← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 71

Sashe 34

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gently yay sucking bottom lips dinta, omg he has never ever kissed anyone before, yanda lips dinta keda taushin nan ga dumin bala'i yasa yaji all organs din jikinshi sun soma amsawa da sauri yasaki lips din nata and move back towards the wall kaman wanda aka tura ya jingina da bangon tareda lumshe ido yana sauke ajiyan zuciya anatse trying to get his self back to normal, bude kofan dayaji anyi yasa yabude ido ya taso daga jikin bangon yana kallon kofan, Dr yagani shi kadai rikeda takarda da byro, karasowa ciki Dr yayi yana kallon Aneesan da idanunta kenan a kulle hawaye nafita ta gefen idanunta ancire mata oxygen din dan babu shi akan hancinta, da sauri yakara sa jikin gadon yana kallon yanda ta cire shi ta ijiye gefe yace "cire oxygen din kikayi patient dina sabida kin tashi kin soma samin lafiya? And why are you crying, your mummy is coming back yanzun nan abinci taje tadafa miki" yajuya ya kalli Aliyu dayazo ya tsaya a gefenshi batare dayace mai kalaba yarungume hannu a kirji yana kallonta, tsayar da abinda yakeyi Dr yayi yace "Sir may I know you please? Yaushe kazo?" dan juyowa Aliyu yayi ya zubamai mayun idanunshi yace "Bandade da zuwa ba" yamikama Dr hannu, hannu Dr yamiko mai suka gaisa Aliyu yace "am Aliyu, her husband to be" ware ido Dr yayi saikuma yay dariya yace "I see, no wonder takema kukan shagwaba anki bude ido a kallemu" dan murmushi Aliyu yayi yajuya ya kalleta har lokacin idanunta a lumshe jiyake kaman ya sunkuceta daga kan gadon nan yay gidanshi da ita let them just stay there forever and ever, dan juyo dakai yayi ya kalli Dr dake yan rubuce rubuce yace "what's wrong with Love of my life Dr?" dago kai Dr yayi ya kallai yace "I must say, kayi dacen mace, your wife is a very very strong, she's a fighter, masu maleria datake dashi giving up suke but ita tace ina she must live to tell the story of her love life" dan murmushi Aliyu yayi yasake kallonta batare daya janye idanunshi daga kanta ba yace "yeah, my baby is very strong, bold and above all fearless, she don't wanna leave me dan tasan bazan iya rayuwa bataba" tafi Dr yashiga yi dayake yanada son surutu hakan yasa Aliyu tajuyo ya kallai, tsayar da dariyan yayi yace "maleria take fama dashi 4+, an shigo da ita jiya tana seriously convulsing ga wani uban high temperature datake running finding it difficult to breath, but fear not muna bata best treatment, yanzu ma Mum dinta muke jira takawo abinci dole saitaci abinci sanan zamu bata magani musamata wani karin ruwa dan wanan yakare tun dazu dasafe nazo nacire mata" gyadamai kai Aliyu yayi batare dayace komiba, Dr yace "bari nabarku tare karna katse muku hira" , yasa hannunshi a aljihun lab coat din jikinshi ya ciro new toothpaste da new toothbrush da asibitin kebama all patients dinsu yace "ga abinda nakawo mata, ta wanke baki kotaji dadin jikinta" hannu Aliyu yamika ya karba yana kallo Toothpaste din dako kadan baimai ba, Dr yace "bari naje before 10 her Mum will be back, ka lallabata please makesure she tadena kukan" yay maganan yana fita daga dakin yarufo musu kofa, kujera yaja ahankali ya zauna yana ijiye su brush din akan drawer kusada gadon yana kallon yanda taki bude ido har yanzu saidai tadena kukan dan hawayen sun dena zuba, murya chan kasa yakira sunanta. "Aneesah" ganin taki kallonshi ko motsi ma batayiba yasa yace "please open your eyes" kin bude idanun tayi tana saukar da numfashi ahankali, tarasa mesa duk in Aliyu na kusada ita rasa natsuwan ta take sai zuciyarta yadinga wani unusual beating, dan shiru yayi batare dayasan mezaiyi ba, tashi tsaye yayi daga kan kujeran yace "am coming" yay hanyar kofa yabude kofar dakin yafita yana tafiyan nan dai dai dake dauke ma mata hankali, ahankali tabude ido tabi kofar daya rufo mata da kallo kaman shi take gani, batada karfi ko kadan saima cikinta dataji yana mata wani mugun ciwo hade da maran ta kaman she's about to have her monthly flow, dan yatsine fuska tayi idanunta na lumlumshewa juyar dakai tayi ta kalli hanunta taga anriga ancire mata drip din hakan yasa ta tattaro duka dan karfin datake dashi ta tashi zaune tana jingina da bangon gadon tana numfashi sama sama tana sauke ajiyan zuciya cikinta na masifar mata ciwo kaman ma harda yunwa, dakin har wani dan juyawa juyawa yake mata, lumshe ido tayi tana sauke ajiyan zuciya saida tai kusan minti biyu ahaka sanan tabude idanun ganin dakin yadena juya mata yasa ta saukar da kafanta daya ahankali tana yatsine fuska tsayawa tayi tana hutawa dan the pain she's going through yay yawa, almost minti uku tabata sanan ta saukar da dayan kafan shima kasa ahankali tana yatsine fuska, ahankali ta sanya duka hannayenta takama karfen da ake makala drip tarike gam sanan ta mike tsaye kasusuwan jikinta nawani irin kas kas kas, jikinta yay tsami sosai kaman takai shekara daya a kwance ko kadan batada karfi kaman an mata alluran kashe karfin jiki, jin kaman tana neman tafadi kanta namata zuuu zuuu yasa tarike karfen gam trying to have control over her body, takai kusan minti hudu ahaka sanan tadanji daidai taji ciwon cikin ma yadan lafa, sakin karfen drip din tayi ahankali tamika hanunta tadau toothpaste da toothbrush din da Aliyu ya ijiye kan drawer tarike danko kadan bakinta bai mata dadi, gently ta daga kafanta tai taking first step sotake taje bayi tai brush then ease her self dan fitsari takeji sosai, tana numfashi da sauri da sauri tasake taking second step.

Kadan kadan take tafiyan tana hutawa hartakai kofan data kyautata zaton bayine sabida signboard din toilet dake jikin kofan, murdawa tayi ahankali ta shiga ciki ta mayar da kofan ta rufe ta shiga kallon bayin, bayin badai kyauba komi very clean and neat, juyawa da idanunta suka farayi yasa ta daura kanta jikin kofan ta lumshe ido saida taji daidai sanan tabude idanun tadago kanta tafara tafiya, ahankali takarasa gaban wash hand basin kunna tap din tayi ruwan ya shiga zubowa tabude brush din da kyar tarike ta tana kokarin matsa toothpaste akai hanunta ya shiga rawa, faduwa daga toothpaste din har brush din sukayi akasa daga hanunta jikinta ya shiga rawa maranta yafara daurewa, matsawa tayi gefe, wani irin murdamata da cikinta yayi yasa da sauri tai releasing bladder ta tai fitsari tai tsarki sanan ta tashi tana dafa bango tana kallon kofan fita datake so taje tafita dan jirin data fara gani yasoma fin karfinta, da kyar ta iya daga kafa tana tafiya tana layi kafin tawani irin zube akan dry clean tiles din bayin tasaki wani irin wahalallen kara...
Chapter 34 · 0% Book details