← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 71

Sashe 40

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ahankali Abdul dake kallon su Aneesan batare daya kalli Aliyu ba yace "is she the one Leo?" jin shiru Aliyu bai amsashi ba yasa ya juyo ahankali ya kallai su ya gani yana kallo idanunshi sunyi ja sosai kirjinshi na bugawa da sauri sauri danko shi yana ganin yanda kirjin ke sama da kasa tagaban rigan, da sauri yace "Leo, Leo are you okay?" wani irin bude kofa Aliyu yayi yafita daidai lokacin Yusuf ya zura hannu a aljihun wandon shi yaciro dari biyar ya mikama Aneesa yana murmushi yace "ga wanan asai su lemu asha Aneesa" da sauri ta girgixa kai tajuya zata shiga gida tace "kabarshi nagode, saida safe" hannu yasa yakama hijabinta yace "a'a wlh saikin karb......" wani wawan mari aka dauke shi dashi dayasa Aneesa dake kokarin bude kofa juyowa da sauri dan bama tasan yarike mata hijabi abinka damai dogon hijabi, hada ido tayi da Aliyu da idanunshi sukai jajir yana wani irin kallonta, Yusuf dafe kuncin shi yayi dan marin ya mugun shigan shi yana kallon fuskan Aliyun, dauke kai Aliyu yayi daga kallonta ya fizge hijabinta daga hannun Yusuf din yanamai wani irin kallon tsana jiyakr kaman ya chakamai wuka, janye hannu Yusuf yayi daga inda Aliyu yamai marin ya kalli Aneesa yace "waye wanan Aneesa?" cikin fushi Yusuf ya kalli Aliyun yace "kasan koni waye dakamare ni, kasan me tsakanina da Aneesa, kasan tun yaushe nasanta nake rainon sonta axuciya kasan koni waye? A whole chief security officer ka mara" cikin mugun zuciya Aliyu yanunamai machine dinshi yace "take your bike and get out of here right now and never come back" "baza'a bar nan dinba, kuma wlh zan nunama kai kuskuren mari na" hannu yadaga zai kodama Aliyu mari da sauri Aneesa ta shiga gaban Aliyun kirjinta na daukan uku uku hakan yasa Yusuf ya tsaya tsak batare dayay marin ba, dan juyowa Aneesan tayi suka hada ido da Aliyun dake kallonta da sauri ta dauke kai ta maida kanta kan Yusuf tama rasa mezata ce gabanta sai faduwa yake itadai kawai bataso Yusuf ya daki Aliyun dan tasan baida karfi, bakinta har rawa yake tace "uhmmm karka marai, yakuri katafi please" cikin fushi Yusuf yace "natafi Aneesa kikace?" gyadamai kai tayi da sauri kaman mai koyan magana tace "uhnnn.....eh, k...katafi" cikin fushi Yusuf ya kalli Aliyun tareda mai pointing idanunshi da yatsu biyu yace "watch out, zakasan katabo haifaffen dan Suleja" yahau kan machine dinshi ya burga azuciye yabar wajen bin machine din tayi da kallo harsaida tadaina hango machine din sanan tajuyo ta kalli Aliyun cikin fushi tace "why did you slap him meruwan ka dashi eh?" cikin tsananin zuciya Aliyu yace "why are you talking to him? Nace kiyi magana dawani ne eh?" ganin yanda yake magana kaman zai daketa yasa ta saukar da kanta kasa batare da tace mai komiba shikuma abinda ya tsana kenan, tsawa yadaka mata kishi kaman zai hadiye zuciya yamutu yama manta da bata da lafiya yace "am talking! Mesa kikamai magana? How dare you talk to him haryana rike miki hijabi" faduwa gabanta yayi cikeda tsananin tsoro da sauri tajuya ta kalli kofar gidansu tsoron kar Ammi taji hayaniya tafito take gashi magrib yayi sai kallonsu masu wucewa ake, bakinta na rawa sosai cikin bacin rai tace "wai me ruwanka dani eh? Kadenamin ihu, karka sakemin ihu" tana gama maganan tai fuuu tabi ta gefenshi zata shige gida hanunta ya rike chak da sauri tadago kai ta kallai, fizgota yayi back azuciye.

_*how to subscribe*_
_zaki turo 300 ta account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na sainai adding dinki a group din danake posting_
_you can also send MTN card 300 for those dabasu da account_
_duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa_
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

3⃣0⃣

Kaman ya jawo tsinke haka tadawo luuu numfashinta na fita sama sama kaman zata suma, cike da masifa sosai kaman zai daketa Aliyu yace "how dare you walk out while am still talking to you" kasa magana tayi sai hanunta datake kokarin fizgewa, kara matse hannun yay da kyau dayasa ta runste ido da karfi sabida zafi, cikin muryan fushi Aliyu yace "get this straight I love you Aneesa, I Love You and I don't share what I Love, koma waye kike tareda su kirabu dasu this should be the last time dazan kara ganin kina magana dawani inba hakaba u will see my other side, and you're not gonna like that, last warning!!!" sakin hanunta yayi azuciye yawuce wajen mota, dago kai tayi tana kallon motan daya bude ya shiga tana shafa inda yarike dake mata mugun zafi idanunta sun cicciko da hawaye zuciyarta na tafarfasa, da sauri tasa hannu ta share hawayen wani irin masifa yataso mata, wajen motan daya shiga tayi kaman zata tashi sama ta window inda yake da glass din yake arufe ta tsaya, glass din tinted ne bata iya ganinshi dukan glass din tayi da duka karfin ta da hannu hawaye na cika idanunta cikeda masifa tace "ba'a sonka din, ba'a sonka din do your worse, ance ba'a sonka din" yanda take bubbuga glass din motar zaka zaci fasawa take shirin yi, ganin hannayenta namata zafi tsabagen bugawa yasa ta tsaya tasake sa hannu ta share hawayen daya zubomata ta juya tana kallon kasan wajen tana neme neme, hango bawon ayaba datayi ata gaban motan yasa takoma gaban motan da sauri ta tsugunna ta dauko bawon ayaban ta jefama gaban motan da duka karfin ta kaman shitake jefamawa tace "baza'a rabu dasu dinba, nafi son dukan su, mezanyi dakai masifaffe dakai, sai feeling kaman ka isa dakowa sai kace wani dan sarki, dan kazo da wanan akwalan motan mai kama da bons, kuma daga yau ka kara dawowa gaban gidanmu saina faffasama tayoyin wanan bakar motan, mummunan mota kawai" ta tsugunna ta kwashi kasa a hanunta ta watsa ma glass din Abdul ya ware ido tareda kama baki yace "toooooo" da yatsa ta nuna motan tace "karka kara zuwa anguwan nan, kuma kaima last warning, Allah kasake zuwa saina dauko tabarya na rotsa glass din gaban nan" tawuce tai gidansu a zuciye Aliyu nabinta da kallo barinma cute feet dinta da babu safa ajiki dan saiyau yaga feet nata da kyau yatun masu kyau dake dauke da white fitted nails farare fat.
Chapter 40 · 0% Book details