← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 71

Sashe 17

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 6 min read

_Free page_
Shigowa dakin Dady yayi sanye da jallabiya fuskarshi lema leman ruwa alamun kaman alwala yayi hada ido sukayi da Dady yana zaune kan kujera, bedroom dinshi Dady yawuce baiwani jima acikiba yafito dawani white iron jallabiya mai kyau namaka yafito daga dakin nashi yace "tashi kasa mutafi masallaci" turo baki yayi yana karasa shan yoghurt dinshi yace "ni banyi alwala ba" ajiye jallabiyan Dady yayi kan saman kujera yazo inda yake ya karbe cup din hanunshi yace "you and yogurt, give me the cup" ya karbe cup din ya ijiye akan center table yace "to tashi kashiga nan visitors toilet kadauro alwala Son, kaga anma fara kiran salla" gyadamai kai yayi yamike tsaye ahankali yana tafiya kaman baison yi ya shiga bayin Dady yabi bayanshi da kallo kafin yadau cup din yogurt din daya ijiye yawuce kitchen yaje ya ijiye a cikin sink, fitowa yayi daidai shima yafito daga bayin daure da alwala Jallabiyan Dady yadauka yamikamai karba yayi yasaka suka fita daga dakin sukai masallaci Dady nabashi labarin yanda yayi dasu Mama da Khamis dazu har mari saida yama Khamis lafiyayyu guda uku da yaso ya kulleshi ma da kyar yahakura bayan sunbabbashi hakuri, murmushi kawai yayi yanajin Dady harsuka shiga masallaci. Saida sukai isha'i sanan suka dawo gida zaiyi part dinshi Dady yace "let's go to side dina muyi dinner" girgixa kai yayi yanadan lumshe ido ahankali yace "am sleepy and am not hungry Dad, I love you gud night" tsayawa Dady yayi yana kallonshi kafin yadan numfasa yace "shikenan gud night kiddo I love you more" turo bakinshi yayi yace "Daddd kiddo kuma" hancinshi Dady yaja yace "kafito da mata namaka aure kaga idan nakara kiranka da Kiddo" dan dariya yayi yace "nay nay na" tallabe keyanshi Dady yayi yace "zakaci gidanku da nay nay na ne, motar waye a pake a gaban side dinka?" Dady yay maganan yana kallon gaban shashinshi dansai yanzu ya lura da motar, juyawa yayi ya kalli shashin dan murmushi yayi yace "is Abdul Dady, bye gud night bari naje" yafada da sauri yana tafiya, murmushi Dady yayi yace "su aboki anzo har ana sauri ko an manta dasu Dady" juyowa yayi da sauri jin maganan da Dady yayi da sauri yaje ya rungume Dady yay lamo a jikinshi ahankali yace "you know you are the best Dady in the whole world" shafa bayanshi Dady yayi yana washe baki yace "and you are the best son in the whole world Aliyu am a proud father to this yaro maijin magana just a lil stubborn and annoying atimes" dariya dukansu suka fashe dashi a tsakar gidan atare kafin sundanyi shiru yana jikinshi har lokacin, murya chan yace "Dad" anatse Dad dake rike dashi yace "na'am Gadanga na" ahankali yace "you are my Dady and My Mummy, kamaye gurbin Ummi, baka taba bari naji kewanta ba, you feel that hole in my heart, you are my everything Dad, and happy Fathers day" rungume shi tight Dady yayi his heart is so swollen kalman Mum daya fada yasa yatuna da marigayiya matarshi the best wife daharyau yakasa samun kamanta shiru sukadanyi for a while kafin yasaki Aliyu yana share hawayen dasuka cikamai ido da sauri dan karya gani sanan yay murmushi yace "wuce katafi Abdul na jiranka, zan aiko muku da abinci" gyadamai kai yayi ahankali yace "bye Dady" "bye son" juyawa yayi yay part dinshi Dady ya tsaya yana kallonshi saida yaga shiganshi yawuce yay part dinshi shima.

Ahankali yabude door din part dinshi babu kowa a falon sai manyan jakunkunan kwali da aka rubuta Men by Robanni wears ajiki hakan yasa yagane kayan bikin dazasu sakan gobene Abdul ya karbo musu din, hanyar bedroom dinshi yayi, bude kofa yayi ya shiga babu kowa adakin sai car keys da waya dake kan gado karan ruwan dayaji yasa yagane yana bathroom, dan ajiyan zuciya ya sauke ya zare jallabiyan jikinshi yay hanging a hanger yasaka a wardrobe sanan yazo yafada kan gado.

Bude kofan bathroom da akayi yasa yadago kanshi wani guy ne kusan kansu daya da Aliyun saidai Aliyu yadan fishi dan kaurin jiki dakuma haske dan Aliyu farin sosai Abdul ma farine but baikai Aliyu haske ba, fitowa Abdul yayi daure da towel a waist harara yana rike da karami a hannu dayake goge gashin kanshi dashi yazubama Aliyun dayay lamo akan gado yana kallonshi yace "dan iska kafin laifi kawani kwanta forming innocent right, kama ta shine malam" yay gaban mirror yana tsane jikin da towel kafin yaje gaban wardrobe din Aliyu yabude yadauko daya daga cikin pyjamas dinshi milk color yasaka sanan ya shiga bayi yaje yay hanging towel din back sanan yafito yay kan gadon ganin zai fado kanshi yasa Aliyu yatashi da sauri yanadan dariyan shakiyanci yace "leave me alone jor, karka karyani, shine kazo koka kirani" wayarshi dake kan gadon yadauka yace "I know kana mosque saisa I didn't call, wait before anything am hungry" hararan shi Aliyu yayi yatashi daga kan gadon yace "chop chop, Dady zai aiko mana da abinci, let's go, muje falo" tashi Abdul yayi yabi bayanshi suka fita falon daidai lokacin akai knocking kofa, Abdul ne ya amsa shikuma Aliyu yafada kan kujera. "yes come in" bude kofa akayi bodyguard su biyu na Aliyu suka shigo dakin daya dauke da manyan warmers guda biyu sai dayan kuma dauke da tray da slice fruits a bowls kekai, dining Aliyu ya nuna musu suka kai abincin wajen sanan suka juya suka fita, hanyar dining din Abdul yayi yazauna yana bubbude warmers din yana kallon abincin dake ciki kafin yadau plate da spoon ya debi ofada rice da smoke fish stew ya ijiye a gabanshi, wani bowl yasake dauka yadau spoon yacika bowl din da fried pepper chicken sanan yadaga kai ya kalli Aliyu dahar ya kwanta akan kujera yana daddana remote yana lumlumshe ido yace "let's eat Leo" yatsine fuska yayi yace "me aka dafa? Me acikin warmers din?" hararan shi Abdul yayi yafara cin abincin shi batare daya kulashi ba dan yaga iskanci Aliyu keji shikuma right now he's starving bari yabama cikinshi hakkinshi tukunna yanda Abdul kecin abincin was tempting his taste bud ahankali yatashi daga kan kujeran ya mike tsaye, dariya Abdul yafashe dashi ganin yatashi, karasowa dining din yayi yaja daya daga cikin kujerun dining din na kusada Abdul din dakemai dariya ya zauna fizge spoon din hanun Abdul din yayi yaja plate din rice din ya shiga ci, dariya Abdul ya shiga yi yace "nadaiji shege waya gayama anama abinci yanga" yay maganan yana daukan wani spoon suka shiga ci tare, he hardly eat much but because yanaci tareda wani sosai yaci abincin har Abdul na karamusu sukaci, baiwani ci pepper chicken din sosai ba yazuba juice ya kwankwada shikuma Abdul yaci tass, saida suka gama yace "this fruit kasasu a fridge Leo ni banda inda zasu shiga acikina while I clear the dining" gyadamai kai yayi yatashi ya dai bowls din yakai fridge shikuma Abdul ya kwashi plate yakai kitchen.

Gamawa sukayi sukai falo Abdul yadau jakunkunan kayan su yace "kaga kayanmu gobe zamu fita dawuri fa, mune abokan ango" tabe baki yayi yadan shafa kai yace "am sleepy sosai bangane mekake cewa, let's go to bed" waya Abdul yadauka yana gyara kwanciya kan kujera yace "kai kaje ni waya zanyi da" ya kashemai ido, tsaki Aliyu yayi yay hanyar bedroom yace "dan iska aikin kenan soyayya" daga murya Abdul yayi yace "bari kafara naka bazaka bari muhuta ba, kardai kazo kana mana kuka idan tace bata sonka" daga murya yayi daga bedroom yace "never" shima daga murya Abdul yayi daga falo yace "is a bet" tsaki Aliyu yaja yana cire rigan jikinshi yace "rubbish, why will I ever cry over soyayya? Allah kyauta" yatabe baki ya shiga bathroom yana tafiya da kyar so yake yay wanka yazo yay bacci.
Asuba tagari!!!!
Chapter 17 · 0% Book details