Sashe 27
A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 4 min read
Yana tafiya kaman wani bijimin zaki tsabagen yanda zuciya yazomai wuya. Wani mutumi ne yafito daga cikin cafe da dan gudunshi rike da adaptor a hanunshi yazo wajen Mazimaziz yace "Malam Auwal you have to come with me akwai matsala babba, systems din row 2 are crashing wlh" da sauri yace "wat?!" mikama Aneesa wayan yayi yace "sorry Fateema, sai gobe zamuyi magana kinji, make sure you come early" yay maganan yanabin bayan mutumin da sauri suka shiga cikin cafe daidai lokacin Aliyu yawani iso gabanta yana wani irin kallonta tacikin black glasses din kan idanunshi, dudda bata iya ganin fuskarshi sosai amma saida gabanta yay wani mummunan faduwa, rawa lips dinta suka shiga yi tana kallon fuskarshi ganin yanda yake kallonta kaman zai wani watsa mata kyawawan mari yasa tafara komawa baya ahankali tana kallonshi kafin tajuya da sauri zata koma cikin cafe hanunta ya fizgo chak yarike gam, da sauri tajuyo tana zaro ido ta kallai, hanunshi sanyin bala'i ga taushin tsiya kaman baya aikin wahala, kokarin fizge hanunta tashiga yi tana kallon fuskarshi amma ko gezau baiyiba saima wani irin fizganta dayayi takusa faduwa yay wajen premises din da ita jama'a na kallon su, wani irin bugata yay da jikin mota saida tai kara yasa kafanshi ya daki gefen datake tsaye ajikin motan, jiyake kaman zai mutu da bakin ciki kafin yasa hannu yay punching motan da karfi with all his heart saida wurin yadan lotsa aciki yace "damn it!" sake daukan motan yayi da karfi dahar saida ta tsorata idanunta sukai ja, cikin ihu yace "who was that Man Aneesa? Who is he?" ya daka mata mugun tsawan da saida yasa duka idanun mutanen dake cikin cafe din yadawo kansu, ganin yanda mutane ke kallonsu yasa ta daure sosai tahana kanta kukan dayake shirin zuwan mata, ganin yanda kirjinshi ke tafarfasa hartana hango bugawan heart dinshi tagaban riga yasa tace "c...calm d...dow..." sake buga motan yayi dayasa ta runtse ido da sauri tsabagen tsoro dan har kwakwalwanta takejin karan buga motan, yace "don't tell me to f**king calm down, uban waye wanan katon dakike ta yima murmushi eh?" yasake dukan motan kaman da motan yake fada, shigewa jikin motan tayi jikinta ko ina rawa yake kaman zata tsaga motan ta shige gabaki daya ta kame kamar wata yar sanda, ahankali tadan bude ido ta kallai numfashinta nafita da sauri da sauri, ahankali bakinta na rawa sosai tace "kaga ana kallonmu please kadena dukan motan nan, am so scared, kadena ana kallon mu" punching motan yayi da hannu kaman wanda ya zare yadaki motan da kafa cikin tsananin zuciya dashi kanshi baisan daga ina zuciyan takeba yace "who d f*ck is dat Man?! I said who is he? Talk!" yadaka mata wani mahaukacin tsawan da saida tasake firgita ta runtse ido da sauri jikinta ko ina narawa takasa magana, buga motar ya shigayi ganin takimai magana yace "damn it, damn it, dammmmnnnn it" hanunshi dasukai jajir tsabagen yanda yake punching motar suka shiga rawa kaman wanda ke farfadiya yana kallonta. "I've been calling you, so you are here with this stupid man eh Aneesa" yay ihu kaman zai shige jikinta, buga mota yayi ganin tama maidashi mahaukaci taki cemai komi yace "who is he? Who is he Aneesa kifadamin karkija ma mutumin nan dan he talking to you could cost him alot, tell me who the fuck is he" yasake buga motan, at this point kuka sosai yazoma Aneesa makogoro, bude ido tayi ahankali ganin yanda dalibai duk suka fito wajen Gate din cafe ana kallonsu kaman sun dawo film yasa ta kalli Aliyun dake kallonta bakinta narawa sosai tana kokarin hana kanta kukan dake zuwan mata tace "please please Ya Aliyu stop this you are embarrassing me, ana kallon mu, dan Allah kadena you are embarrassing me" glass din dake kan idanunshi yazare saida taji tsoro dataga idanunshi sunyi masifaffen ja, cikin fushi yanuna cafe da yatsa yace "because saurayin ki na nan shine nake baki kunya eh? Are you telling me this Aneesa, how dare you talk to that man? How dare you?" yanda yake mata ihu yana tozarta ta yasa taji she can not take it anymore, danne faduwan da gabanta yakeyi tayi, ta dake iya dakewa ta kallai tace "to wai meruwanka eh? Meruwan ka dani? Koma dawa nai magana ina ruwanka? Ka sanni ne? Mena hada dakai? Sai bala'i kakemin kaman wata yarka, anyi magana dashi din do you wor....." "Aneesah!" ya daga hannu zai kai mata wani irin wawan mari da sauri ta kawad dakai tareda rufe fuskarta da hijabi gabanta na faduwa gabaki dayan jikinta yadau bari, tsayar da hannun daya daga zai mareta dashi yayi yana kallon yanda tarufe fuskan jikinta narawa sosai kaman an jonata da transformer, ahankali yace "just thank God I love you dasaikin yi nadaman fadamin kalaman nan dakikayi" yamaida hanunshi kasa tareda wucewa azuciye ya shige mota yaja motar d masifar gudu yay reverse da sauri daliban dake gaban gate suka koma ciki danyi yayi kaman zai kadesu yaja motar yabar wajen da masifan gudu zuciyarshi har ciwo takemai tsabagen fushi, ruwan dayaji akan fuskarshi yasa yakai hannu yataba fuskar hawaye ne masu mugun dumi suka gangaro daga idanunshi, da sauri ya share fuskar da bayan hannu yakarama motar gudu.