mota ba, sanya su ta yi a gaba suka soma taka matattakala wadda zata sada su da ofishin V.C.

Mutum biyu ne a gabanta, sai da ta jira suka fito, sannan ta kama hannun Habib da Amir suka sanya kai cikin ofishin, bakinta yana mai furta sassanyar sallama.

Ya juya baya yana zakulo wasu takardu cikin loka. Idanunshi saye cikin farin gilashi, sanye cikin farar shadda 'excelsior' dinkin Muhammed Abacha. Hular kanshi na aje bisa teburinshi.
Gaban Mairo ya yi wani irin mugun faduwa, takardun da ke hannunta suka kwace suka watse a kasa. Amir ya tsugunna yana tsince mata. Shi kuwa Habib tattakawa yakeyi da cambos dinsa.
Ko mutuwa ta yi ta dawo, ba zata mance surar UNCLE JUNAID ba, wanda ke tsaye nan a gabanta. Sai dai wannan Junaidun, ya sha ban-ban da wanda ta sani shekaru goma sha biyu a baya. Wannan cikakken magidanci ne, da yasha gwagwarmayar rayuwar neman ilmi cikin fanninnika daban-daban, ba dan saurayi Junaid Galadanci ba.
Duk da alamun shekaru da suka hau kansa, har yanzu yana nan a Junaidunsa da ta sani, ma'abocin zati da kamala, gami da kwarjini bayyananne daga Sarkin halitta. Ta rasa cikin halin da ta samu kanta, rudewa ce ko gigicewa ce? A'a, ko kuwa gaba daya makuwa zata ce ta yi?
Ta juya da baya–da-baya zata bar ofishin, ya juyo a hankali ya dubi mai shigowa.

"Mariama!"

Maironshi da a kullum ta ke zuwa a farke, ko cikin mafarkinshi. Mairon da dai-dai da rana daya cikin shekaru goma sha shidda, zuciya ba ta taba hutawa da kaunarta ba. Ruhi bai bar mafarkinta ba, haka tunani bai taba kuskuren manta ta ba.
Ya dago Habib ya dauke shi tare da kama hannun Amir ya zauna a kujerar da mutane suke zama don ganawa da shi. Cikin wata irin kassararriyar murya, ya ce.

"Ya ya za ki koma? Ko ba ke ce 'Proffessor Maryam Bedin ba?"
Chapter 49 · 0% Book details