← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 71

Sashe 22

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 4 min read

Fuskarshi ta kalla ganin driving dinshi yake hankalin shi nakan hanya yasa tamika hanunta dake rawa sosai ta karbi wayan tai picking takara akunne. "Aneesa kina ina yanzu?" ahankali tace "muna hanya" da sauri Ammi tace "mutumin ne zai kaiki?" gyadama Ammi kai tayi ahankali tace "eh shine" dan ajiyan zuciya Ammi tasauke tace "to Alhamdulillahi, dazaran kunkai bakin titi akwai Motocin Suleja dayawa saiki shiga kinji idan kin shiga ki kirani ki sanar dani kinji, kidena kuka babu abinda zai saman mini ke okay" gyadama Ammi kai tayi tace "tom" katse wayan Ammi tayi hakan yasa ta janye wayan daga kunenta ta ijiye akan cinyarta tana sauke ajiyan zuciya, ganin sun shigo kan titi yasa ta kallai ganin har lokacin hankalinshi nakan titi yasa tadan gyara murya danji tayi muryan ta yadishe sosai sabida kukan datayi, ahankali tace "uhhhh anan, anan kan titi Ammi na tace na sauka" dan juyo dakai yayi ya kalleta suka hada ido dan lumshe ido kadan yayi yabude kafin ya maida hankalinshi kan tukin dayake yi batare dayace mata komiba, ringing da wayarshi yayi yasa ya kalli wayar dake ajiye gefen shi ganin Abdul ne yasa baiyi picking ba dan yasan nemanshi yakeyi, saida yasake kiranshi akaro na biyu sanan yadaga wayan yakara akunne yay shiru. "where are you Leo? Nafito banmaga motanmu ba don't tell me kakoma gida, waikai wani irine eh fisabilillahi fa, he's our friend fa, haka kakeso amana ranan bikin ka eh? Duk abokanen ka suki zuwa sabida baka zuwa nasu?" dan yatsine fuska yayi yace "kacikani da surutu am driving fa" "driving? Driving to where?" dan murmushi yayi kadan yace "idan nadawo we will talk, am tired yanzu" ya katse wayar yamaida kan cinyarshi, ta gefen ido yaga sai share hawayen dasuka shiga zubo mata takeyi hakanan batasan mesa taji tana shakkanshi ba, takasa mai magana dudda batasan inda zai kaita ba, kuma gashi Ammi tace akan titi zai sauketa tahau motan dake kawo mutane Suleja, itadai yau tata takare, bata tabayin dare haka awuriba, tunanin hakan yasa hawaye sai zubowa daga idanunta suke, dan murmushi yayi yasa hanunshi a aljihu yazaro wani clean soft handkerchief dake wani cool kamshi yamika mata, kallon handkerchief din tayi kafin tasa hannu ta share hawayen dake kan fuskarta ta girgizamai kai batare data karba ba alamun a'a, ajiye mata handkerchief din yayi akan cinya yamaida hankalinshi kan tuki fuskarshi nakan hanya, sai share hawaye take dasunki tsayawa saida taga wani signboard an rubuta Suleja 20km yasa tai wani irin murmushin kuka, juyawa tayi da sauri ta kallai juyowa shima yayi ya kalleta dawani irin calm look da yatsar shi yamata pointing handkerchief din dayabata dake kan jikinta, da sauri tadauki handkerchief din ta share fuskar ta tass tareda sauke wani irin ajiyan zuciya mai kara dahar saida yaji, dan murmushi yayi ganin yanda ta natsu dataga sundau hanyan gida.

Gudu yake sosai basu wani jimaba ya kai Sulejan sanan yarage gudu yadan kalleta cikin calm voice dinshi yace "show me the road to your house" gyadakai kai tayi tasa hannu tana nunamai hanyar yanata bi har sukakai anguwan su, a kofar gidansu ta hango Ammin su tsaye sanye da dogon hijabin ta hanunta rikeda waya, da hannu tamai pointing Ammi tace "ga Ammi na nan" rage gudu yayi tareda rage karfin wutan gaban motan sabida karya haska Ammin sosai tun kafin yay parking tawani irin bude motar da gudu tai wajen Ammi data tsare motar da kallo. "Ammi, Ammi, Ammi" kafin Ammi tace ma wani abu taje da gudun gaske tai tsalle ta rungume Ammin kaman wacce tai shekara bataga Ammin nataba, rungumeta tight Ammi tayi tanama Allah godiya. "Alhamdulillah" kafin ta dagota daga jikinta takama habarta da hannu daya tasa dayan hanunta tana share mata fuska tace "Alhamdulillah Allah nagode maka, you are ok ko Aneesa na?" hannun Ammi ta rike tareda gyada matakai tana murmushi hakan yasa Ammi tasake sata ajikinta ta rungumeta, shiru yayi ya tsaya a mota yana kallonsu, looking at affection din Ammi towards Aneesa yasa yaji he just wish Mummy shi was alife to hug him like this, he miss his mum so so sooo much, lumshe ido yayi ahankali zuciyanshi namai wani irin zafi.
Chapter 22 · 0% Book details