← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 71

Sashe 12

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jan Raudan yayi da batada karfi ko digi ajiki har yanzu jin kennenta take dummm kaman banata ba Aneesa da jikinta yafara rawa sosai ganin yanda yawani irin daure fuska tasaki wani irin wawan ihu. "Ammiiiiiii! Wayyo Allah n..." buge bakinta yayi azuciye yace "yau zakici uwarki, gwara wanan" yanuna Rauda dake sauke ajiyan zuciya kawai yace "su sunsan inda zasu ganni a duniyan nan , keko baki sanni ba, daga yau baki kara haduwa dani, shiga shara ba shanu banga uban abinda zai hanani yimiki fata fataba dama daga ganinki zakiyi man shanu" ya jasu duka biyun kaman raguna yay hanyar kofar dakin zai shigar dasu, Aneesa sai tutturjewa take, wani irin bugo Gate din da akayi da karfin bala'i yasa dukansu ukun suka waigo, ido da ido Khamis yay da Aliyu dake sanye cikin wani Milk wagambarin shadda da aka mishi dinkin fitted yaji aikin hannu, yasa takalmi irin na yan gidan sarauta dinan kanshi babu hula sai bakin gashin kanshi dake masifar kyalli kaman ya shafa man gashi, idanunshi sanye cikin dark shade abinda yaboye jan da idanunshi sukayi kenan tsabagen yanda ranshi yakai ga baci, yana tsaye wajen Gate amma saida kamshin turarenshi yakai har inda suke gaban kofa ko ina yadau kamshin shi, ganin Aliyun yasa wani irin karfi yazoma Rauda tawani irin fizge hannunta daga rikon da Khamis yamata ta tashi tsaye tazo da gudu tafada jikin Aliyu tasaki kuka sosai takasa magana, ganin haka yasa Aneesa ma da gabanta ke faduwa bana wasaba ta fizge hijabin ta da Khamis yarike ta taho da saurinta gefensu Aliyun ta tsaya kirjinta na bugawa kaman zai tsage, dan wayancewa Khamis yayi yakakalo murmushi yatako ahankali yana dumfaro su da sauri Rauda tasaki Aliyu takoma bayanshi ta labe tana kuka hakan yasa Khamis ya tsaya chak a tsakar gidan yakasa karasowa gabansu, hannu Aliyu yasa yazare dark shade din dake idanunshi ya zubama Khamis jajayen idanunshi dayasa yaji internal organs dinshi na girgiza cikin wani Husky harsh voice yace "how dare you raise those your filty hands on my sister, how dare you touch her" hausawa sunce tabarman kunya da hauka ake nannade ta, cikeda borin kunya shi adole shi shine yace "who is your sister? Raudan ce sister ka?" ya tambayi Aliyu cikeda kallon isgilanci yace "as far as am concern and base on wat I know ko mahaifiyar ta tacha cewa kai ba wan yaranta bane, you guys are not blood related, bama tasan da zamanka ba, kuma mahaifiyarta tabani izini na dauketa nakaita yawon ido karmu dawo sai dare gatanan u can ask her and hear for yourself, banda hakama who do you think you are to talk to me in such manner nafika matsayi da iko akan Rauda, am her Mum's elder sisters first son, and her husband to be, ko ubanka yasan da hakan so back off please, ke Rauda let's go" yay maganan yana tahowa yazohar gaban Aliyun yasa hannu zai jawo Raudan cikin wani irin fushi Aliyu ya kwasheshi da mahaukacin mari. "Tau!" da sauri Aliyu yarike hanunshi sabida zafin da hanunshi yadauka ya murza hanun kaman zaiyi kuka yace "aauchhhh" yana yarfe hannun, yanda yayi saida yasa Khamis fashewa da mugun dariya dudda marin ta shigeshi dan har gefen fuskar da Aliyun ya mara yay ja abunku da fari, da yatsa ya nuna Aliyun dake yarfe hannu yana yatsine fuska yace "wanan ne, wanan ajebotan kuka kira yay protecting naku daga ni? wanan malalacin namijin daya rako maza duniya wanan maza matan dayamafi mace yauki kaman kubewa ne kuka tunanin can beat me up?" hannu yakai yafara bude boturan gaban shaddan riganshi yace "zan nunama u have messed with the wrong guy ni haifaffen dan kwari ne ba girman turai ba, girman tasha, kar har purewater na saida a park" fashewa da kuka Rauda tayi dan tasan Ya Aliyu bai iya fadaba ko kadan ta jijjigashi tace "Ya Aliyu mugudu please" itama Aneesan jikinta rawa yafara ganin Khamis cikakken dan tasha ne kam yana magana kaman dan wiwi, riganshi ya zare ya yar akasa ya matso gaban Aliyu ahaukace yasa duka hannayenshi ya daki kirjin Aliyu da saida yay baya kaman zai fadi yace "kai ubanka yaci ubanka kaji, dan babar ka nataba kanwar taka uban me zaka iya? Eh nace ubanme zaka iya?" Khamis yay maganan kaman dan daba yana hura hanci, Aliyu ya kafeshi da ido he really do not know how tayaya ma zai fara fighting dinshi ba, indako yasani daya kusan kashe yaron nan, cikin kuri yay pointing Aliyun da yatsa yana murmushi ya kalli Aneesa da Raudan dasukai zuru zurun barinma Rauda dake kuka wiwi za'a dakinmata yayanta yace "do you all see what am saying, bakazo shigarma kanwarka dat I was trying to rape bane? Then beat me up now Aliyu, are you scared Mama boy? Beat me mana, kawa Allah ka dakan, baku ganiba matsoraci bane, kai" ya dungure ma Aliyun goshi da yatsa Aliyu yasakeyin baya, Khamis ya nunamai yatsar shi ta tsakiya yace "f**k you Aliyu, I said f**k you mezaka iya? Daken mana kaji tsoro ne eh? Eh malalaci?" yanda yakema Aliyun daya tsaya kikam yana kallonshi tijara yamugun sosa ran Aneesa saitaji kaman tai kuka dan daga ganin yanda Aliyu ya mareshi da farko ya shiga yarfe hannu zaka gane baida karfi kona sisi, kallon yanda Rauda ke kuka sosai abayanshi take alamun batada hope zai musu dukan tsiya sanan yama yayan nata dukan tsiya shima hakan yasa taji wani karfi yazo mata da bata taba jin irin that kind boldness ba in her life, cikin wani irin izza ta shiga gaban Aliyu tana taku dai dai tana clapping hands dinta cikin isa da takama tana clapping din tana kallon fuskan Khamis din dake kallonta kaman yanzu yafara ganinta, tsayar da tafin tayi tace "kasan mesa nake tafa maka?" tai wani murmushi ganin baice komiba kawai kallonta yake kaman wani wawa tace "wani zubin idan kare na haushi idan kai tafi saikaga yadan natsu" cikin fada yace "nikike cema kare?" cikin dakewa ta nunamai yatsa tace "quit, am still talking" samun kanshi yayi dayin gum ganin yar yarinya namai magana kaman uwarshi, tace "what differentiate human being da animals is ability to think and reason which bakada duka biyun you are just a dog malam which yayan mu bazai taba iya biyema yadawo kaman kaiba ko?" tadan juyo for the first time ta kalleshi idanunshi da nata suka sarke faduwa sosai gabanta yayi tadan kyafkyafta ido sau biyu pink lips dinta sukadanyi rawa ahankali tace "ko?" gyadamata kai Aliyu yayi batare dayasan yamayi ba, juyar da kanta tayi tace "kai mailafine bagaremu ba kadai har agun Allah, sanan kanada bakin zage zage kana turashi kanaso yabiye maka kuyi fada, wai intambayeka man do you know who is a Man?" wani matsiyacin kallo tamai ganin yanda yasaki baki yana kallonta tace "A Man baya tsayawa yay physical fight da kowa dan physical fight dangrades one's level, banda haka a Man is someone who has control over his heart ayayin dayake cikin tsananin fushi which is abinda yayi yanzu, kazaci kana ihu kana cika kana batsewa kana tunanin by d time dayake so yaci ubanka you can match his level ne eh?" tamai tambayan tana hura hanci daya kaman wata boss tana kallonshi, dan murmushi Aliyu yasaki for the first time ya rungume hannayenshi a kirji, ganin har lokacin Khamis din baice komiba ya tsaya yana mamakin tane yasa tace "and yanzun nan zan nunamaka idan yatashi yace zai ci uban naka u can never match his level of power, kwabaka zaiyi kaman yanda ake kwaba dibila tsaya kagani" tai maganan tana tsugunna wa a wurin duk suka bita da kallo kasan dake bakin Gate din ta kwasa da hannunta dayawa batare da duksun luraba dan hijabinta yarufe mata hannu sundaiga ta tsugunna mikewa tsaye tayi Khamis din nabinta da kallo hannunta tadaga un expectedly ta watsamai kasan a fuska aiko suka shiga idanunshi biyu, ihu yayi. "wayyo Allah na, wash Allah idanuna, sainaci durun uwarki yarinyar nan" yayo kanta yana sosa idanunshi dayakasa budesu tsabagen kasan data sakamai a ciki matsawa gefe tayi da gudu ta kalli Ya Aliyu dake binta da kallo tace "Yayan mu yimai shegen duka ramama kanwarka abinda yamata bazai iya ramawa ba idanunshi cike suke da kasa" ware manyan idanunshi Aliyu yayi yana kallon this wired girl, gyadamai kai tayi da sauri tace "ka zaneshi, daddaki azzalumin" jin daga ta inda take magana yasa Khamis yay wurin yana murza ido yace "dan uwarki ubanwa yace miki koni makahone zai iya tabani ne wanan ragon" dawowa tayi kusada Aliyun ta kallai tace "yimai lilis u can do it, zo zan nuna maka inda zaka dinga duka ajikinshi zokaga" tai gaban Khamis din dake bubbude kafa yana sosa idanu kaman mahaukaci tsabagen azaban kasan dake cikin idon, ta nunama Aliyu cikin shi daya fara dan tara teba dama babu riga ajikinshi tace "zoka naushi nan" turashi Rauda tayi tace "muci ubanshi Ya Aliyu ka rama mana" ahankali Aliyu yadaga kafa yana kallon Aneesa dake nunamai cikin Khamis kaman wawa yakaraso kusada inda take yana kallonta still, zare ido tayi tsabagen jin dadi zasuci ubanshi tarage murya kaman mai shirin gulma tace "yauwa naushi nan".
Chapter 12 · 0% Book details