Sashe 2
Abari Ya Huce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dina ta katseta "akwai hanyoyi da yawa da zaka sakawa mutum Alherin da yayi maka ba dole sai ta hanyar aure ba. Misali shine ki dinga bin shi da kyakkyawar addu'a ba tareda shi din ya sani ba. Wannan addu'ar Ubangiji yayi alkawarin karbar ta Mairo. Kada ki yi mamaki zuwa yanzu shi Junaidun ya samu wadda yake so ya aura ya manta da ke.
Ni na kasa gane kan wannan soyayya da kike yiwa Junaid maras dalili. Kin ce bai taba cewa yana son ki ba! Kince ba kuyi alkawarin aure ba! Kince ya san gidan Baffa amma bai nemeki ba! To Mairo gaya min wace hujja gareki da zata tabbatar da cewa yana son ki?
Bakisan akwai masu taimako sabida Allah ba? Ba don a aure su ko a saka musu da soyayya ba? Haba Mairo, kiyi tunani mana, kiyi amfani da hankalinki, ki so mai son ki a zahiri da badini. Kiyi aure saboda Allah da raya sunnar Ma'aiki amma ba don abinda zuciyarki ta afu a kai ba.
Ina tabbatar miki Amiru in kin nutsu, kin bude zuciyarki a hankali zaki so shi wallahi har ma fiyeda son da kike ma Junaid. Iyakar soyayya ta gaskiya kin yiwa Junaid, ko baki aure shi ba Allah ya shaida! Yayi alkawarin sanya masoyan gaskiya da suka mutu ba tareda sun auri juna ba a gidan aljannah. Ina tunanin Junaid yayi abin nan ne da hausawa ke cewa ABARI YA HUCE SHI KE KAWO DA RABON WANI!"
Ta dubi Dina da sauri har tsakiyar idanunta tace.
"Idan hakane Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana so na, furtawa ne baiyi ba kamar yadda _Inna ta_ da Nabilah ke cewa???"
Gyada kai Dina ta yi. "EH, yana son ki, amma ya bari YA HUCE! Don kuwa a zahiri babu wata mu'amala ta mutunci da tausayi tsakanin mace da namiji sai 'SOYAYYAH'. In ma mutuncin ne da farko, to daga baya rikidewa yake ya koma soyayya. ...
Ke dinnan Mairo har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yimawa ba soyayya ba. Amirun shi kike so da gaske; na gani a kwayar idon ki, na gani a gangar jikinki. Kina jin abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle Junaidun? Kina neman Junaid ya aureki ne don ya tallafi rayuwarki a wancan lokacin da kike neman matallafi ido rufe, amma ba don kinsan hakikanin me aure ya kunsa ba.
Mairo kinaso ki ramawa Junaid halaccin da yayi miki ne ta hanyar 'aure' don da shi kika saba, ya sanki, kin san shi, a tunanin ki wannan shine karshen soyayya, to ba shi bane! Soyayyar aure daban take, Allah ke hada ta, kuma bata fassaruwa.
Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shine tsakaninki da Junaid ba soyayyar aure ba! Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne to sai muyi shirin tafiya Kano, unguwar Galadanchi gidansu Uncle Junaidu, mu nemeshi mu kai kudin aure... mu gaya masa yadda kike son shi, har kina duban tsakiyar idanun masu son ki da aure na hakika kina gaya musu ba kya son su. ......sabida kawai kada ki ci amanar soyayyar shi da ya baki a makaranta. ......" .
Ala dole ta murmusa, ta san _zambo_ ne Dina take mata. Duka wannan bata lokacin da yawan bakin da Dina ta share tana bayani, ba duka abinda tace ne Mairo ta yarda dasu ba.
Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga AMEERU! Sabida shi ta sani, shine mai irin tsarin rayuwar su. Bata san komsi game da rayuwarta ta baya ba, batasan wanene Uncle Junaid a rayuwarta ba. Ita kudin Yaya Habibu ma tsoro yake bata balle na Amirun da ta ji suna cewa yana _World Bank_ karewar _Barclays_ . A karkashin inuwarsa rayuwar Habibu ta ginu bakidayanta. Shi ya maida Yaya Habibu ko me yake a yanzu.
Ta yarda ta hakura da Uncle Junaidu sabida hujjoji kwarara da kowa yake gaya mata. Hatta Nabilah tace da ita "lokaci yayi da zata manta da Uncle Junaidu tayi aure". Ta dubi irin auren da ita tayi, amma daga baya ya zame mata ALHERI. Don yanzu ba abinda take so a duniya sama da Ismael kuma shima hakan har ga albarkar haihuwa.
Ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta bayan fitar Dina. Ta ja bargo har kanta ta kudunduna. Bacci take so ta yi amma ya ki zuwa. Al’amuran na neman tarwatsa mata kwakwalwa tareda wargaza mata tunani bakidaya. Tana so ta yarda da Dina, halaccin dake zuciyarta na karyata Dina. Amma abubuwan da ta zano ai duk haka suke; zata je neman auren Uncle Junaidu ne??? Ko kuwa haka zata kare a zaman jiran *tsammanin warabbuka* ???
Zata iya cigaba da zaman jiran ranar da uncle Junaid zai nemeta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya bata uzurin da ya hana shi yin hakan a lokacin da ya dace daga nan har gaban abada! Amma bazata iya jure bukatar gangar jiki da zuciyarta ba irin na kowanne lafiyayyen dan Adam. In hakane aure ya zama dole a gareta domin kare kanta daga _zina_ , da sauran ayyukan alfasha, cikar mutunci a idon duniya da karuwar matsayi a fadar Ubangiji.
Wayarta dake karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text ). Cike da mamakin wanda ya yo mata sako a daidai wannan lokacin karfe biyu na sulusin dare agogonsu na can ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna. Bata san lambar ba don kuwa bakuwa ce, ga abinda ke rubuce;
".......... _When life changes, and we go our separate ways, you will still be in my heart till my dying days...... my world has never meet a person like you!"_
(A yayin da rayuwa ta canza ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu) zaki cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin ki ba).
Haka ta sa sakon a gaba tana ta karantawa har akayi kiran Assalatu. Don ta tabbata ba kowa bane; Amiru ne. Duk da bai saka suna ba ko wata alama mai nuna shi din ne. Allah sarki! Har YA HUCE ne? Tana so ta bashi amsa bata san me zata ce masa ba.
Da safe take nunawa Dina a kitchen, ta karanta tayi dan miskilin murmushin nan nata. Tace "ke kuma kika ce me?"
Ta zumburi baki "ni ko kula sa ma na yi?"
Dina tayi dariya tana kwaikwayon muryar ta tace "Haba Mairo! Yi hakuri ki dan kula sa. Kin ga shi yayi fushin amma ya sauko, sabida ya fahimci Mairo ba sonsa bane bata yi, kawai ita din mai *amana* da *rikon alkawari* ce".
Tayi murmushi har kumatunta ya lotsa. Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami. Tace.
"To me zan rubuta???"
"Ki ce kawai yazo yayi _joining_ dinmu _breakfast_ ".
Mairo ta rubuta ta tura. Amsar da ya bata ta sa ta yin murmushi, domin ya ambato rabin ranta.
"A'ah kirawo JUNAID......"
" He's far away....!_ " (Amsar Mairo).
"And I'm not closer too.... I'm far away either, and I will not come back. On my way to Detroit-Metro".
Hankalinta yayi mummunan tashi. Saboda ita ne Amiru zai bar kasar da haihuwarsa ne kawai ba'ayi cikinta ba? Da sauri ta jefar da wayar. Da gudu tayi daki ta dauko mukullinta. Dina na kira amma bata juyo ba take fadin.
"Shima zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min soyayyarsu. Banaso in samu wannan _heartbreak_ (karyewar zuciyar) a karo na biyu".
Dina tace.
"Bi shi Mairo. Shine ZABIN ALLAH!!!"
Gudu take shararawa a kan titin da zai kaita _airport_ din Detroit. Cikin kankanuwar motarta *GMC Terrain.* Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke; wannan itace SOYAYYAH! Da gaske Dina ta ke Amiru shine ZABIN ALLAH! Da gaske Dina ta ke da tace ta kama mai sonta, ta rabu da *JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA!* Ta karbi *soyayyah* a hankali zata rikide ta zama *kauna* . To ga shi soyayyar ma zata gudu ta barta da tsammanin warabbukanta wanda bata fata. .........................!!!
Koda Ta iso airport din ko kulle motar bata yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta shige cikin _reception_ tana dube dube. Babu Amiru babu ko mai kama da *AMIRU* ! Ta karasa _terminal_ bayan ta hankade ma’aikacin dake kokarin hanata shiga. Daidai sanda anka rufe kofar jirgin ( _Lufthansa_ ) wanda zai tashi zuwa kasarmu mai dimbin albarka. Ba da jimawa ba kuma ya soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi, kafin ya daidaita sosai a sararin samaniya.
Mairo ta durkushe anan tana kuka. Kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin BABANTA da INNAR TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan farin cikin data samu cikin *Michigan* wanda Yaya Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne ya kara rusa komai. Ya tafiyar da sauran karfin zuciyarta. Ya dawo da rayuwa *unbearable* kamar kamar uncle Junaidun? Me yasa ita bata da sa'a a soyayya komai kankantarta???
Ji tayi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma an kai hannu a hankali an dafa kafadarta. A sannu ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wanene wannan???
*A BARI YA HUCE* . ......
Littafin
*_Sumayyah Abdulkadir Takori*_
_Wannan littafi tukuici ne ga masu sha'awar ganin rubutun TAKORI a yanar gizo. Ga mai son cikakken labarin (book 1-4) ya biya N1000 ga wannan account number_
*Sumayyah K Kabara*
*Zenith bank*
*2089357770*
_Sannan sai ya turo screenshot zuwa 07030137870_
NAGODE
7/28/21, 10:59 AM - Buhainat😝: KAUYEN GURIN-GAWA, 1988
Gurin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al'umma masu sana'o'i daban-daban, amma duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da manyan malaman da a halin yanzun suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano. Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar wutar lantarki, ruwan sha mai tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar nomansu.