← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 71

Sashe 52

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 3 min read

Dady yace "Ummu Aliyu akwai enough food yar abokina na hanya, wacce zata zo muga yazata kasance ai nafada miki ko" fashewa da dariya Abdul yayi ganin yanda Aliyu yay kini kini da fuska, kallon fuskar Aliyun Ammi tayi tadanyi murmushi tace "shikenan Alhaji, kutaso kuzo kuci" tashi dukansu sukayi sukai dining banda Aliyu da ranshi yake abace, Momma tace "Beta are you not eating?" daure fuska yayi yace "am not" Momma zata kara magana ahankali Ammi tace "kuna damun min d'a fa" dan dariya daga Momma har Dady sukayi Momma tace "Aliyu kayan haushi, munkusa ganinku arana indai wanan rubabben yaron ne" girgiza kai Ammi tayi tadau tray ta daura plate of fried rice da chicken akai sai coconut juice a jug da glass cup tafito daga dining duk Dady dayay kaman yanacin abinci yana kallonta, dan karamin stool taja takawo gaban Aliyun da kunya yakamashi ganin itada kanta tazo, stool din taja ta daura tray akai sanan ta zauna gefenshi abincin ta dauka ta mikamai tace "don't mind them ga abincin ka kaci bazasu ganmu arana bako" ahankali as usual yanda yakema Dady, a shagwabe yace "banda apatite nacin abincin Mum" dan shiru Ammi tayi tana nazarin fuskanshi kafin tace "okay let's do this" tai maganan ta yanda daga ita sai Aliyun zasu ji, hakanan takeson yaron sanan yana bata tausayi ganin yanda yakeyi, komi babanshi, komi babanshi, ahankali tace "anama iyaye biyayya ne dan asami albarka right" gyadamata kai yayi tai murmushi tace "gud, give it a chance, idan tazo kaganta bakasan wazaka gani ba kuyi gaisuwa na mutunci koba komi kanwar kace itama ai ko, so karkaji komi inhar ina gidan nan you get to marry wacce kakeso, am your Mummy I will always stand by you against all odd, are we gud now" tunda Ammi take maganan yake kallonta ta bala'in burgeshi kawai ya girma ne da baiga mezai hanashi rungume ta ba maganganun ta sunmai dadi sosai, wani irin cute gamshashen smile yasakin mata tareda gyada mata kai yace "Alright Mum" murmushi itama Ammi tamai tace "ga abincin ka, bari naje naji da baban ka" da sauri yamika hannu ya karbi abincin yafara ci murmushi kowa na dining din sukayi dan hankalin su na kansu kuma tsaf sukaji abinda Ammi tafadin mai dudda bada karfi take maganganun ba, Dady karkada kafa kawai yake yana tunanin mezema Ammi, shi inhar mutum zaiso Aliyun nan nashi to wlh zaima iya bama mutumin kanshi ta hanyar zama bawa agreshi, Aliyu is his life so duk wanda zaizo Aliyu yagamamai komi aduniya, kujeran kusada shi da Ammi taja ta zauna yasa ya yadaga kai ya kalleta itama kallonshi tayi cikeda so da kauna, abincinshi yadeba da spoon yakai bakinta akunyace ta bude baki ta karba batason tai turning nashi down but she's shy ga yara awurin kuma saisa kawai ta karba, sosa keya Abdul yayi ganin soyayyan tsofaffi kafin yaja plate dinshi ya sauka daga kan dining table din yakoma kan kujera wurin Aliyu, daga Momma har Ihsan sukai murmushi duk aka cigaba dacin abincin.
Chapter 52 · 0% Book details