← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 71

Sashe 70

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tundaga yanda Ammi taga fuskarshi gabanta ya shiga faduwa ta shiga ambaton Allah, dawani irin zuciya Dady ke dumfaro su harya karaso inda suke tsaye hannu yasa yawani irin fizgo Aneesa dake tsaye kusada Ammi jikinta na rawa Dady baiyi wata wataba ya daga hannu ya watsa mata lafiyayyen mari "tass!" runste ido Ammi tayi dan har kashinta taji marin da Dady ya dauke Aneesa dashi, fashewa da kuka sosai Aneesa tayi tsabagen tsoro tamika hannunta tana kokarin kamo Ammi tace "wayyo Allah na Ammi, Ammi, Ammi, Ammi n...." zuba mata wani marin Dady yayi akaro na biyu da saita yasa tai shiru tai gum tama kasa magana sai dubu datake gani a idanunta cikin ihu da daga murya Dady ya jijjigata yace "me Aliyu yamiki? Meya miki kikeso kiashi lahira? Ubanwa yasaki kikashe min d'a??" yakara daga hannu zaikai mata mari na uku Ammi ta kirashi. "Alhaji" dago kai yayi ya kalli Ammi idanunta sunyi jajir suna shirin tsiyayar da hawaye, cikin raunin zuciya Ammi tace "kayakuri Alhaji ka kwantar da zuciyan ka abi komi ahankali, Aneesa bazata iya kisa ba, nasan abinda na haifa" cikin wani irin fushi Dady yace "nine makaryaci ko, kina zaton shiri nama yarki? Okay naji shairi namata a CCTV baya shairi ko to muje kigani" ya finciki Aneesa dahar lokacin bata gani sosai yay flat din Mama Ammi tabisu da sauri su Rauda dake kuka sosai da sauran matan Dady ma suka bisu har dakin cameran, shiga dakin Dady yayi rikeda Aneesa kaman wacce tai sata sauran matan ma da Ammi ma ta shigo cikin tsananin fushi Dady yace "play d footage back officer" dan bude idanu Aneesa tayi ta kafe computer da ido, wani irin faduwa gaban Ammi keyi lokacin da sukaga Aneesa ta jefa kwayar a mug da lokacin data dagargaza daya ta zuba akan pancake dakin yadau salati Mama tace "ga irinta nan ai, aure aure yau munga ranan aure aure, ka aurosu karufa mata asiri ka kawota gidanan da ita da agolan yarta, kahada yarta da namu gashinan suke son kashemaka d'a muda muke gidan nan shekara da shekaru ko kurjewa bamu tabasa Aliyu yayi ba amma gasunan dududu satinsu nawa a gidan just sati biyu da kwana daya" tajuya ta kalli Ammi tana mata tafi a fuska tace "to Allah yatona asirin ku, Allah yatona asirin ku kinyi amfani da yarki ta kashe Aliyu an kamaku, Allah saiya sakama Aliyu, butulu kawai murders, Aliyu daya dauke ku a matsayin uwa, andaiji kunya anji kunya, wlh hukuma ce zata rabamu daku, mutumin daya miki komi yafi fitaki kanmu harda siyamiki mota ne zaki kashema da" Dady jiyayi kirjinshi na tafarfasa kan maganganun Mama dan kaman tana sosamai inda kemai ciwone, cikin fushi Dady yajijjiga Aneesa dake kuka sosai yace "me dana yamiki Aneesa zaki kasheahi tell me the truth" fashewa da kuka sosai tayi tace "Abba wlh wlh, na rantse maka da girman Allah bani bane wlh, wlh kuw......" wani irin mari Dady ya kifa mata abaki saijini cikin ihu yace "stop lying! Stop lying kifadamin gaskiya, Maman ki tasa ki kashemin Aliyu kowane?" da sauri ta girgixa kai muryanta harbaya fita da kyau tsabagen kuka tace "wlh Abba banine ba, banine ba na rantse maka da girman Allah" cikin wani irin fushi ganin yanda take karya bayan ankamata dumu dumu yasa Dady yarufe ta da duka baji bagani tun Aneesa na ihu tana kiran Ammi hartazo takasa ihu ganin yana neman sumar da ita yasa officer da yaranshi suka rikeshi, yaciro ankwa daga aljihu yakama hannun Aneesa yasamata yace "with all the evidence damuka samu a kanki malama Aneesa, you are under arrest for attempt murder of Aliyu Muhammad Ibrahim you have the right to remain silent anything you say will be used against you" yajuya ya kalli Ammi dake kallon Aneesan dako numfashi bata iyayi yace "ki gayama yarki tafadi gaskiyan duk inda tasamo wanan poison din inba hakaba gidan yari ne makomarta" yaja Aneesan kaman yanajan kare sukai hanyar fita daga dakin Ammi ta tsaya still tana ma Dady wani irin kallo, duk fita akayi daga dakin akabi su officer dan aga inda zasuyi da Aneesa yarage daga Ammi sai Dady adakin, ko kallonta Dady baiyiba azuciye yazo zaibi tagefenta yawuce takama hannunshi tarike lumshe ido Dady yayi Allah kadai yasan iyason dayake ma Ammi dan tabashin nan datayi har brain dinshi yaji, kasa juyowa yayi hakan yasa ahankali Ammi ta zagayo ta gabanshi tasan Dady nacikin tashin hankali, ya acikin matsala saisa dudda uban dukan dayama Aneesa still tamai uzuri batason ko kadan taga bakinshi, ahankali tana kallon fuskan shi tai kneeling akasa ta hade hannayenta ta danne zuciyata sosai dan bata so ta karaya she needs to be strong and fight this battle for her daughter a yanzu Aneesa batada kowa sai ita she's all alone, Murya chan kasa tace "Alhaji nasan kana cikin tsananin fushi da bacin rai amma dan girman Allah ka sauraren" tadanyi shiru tana sauke ajiyan zuciya tadaga fuskanta ta kallai har yanzu idanunshi a lumshe kaman bayamason ganinta ne, Murya chan kasa tace "Alhaji bantabajin daidai da atom of hatred towards Aliyu ba, na rantse maka da Allah ubangijin mu, ubangijin Al arshi wanda ya busamana numfashi, ubangijin sammai bakwai, wanda ya halicce ni ya hallice ka ya hallici duwatsu da dabboni Alhaji bazan taba tunanin bama Aliyu wani abu danna halaka shi ko kokuma wani abu mai kama da hakan, haka zalika zan iya rantsemaka Aneesa ma bazata iya hakanba, am not justifying abinda Aneesa tayi bakuma kokarin kareta nakeba, but dan Allah ka yakuri, ka sauko da zuciyan ka, dan girman Allah kasaka asaki Aneesa she is too small tazata san rayuwan gidan yari kokuma rayuwan police station the trauma bazai taba barinta ba, Allah kayakuri ka janye case dinan kasa asaki Aneesa tadawo gida let's solve matsalan nan maturely, matsalan gidane let's solve it at home dan girman Allah kaji".

_follow me lemme walk on the journey of visuals can be deceptive wlh_
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

4️⃣5️⃣

Ko minti biyar baiyiba yawani irin yaye bargon da sauri yatashi zaune sabida jidayayi kaman hanjin cikinshi na harhardewa tundaga wuyan shi har zuwa cikinshi zafi yakemai kaman an watsa garwashin wuta akansu, wani irin kara yayi yana juyi "ahhhh" yajuya yana nukurkusu yana nishin azaba, azaban dayakeji yawuce misali, goran bottle water dake kan side drawer dinshi ne yadauka yabude ya kurba ko ya ragemai ciwon kaman yazuba gishiri a ciwo haka yaji hakan yasa yawani irin bankare yana ihu yana lankwashewa......

Shigowa gidan Nazif yayi yay parking motarshi Mama dahar lokacin ke jikin window tana kallon komi dake faruwa na tsakar gidanne gabanta nafaduwa tana addu'a Allah yabata nasara ne tabude kofa da sauri tamai alamu da hannu daya yakarso da sauri, karasowa yayi kafin ma yay magana taja hannunshi suka shiga dakin tamaida kofan falon tarufe, hada ido yayi da Rauda dake zaune da kanninta suna kallon cartoon, daure fuska tayi kaman batasan shiba dan ta mugun tsananshi yanzu, hararanta Mama tayi tace "bance ki cinyemin d'a da idanunki dasukai kama dana ubanki ba mai bakin hali kawai, common tashi kifitan min daga flat, wuce kitafi wurin Yayan ki mayya nasan abinda kikeso kenan" da sauri Rauda ta kalleta dan bata yadda da abinda taji Mama tafada yanzun nanba, anya Mama ce zata turata wurin Ya Aliyu willingly kuwa?, cikin daga murya da masifa Mama tace "kindaiji menace ko, tashi ki barmin daki kiwuce wajen Yayanki magana zanyi da Nazif mai mahimmanci" dawani irin gudu Rauda tai tsalle ta mike tsaye tai hanyar fita Nazif yabita da kallo, cikin rawan jiki Mama tace "kai yanzu ba lokacin kallon Rauda bane wani muhimmin abu nikeso kamin yanzun nan muje kaga" sama tai dashi wani dakin Dady tabude ta shiga yana biyeda ita tasa Hajar gadi afalo dazaran taga Abba kokuma Rauda tafada mata kota mata signal.......

Sallama Rauda tai a part din Aliyun jin shiru yasa tabude kofa ta shiga abinta ta maida kofan tarufe tana hararan TV dake aiki a tashan kwallo tace "shi ya Aliyu kullum, kullum ball, ball ball uhm" tai maganan tana daukan remote ta chanza channel zuwa cartoon ta ijiye remote din tai hanyar bedroom dinshi tana kwalmai kira. "Ya Aliyu, Ya Aliyu kana bathroom ne? Ya Aliyu" agaban bakin kofanshi ta tsaya tai knocking jin shiru yasa tabude ahankali dan tasaba shiga dakinshi kai tsaye daman kuma baya hanata, dayake itama daga rana take batagani sosai dudda bedside lamp dinshi akunne yake, ahankali tadaga hannunta zata kunna switch din wutan dakin tace "bacci kakene Ya Aliyu?" kunna wutan tayi dakin yay haske, idanunta ne suka sauka kan Aliyu dake kasa yana wani irin mimmikewa kaman wanda ake zarema rai idanunshi na juyawa, harshen shi yafito daga bakinshi wani irin kumfa nabin gefen bakin nashi, wani irin talo idanu waje Rauda tayi tana kara kallon Ya Aliyu danta tabbatar shine koba shi bane yana sanye da dogon jeans dinshi blue jikinshi ba riga lying on the floor yana fizge fizge jijiyoyin wuyanshi dana fuskanshi sun fito tsabagen yanda yake stretching din azaba, wani irin ihu Rauda tayi da saida gabaki dayan flat din Aliyu ya amsa. "Ya Aliyuuuuuuuu!" da gudu tai kanshi ta tsugunna agabanshi tana tabbatashi bama tasan metake yiba. "Ya Aliyu, Ya Aliyu, Ya Aliyu menene menene wanan sabulu kasha ne?" ganin Aliyu baimasan waye akanshi ba kakkari yake yana har yanzu harshen shi awaje bakinshi nafitar d kumfa yasa tai wani irin jumping tsaye tama rasa mezatayi da gudu tafita tana kwalama Dady kira da duka muryanta. "Dady, Dady, Daddy Ya Aliyu" yanda take kwalama Dady kira zaka zaci ta haukace ne da gudu tai flat din Dady hannu ta daura kan handle ta shiga murzawa amma kofan a kulle hakan yasa tasa duka hannayenta ta shiga bubbugawa tana kwalama Dady kira. "Daddy, Dady, Dady Ya Aliyu, Dady ya Aliyu zai mutu wlh, wayyo Allah Ya Aliyu Dady"
Chapter 70 · 0% Book details