← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 71

Sashe 48

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 3 min read

Almost to seven Dady da Aliyu daya saka milk jallabiya suka shigo gidan, Daddy ya tambayi Aliyu abinda ke damun shi yafi sau goma dan duk yay mai wani iri, juyawa Aliyu yayi zaiyi hanyar side dinshi Dady yarike mai hannu da sauri ya juyo yana kallon Dady da manyan idanunshi dasukai haske sosai sabida tashin dayayi daga bacci kaman yazuba madara, cikeda damuwa Dady yace "wai bazaka gayamin meke damunka ba Gadanga? Aliyu" Dady ya kirashi da dan tsatsauran murya hakan yasa ya kalli Dad din asanyaye kaman wani mara lafiya, cikin tsatsauran murya Dady yace "nace kafadamin meke damunka wlh Aliyu kasa hawan jinina yatashi just know is you, Son what happen to you dabaka iya gayamin matsalolin ka yanzu? Batun yau nalura abu nadamunka ba tun ranan daka shigo gidan nan hanunka duk bruises, what is wrong? What is disturbing my baby Boy dina Aliyu?" Dady yay maganan cike da sigan lallashin yaro yana shafa kumatun Aliyun, wani irin ajiyan zuciya Aliyu ya sauke arayuwan shi yanason lallashi kodan Dady ya raineshi a hakane oho, jikinshi nason ana lallashi shi, ahankali hawaye suka shiga taruwa a idanunshi batare dayay magana ba yana tuna kalaman Aneesa datana watsa musu kasa a mota she hates him kuma karya kara dawowa anguwan su, ganin yanda hawaye suka shiga xiccikowa a idanunshi yasa Dady yace "subhanallah Gadanga na" hanunshi yaja sukai part dinshi akan kujeran falonshi Dady yazaunar dashi yadawo ta gabanshi yaja center table yazauna akai cikeda damuwa yace "menene? What's bothering you? Maman su Rauda ko any one of them ne suka batama rai komene" girgizama Dady kai yayi yana kokarin hana hawaye zubowa, hannu Dady yasa ya share hawayen yace "to menene kafadamin" ajiyan zuciya ya sauke yana kokarin controlling zuciyan shi, kafin yadago kai ya kalli Dady ahankali yace "I want to go back to California, nagaji da Nigeria, am tired of everything here Dad" wani irin daure fuska Daddy yayi kaman bashi bane ke lallabashi yanzun nanba, strictly babu alamun wasa yace "kaga Aliyu idan kasaka kafa ka kara barin Nigeria nan tokai da matarka ne, ina gayamaka, inbako hakaba to gaskiya kagama tafiya outside, I told you I want you to settle down, marry I want to see my grandchildren, ga yar abokina dana fadama sunyi makaranta da Hajar yau zamata zo gidan nan kace kai a'a da kanka zaka nemo da wace mace kake magana da zakace kai da kanka zaka nemo eh" shiru Aliyu yayi yanajin yanda Dady kemai fada kaman yafasa ihu, agogon dakin Dady ya kalla ganin bakwai tadan gota yasa yamike yace "zamu gama maganan nan anjima, yanzu inaso nakai yaran gidan nan hadda dakaina sabida nai enrolling yar yar new Mum dinka idan nadawo sai muje ka gaida new Mum dinka, go and shower son don't conclude yau idan tazo zaka ganta okay" yay maganan yana bude kofa yafita ajiyan zuciya Aliyu ya sauke kafin yaciro wayarshi daga aljihu yana kallo ahankali ya kunna wayan yay dialing number Aneesa.
Chapter 48 · 0% Book details