Sashe 69
A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 6 min read
Officer ne yanunama Dady mug da tray dasuka saka a forensic Bag yace "Sir he was poison ta wayanan abincin biyu, coffee akwai high level a poison a coffee nan sanan akwai a pancake dinan bari kaga" kallon daya daga cikin ma'aikatan yayi yace "get me water" da sauri mai aikin yatafi dauko ruwa officer kuma ya tsugunna ahankali yay unzipping bag din already da safan hannu a hannunshi yaciro mug din sanan yaciro pancake din daidai Gardner yakawo ruwa a babban buta karba officer yayi, ahankali Officer ya tsiyaya ruwa kan empty coffee mug din chaaaa ruwan yahau kumfa amma ba sosai ba sabida babu coffee saiya tsiyaya ruwa kan pancake din saiga kumfa shima nan wurin yadauki hayaniya, mikewa tsaye officer yayi ya kalli Abba daya tsaya yana kallon ikon Allah yace "waye yabashi abincin nan?" cikeda mamaki Dady yace "Aneesah nace tamai pancake da coffee but ai Aneesa can't do this" da sauri officer yace "waye Aneesa" juyawa Ammi da gabanta kewani irin faduwa tayi takira Anessa dake gaban flat dinsu alamun tazo fara zuwa tayi gabanta na dukn uku uku daidai nan wasu polisawa guda biyu suka fito daga part din Ammi, wani katin nagani suka mikama ogan nasu daidai Aneesa ta iso wajen ahankali tace "gani" da hannu officer yadaga mata yace "tsaya tukunna" ya kalli Dady yamai pointing flat din su Ammi yace "wacece mai flat dinchan" da sauri Dady yace "amarya tace gatanan" yamai pointing Ammi dake kallonsu, dan ajiyan zuciya officer ya sauke yamikama Dady katin maganin yace "ga poison din da aka sama Aliyu a abinci nan, a bolan gaban kitchen din flat din amaryan ka aka gani" da sauri Ammi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wakhlifni khairan minha" taron jama'an yadauki kara kaman jira ake akira sunan ta Maman su Rauda tace "Allahu akbar ana zaton aga wuta tamakera sai akaga akasin hakan" cha cha cha sukahau yada kananun zancen duk Dady najinsu amma idanunshi nakan Ammi ne dayaga hankalinta yatashi and zuciyar shi bataso ta yadda itace no she can't betray him like that, kallon officer yayi yace "officer are you sure wanan poison ne sanan are you sure a bolansu aka gani?" ahankali officer yace "gasunan daga shashinta suka fito ai bari kaga" tsugunnawa yasake yi duk aka bishi da kallo akai shiru ballo kwaya daya yayi yajefa a ruwan mug din kofin wani iri chichi hi ruwan yayi yafara komawa bakin kirin salati aka dauka ana tafi da sauri Ammi tace "Alhaji me zamuyi da irin wanan maganin, tunda nazo gidan nan ko ciwon kai bamu yiba bamamu da nagani balle har munsami wanan za....." hannu officer yadaga mata yace "excuse me Madam ban katse kiba saura abu na karshe" wani karamin leda yamikama Dady da dan kunne kwaya daya keciki yace "wanan earing din kwaya daya munganshi akasan uwar dakan Aliyu ne" da sauri Dady yaciro dankunnen daga leda yadaga sama yace "dan kunen waye wanan?" faduwa gaban Aneesa yayi da sauri tasa hannunta ta taba dayan kunnenta aiko babu dayan da kunnenta, kafe dan kunen Ammi tayi da ido kirjinta na bugawa ganin dan kunen Aneesa ne tama kasa magana, ahankali Aneesa tadaga hannunta bakinta na rawa tace "n....n...nawane Abba" shewa Mama tadauka tace "ahayye nanaye idan baka mutuba zakaga abu aduniya" cikin fushi Dady yanuna Mama da yatsa yace "wlh kika sake cewa wani abu anan saina katseki da mari wawiya kawai" yajuya ya kalli Aneesa anatse yace "meyakai dan kunenki dakin Aliyu?" rawa jikinta yahauyi datama rasa dalili dawowa tayi kaman wacce bata iya magana ba kodan sabida yanda kowa na wurin kallonta ne oho bakinta narawa tace "y....ya... Aliyu yace nakawomai abincin bangaren shi cikinshi na ciwo bazai iya zuwa ba" da sauri officer yace "ta ina ya ganki yafada miki hakan?" bakinta narawa sosai tace "w....wa...ya" gyadakai officer yayi yace "ke kika dafa abinci ko kawai baki akayi ki kaimai?" ahankali tace "nina d...afa" "okay keda waye a shashin dakika dafa abincin" "n...ni kadai ne Ammi na wurin Abba?" "tun yaushe Ammi naki ta tafi wurin Abba? Kin fara abinci ko baki faraba?" muryanta narawa sosai tace "ban faraba....l...okacin" dan murmushi officer yayi yanuna mata katin maganin poison din yace "Aneesah sunan ki ko?" da sauri ta gyadamai kai, ahankali yace "kigayamin gaskiya, ni inhar mutum yafadamin gaskiya to komi na zuwan mai ta sauki inyamin karyane yakecin bakar wuya, a ina kika sami katin maganin nan? Kowani yabaki kisa karkimin karya bazan miki komiba, fadamin a ina kika sami katin nan? Wayabaki kisakama Aliyu a abinci?" girgixa kai Aneesa tayi hawaye ya gangaro tace "wlh, wlh nibansan katin maganin nanba, ni wlh banma taba ganinshi arayuwata ba wlh kuwan" hawaye suka zubo sharrr ta share da bayan hannu, murmushi Officer yasake yi yace "kin tsani Aliyu kin tsani Aliyu, luckily sai jiya babanshi yace kidafa mai abinci, sai abin yazama babu kowa adakin shine kika ciro magani kika samai danyaci yamutu hakane Aneesa?" fashewa da kuka tayi sosai tazo kusada Ammi tarike Ammi gam cikeda tsoro tace "Ammi kicemusu ni wlh bansan maganin nanba, ni bazan taba kashe Ya Aliyu ba wlh wlh kuwan" tafashe dawani irin kuka ajikin Ammi ahankali Ammi ke kallon Dady dayay shiru yana kallon Aneesan dake kuka girgiza kai yayi yace "No officer kubar yarinyar nan trust me something happen, Aneesa bazata iya kisa ba, dan ita tadafa abinci doesn't mean ita tasaka poison, banda haka ba itakadai ne agidan nanba sanan kowa anan can enter bangaren Aliyu" cikeda rashin kunya da rashin mutunci Maman su Rauda tace "me kake nufi Alhaji Aneesa bazata iya kisa ba to mune kenan zamu iya? Sonkai kiri kiri sabida yar gaban goshin kace, mukake zargi kenan mune zamu iya ko, nagadai akwai CCTV agidan aje aduba mana hakanan nifa na tsani zargi koba hakaba Amina" da sauri sukace hakane wlh, officer ne ya kalli Dady yace "Sir akwai CCTV agidan nanne?" gyadamai kai Dady yayi yace "akwai a compound dinan, banda haka akwai CCTV a bangaren Aliyu dashi kanshi baisani dashi ba, CCTV tareda kwan lantarkin dakinshi yake, nasaka ne sabida nasan matayena sun tsaneshi zasu iya komi akanshi saisa nasaka?" da sauri officer yace "ina zamuga footage din" "muje yana secret room dina" ya kalli matan yace "kar wacce ta tafi daki kujiramu anan" hanyar flat din Mama Dady yayi da Officer, wani irin murmushi Mama tayi zuciyata tai sanyi dama takira CCTV ne sabida tasa aduba, Dady yazaci shi kadai ysan password din shiga dakin baisani batun yauba tasan.
Dakin Mama sukayi sukai sama, agaban wani daki ya tsaya da handle din kenan kaman waya ga boturan dannawa, password din yasaka saiga dakin yabudu computers ne wurin shiga adakin, straight computer bangaren Aliyu Dady yanuna musu, officer ya zauna gaban computer yay rewinding back har zuwa footage din jiya, rewinding sosai yayi har zuwa daidai inda Aneesa tazo part dinshi ahankali yace "got it" tsayawa Dady yay akanshi ya shiga kallo kirjinshi na bugawa shigowa part din tayi rike da tray ta kalli ko ina kaman tana neman wani abu kafin suga tai tafiya da sauri ta shiga falon ta sauke tray din kan center table tana kalle kalle, sai sukaga ta chusa hannunta agefen zaninta basuga metayi ba sundaiga tafito da kwaya daya ta jefa a mug saikuma tadauko daya ta dagargaza kaman yanda ake dagargaza magi da hannu ta barbaza kan saman pancake ta kakkabe hannunta tadauka da sauri tai hanyar bedroom dinshi tabude kofa ta shiga dayake babu CCTV a bedroom dinshi basusan meya faru ba sundaiga chan tafito daga dakin aguje, baya Dady yayi zai fadi tsabagen yanda heartbeat dinshi yay weak polisawan suka tareshi suna salati wani irin fincike kanshi Dady yayi yafita daga dakin da mugun zuciya.
Dakin Mama sukayi sukai sama, agaban wani daki ya tsaya da handle din kenan kaman waya ga boturan dannawa, password din yasaka saiga dakin yabudu computers ne wurin shiga adakin, straight computer bangaren Aliyu Dady yanuna musu, officer ya zauna gaban computer yay rewinding back har zuwa footage din jiya, rewinding sosai yayi har zuwa daidai inda Aneesa tazo part dinshi ahankali yace "got it" tsayawa Dady yay akanshi ya shiga kallo kirjinshi na bugawa shigowa part din tayi rike da tray ta kalli ko ina kaman tana neman wani abu kafin suga tai tafiya da sauri ta shiga falon ta sauke tray din kan center table tana kalle kalle, sai sukaga ta chusa hannunta agefen zaninta basuga metayi ba sundaiga tafito da kwaya daya ta jefa a mug saikuma tadauko daya ta dagargaza kaman yanda ake dagargaza magi da hannu ta barbaza kan saman pancake ta kakkabe hannunta tadauka da sauri tai hanyar bedroom dinshi tabude kofa ta shiga dayake babu CCTV a bedroom dinshi basusan meya faru ba sundaiga chan tafito daga dakin aguje, baya Dady yayi zai fadi tsabagen yanda heartbeat dinshi yay weak polisawan suka tareshi suna salati wani irin fincike kanshi Dady yayi yafita daga dakin da mugun zuciya.