← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 71

Sashe 41

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin fashewa da dariya Abdul yayi har yana buga kanshi kan abin tuki. "wayyo Allah na cikina, Mommahhh cikina zai fashe" yarike ciki dahar murdamai yake tsabagen dariya da kyar yay shiru ya kalli Aliyu dayaga ya lumshe ido kaman mai bacci nanko duk yagama ganin abinda Aneesa tamusu yace "ashe yar bala'i ka dauko mana Aliyu, wai wai wai nida Anty barkono, chab" yakara kecewa dawani mahaukacin dariya, bude ido ahankali Aliyu yayi dasukai jajir yazuba mai su, hannu Abdul yadaga cike da dariya yace "sorry, sorry nadena" yay shiru yana shafa baki yana kallon glass din motar dayay jajir dan jar kasane a anguwan yace "wai, I mean look at our glass kaman wayanda suka fito daga rami, Allah yasa motarka tama haka da tawace da yasin saika wanke ta, Leo a ina kasamo barkonon nan?" yakara kwashewa da dariya, hannu Aliyu yasa zai bude motan yafita yabarmai dan he's just adding salt to his wound da sauri Abdul yarike shi yana danne dariyan dake cinshi yace "yakuri, yakuri inato zaka? Ihakuri haba Only Friend, but honestly I love her I mean the girl, damn! Masifanta ya mugun burgeni Leo, am just wondering yanda kaida ita zakuyi rayuwa under the same roof kai zuciya ita zuciya inkuka sami mis understanding sunan gidanka gidan kas....kasa Le..." yasake kecewa da dariya, ji Aliyu yake kaman ya shakeshi yahuta kawai ahankali hawaye ya gangaro daga idanunshi yana kallonshi da sauri Abdul ya tsayar da dariyan kaman ba shine ke dariya ba cikeda damuwa yace "Hey Leo mehaka kuma daga wasa, please stop" handkerchief din cikin aljihun shi yaciro da sauri yamikama Aliyun yana shiga taita yin shi, ahankali ya karba ya share hawayen tareda fuzar da iska mai zafi, bude motan Abdul yayi tareda daukan towel din share glass din motar, dariya yakeso yayi ganin yanda Aneesa taci uban motar da kasa saikuma ya gimtse dariyan dan fess Aliyu zai iya tasa shi agaba yay tamai kuka, share glass din yayi tass amma dudda haka motar nan dole sai taje car wash yakoma ciki ya zauna tareda tada motan yafara tafiya ahankali, agaban wani masallaci yay parkin suka fito sukai salla sanan suka koma mota yatada motar yana kallon hanya batare daya kalli fuskar Aliyun ba yace "if you want to win a woman's heart Leo dole ka sauke mata kai, allow her ta tattakaka yanda takeso tawuce tadawo if possible ma ta zubar da shara akanka, ance duk sarautan sarki a wajen matar shi bawa yake dawowa, I believe you know this girl (Aneesa) morethan I do, I just saw her yau harna gane who she is, kaiko nasan this is not d first time daka fara ganinta u understand who she is and yet kana mata zuciya da zafi agabanta, no no no that's very wrong, I understand how you feel seeing wacce kakeso tareda wani but you have to calm down and act maturely, yarinyar nan barkono ce and ta hanya daya ake winning zuciyan mata irinta" yay maganan tareda dan satan kallon Aliyun ganin yanda ya natsu yana kallonshi yasa yay dan murmushi yace "zan baka misali guda daya, ka dauka anyi serving nnaka abinci dake da yaji sosai abincin yaji barkono, harshen ka da bakinka da labban ka duk suka haukace sabida yaji by the time dazaka dauko sweet kabude daga leda ka jefa abakin kafara tsotsa just give yajin a minute or so zakaga dadin sweet din ya rinjayi yajin tun kanajin yajin har saiyazo yabace all you could feel is sweetness of your sweet, so just be like a Sweet towards this girl and trust me you will win her over, be sweet, be gentle, don't hit it hard take it slow one step at a time, forget baaba zata shigo hannu ne tsaf fine boy like you, Dady's Boy fa for that matter" dan murmushi yayi hakan ba karamin dadi yama Abdul ba daman yay hakane dan yasashi murmushi saikuma yayi fuzar da iska yyi yace "let's go home wlh yunwa nakeji".

Ganin babu Ammi a tsakar gida yasa tasauke ajiyan zuciya alwala ta dauro da sauri tawuce ta shiga dakinsu daidai Ammi ta sallame salla tace "hayaniyan menake taji awaje?" rasa me zatace tayi da kyar bakinta yasamo magana tasoma hadawa tace "wasu yara ke fada shine Yusuf yaraba su, yama tafi dama basu ganni bane shine yanemi gidanmu yazo yaji lafiya" charbi Ammi ta dauka tace "ayya, angode to, zokiyi salla kici abinci kisha maganin dare" hawa man dadduman tayi ta kabbarta salla Ammi kuma ta tashi tana kawomata abincin dazataci da magungunan ta tana idarwa tazauna tanaci bayan tagama tasha maganin da kyar shima dan Ammi tamata da gaske ne, suna falo har aka kira isha'i sukayi sanan suka cigaba da hira.

Sallaman Baffa sukaji saikuma ya kwalama Aneesa kira. "Fateema" tashi Aneesa tayi da sauri tafita yana ma wurin zaure tace "sannu da zuwa Baffa" yar ledan hanunshi yamika mata yace "ga tsaraban kinan, jeki cema maman ki Alhaji yazo ta gyara yanzun nan zan shigo dashi" wani irin tsalle tayi tana murmushi tace "tom " dasauri tajuya takoma daki dawani irin gudu taje tafada kan jikin Ammi dake kan dadduma tace "Ammi Baffa yace kici gayu Abba yazo zai shigo dashi" hararanta Ammi tayi tace "to bismillan su mana wani gayu zanyi ni? Namasan shairin kine" ashagabe tana turo baki tace "ni Allah saikin yi, kinji Ammi na please" tai maganan tana daga Ammin tanajan hannunta tashi Ammi tayi tace "nidai nabani da dake Aneesa" dariya tayi sosai taja Ammin sukai dakinta ta zaunar da Ammi kan gado jikinta harwani rawa yake tabude sip din Ammi wani leshi taciro da sauri Ammi tace "lafiyan ki kuwa Aneesa? Da daddaren nan zansa leshinnan dake da nauyi?" kallon leshin Aneesa tayi tana murmushi tace "au hakane wlh Ammi murna nake banmasan me nakeyi ba" tabe baki Ammi tayi tace "kyaji dashi, mikomin wanchan doguwan rigan atampan" tamata pointing wani atampa mai kyau daukowa Aneesa tayi takawo mata sanan tace "yauwa bari naciro hijabin dazai shiga dashi" komawa sip din tayi Ammi kuma yacigaba da shiryawa, wani mustard hijabi taciro mai hula daya dace da doguwan rigan tajuyo har Ammi tagama sa kayan da sauri tawuce gaban madubi hoda ta dauko da kawalli da man baki, kallonta Ammi tayi ganin ta kwaso kayan kwalliya zatai magana Aneesa kaman zatai kuka tace "ni Allah saina miki" shiru Ammi tayi babu yanda ta iya, karasowa tayi ta shiga mata light makeup ta shafa mata man baki sosai Ammi tai kyau har tazo tanajin wani iri dan tamanta rabonta datai kwalliya haka, sallaman dasukaji nasu Baffa yasa Aneesa tace "kisa hijabin bari naje na gaida su" fita tayi da sauri daidai Baffa ya shigo da Dady dayaci manyan kaya na milk shadda sai kamshi yake bazawa, babban dadduman su dasuke shimfida ma baki Aneesa ta dauko ta shimfida tana murmushi tace "Abba sannu dazuwa" cikeda fara'a yace "lallai y'ata ta warke masha Allah, naji dadi, ya jikin?" "Alhamdulillah naji sauki Abba ka zauna" tanunamai dadduman zama yayi tareda yin bismillah, Baffa yace "jeki kira Maman ki saiki dauko tsaraban ki kizo musha a tsakar gida" gyadamai kai tayi tajuya da sauri tai dakin Ammi, Ammi na zaune kan gado tasaka hijabin tai kyau sosai kaman wata sabuwan amarya wani irin tsalle tadaka tafada kan jikin Ammi tana dariya, salati Ammi tace "innalillahi, Oh Allah, haladai kinyi alkawari ne saikin karyani kafin gobe da safe ko Aneesa" kyalkyacewa tayi da dariya tace "Ammi na wlh dadi nakeji, Baffa yace kije, nidai natafi, Ammi na kimai firan nan naki mai dadi" dukan da Ammi ta daga hannu zata maka mata yasa ta tashi da sauri tafita daga dakin tana murmushi ledan tsaraban ta tadauka Baffa dake kallonta yace "yauwa muje" murmushi Dady yayi yace "laaaa ni baza abani ba" da sauri tazo gaban shi tabude mai ledan tace "a'a Abba gashi kasha" tafada akunyace, dariya yayi yace "nagode Allah amfana" cikeda fara'a Baffa yace "yakara auki daharna fara kukan zuci zaka shanye mana kashu dinmu" dariya dukansu sukayi Aneesa tabi Baffa suka fita tsakar gida a binsu suka zauna kan tabarma suna hira suna sha.

Saida Ammi taji fitansu sanan ta tashi ahankali sosai takejin kunyan yanda Aneesa tamata gayu kaman wata yar yarinya, ahankali tayaye labule tafito falon kanta akasa idanun Dady kyam akanta ko kyaftawa ba yayi, karasowa cikin falon tayi zata zauna akan kujera Dady ya nuna mata gefenshi da hannu kan dadduman yace "zoki zauna anan Rukayya" dan dago kai tayi suka hada ido da Dady gyadamata kai yayi hakan yasa ahankali takaraso wurin dadduman ta zauna inda yake nuna mata kusada shi amma adan kwai gab tsakanin su.

Ajiyan zuciya Dady yasauke yana kallonta murya chan kasa yace "kinyi kyau sosai Rukayya" kasa dagokai Ammi tayi dan maganan yabata kunya murya chan kasa tace "barka da zuwa, ina yini, ya aiki" murmushi yayi sosai yace "baza akalleni ba Rukayya, idanuwana na kwadayin ganin fararen idanun nan naki masu sanyaya ma Muhammad Ibrahim zuciya" wani irin masifan kunya kalaman shi suka bama Ammi ahankali tadaure tadago kwayoyin idanunta dasuka sha kwalli ta daura akan Dady, wani irin lumshe ido yayi kafin yabude su ahankali ya kalleta murya chan kasa yace "godiya nake yallabiyata" sallama Aneesa tayi ta tsaya abakin kofa tana jiran abata izinin shigowa, ahankali Ammi tace "shigo" shigowa tayi dauke da best tray dinsu mai kyau da maltina mai sanyi ke kai sai kulan tuwo da miyan kuka dayaji wake da kifi da dan bowl dake dauke da ruwan wanke hannu sai goran ruwan Eva maidan sanyi Baffa yasiyo maltinan da ruwa, karasowa tayi ta ijiye tray tace "Abba ga abincin ka nan, Ammi na tadafa ai zaka cinye ko" da sauri yana kallon fuskan Aneesan yana mata murmushi yana masifar son yarinyar yace "kwarai kuwa, tunda Ammi ki tadafa ai dole na cinye harda side kwano" murmushi sosai Aneesa tayi tadan saci kallon Ammi data watsa mata harara tamike tafita daga dakin takoma wurin su Baffa.
Chapter 41 · 0% Book details