← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 71

Sashe 13

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tanunamai gefen cikin Khamis, farin hanunshi Aliyu ya kalla ya dunkule ahankali yana kallon Aneesan data cije lebe irin ya dunkule hanunnan da kyau dinan tana kallon hannun tana nunamai cikin Khamis din dake sosa ido, daddagewa Aliyu yayi yabugama Khamis uban nishi aciki atare daga Aliyun har Khamis din sukai ihu harsaida Aneesan takoma baya da gudu dan tsoro sabida ihun da Aliyu yayi yana yarfe hannu kaman zaiyi kuka ya kalleta yace "it's hurt, ahhhh, aucchhhh, alottt" sosai yake yarfe hannu hakan yasa ta matso ahankali tana leken Khamis din daya zube akasa dan naushin ya shigeshi gashi yakasa bude ido balle yarama, tsayawa kusada Aliyun tayi dake yarfe hannun nashi dayay jajir tasaka yatsa abaki tana cija danso take suci uban Khamis sosai, kalle kallen compound din ta shiga yi kafin idanunta su sauka kan rigan Khamis din dayacire ya yar da sauri tai wurin rigan tsugunnawa tayi ta dauka ta shiga wurga rigan tana kaman lilo dashi rigan ya shiga kanannadewa danso take tamaida rigan dorina, binta da kallo Aliyu yake yana murza hanunshi harsaida tagama tazo gabanshi da sauri ta mikamai dorinar rigan tace "gashi yayan mu, rama mana da wanan tunda baka iya fadaba, yimai shegen duka da wanan" tamikamai rigan, karban rigan yayi yana kallon fuskarta, nunamai Khamis din tayi tace "zaneshi karka ragamai, ko akotu irinsu bulala tamanin ake musu kaima yimai 80" da sauri ya kalleta yace "80?" kallonshi tayi akaro nabiyu idanunsu yakara sarkewa faduwa gabanta yayi hakan yasa ta kyafkyafta ido sau biyu ta gyadamai kai batare data iya magana ba ta kawad dakanta, ahankali Aliyu yakarasa inda Khamis din yake azube yana sosa ido ya daddage ya shaudamai ihu yayi. "Aliyu wlh idan idanuna suka bude saina kasheka dagakai har shegiyan na..." zubamai nabiyu Aliyu yayi da karfi hakan yasa Rauda ta rungume Aneesa cikeda murna suka shiga tsalle kaman sunsan juna Aneesa harda tafi wani masifar dadi takeji fiye da tunanin mutum, cigaba da dukanshi Aliyu yayi da rigan sunamai tafi itada Rauda harya yarda rigan ya zauna agefe yana haki yagaji, da sauri ta kalli Rauda tace "ina zuwa bari kuga" da sauri tabude gate tafita jakanta tabude ta ciro wani kwababben bakin lalle da mai saida lallenta yahada mata as sample dan kafin tasiya saitasa ya dama mata tadanyi Zane kadan a hannunta ta wanke dan taga iya bakinshi dan kwanaki tasai lalle ko kadan baya baki dudda hydrogen din datake zubamai, shigowa tayi da sauri rike da ledan lallin ta kalli Aliyu tace "Yayan mu daga shi ka zaunar dashi kaga" kasa mata musu Aliyu yayi Yajuya yadago Khamis din da karfi ya zaunar dashi, tace "yauwa rikemin hanunshi tabaya" tsayawa abayanshi Aliyu yayi yarike hanunshi gam, da kyar Khamis dabaya iya bude ido ke magana yace "wlh duk kun shiga uku koba yauba yau ranan kuc...." bai karasa maganan ba Rauda tazare flat shoe kafarta tai bugamai abaki aiko sai jini, dariya sosai Aneesa tayi dayasa dimples dinta lotsawa tana kallon Raudan tace "dama kinada karfin nan tuntuni kiketamai kuka matsoraciya" takarashe maganan tana dariya sosai kafeta da ido Aliyu yayi ko kyafta ido bayayi kaman ance ta kalli gabanta suka kara hada ido shiru tayi ta saukar da idanunta kasa tadan matsa gaban Khamis din sosai kirjinta na bugawa tana gyara bakin ledan lallen, ahankali ta shiga zanamai bullen mage tundaga gefen bakinshi har zuwa wajen sajenshi uku uku sanan taja wani dogon layi tundaga kan hancinshi har zuwa goshinshi shidai Khamis sanyi sanyi da waiwayi waiwayi yakeji akan fuskarshi amma yarasa me akemai, fashewa da dariya sosai Rauda tayi ganin abinda Aneesa tamai harda bubbuga kafa akasa kaman ba itace tagama kukaba da barkakken riganta, mikewa tsaye Aneesan tayi itama tana kallon fuskanshi ta harari Rauda cikeda murmushi tace "am happy you are now smiling nidai nagudu gida, you guys should run for your lives, kugudu kafin idanunshi subude" ta kwasa da gudu tabude Gate tafita da sauri Rauda tabita tana kwala mata kira tace "baiwar Allah, baiwar Allah baki fadamin sunanki ba to" juyowa Aneesa dake kwashe kayanta nakasa awajen Gate din tayi ta kalli Raudan tai murmushi tareda rataya jakanta akafada tace "sunana Nana Fateema" "can we be friends? Inason ki sosai you are so bold wat a fearless lady, a ina kike? Inane gidan ku? Anan Suleja kike?" Rauda tai maganan tana karasowa gabanta murmushi tasakeyi zatai magana idanunta suka sarke dana Aliyu dake tsaye jikin Gate yazuba mata idanu hanunshi zube a aljihun riganshi yana kallonta sosai gabanta yafadi, dan kyafkyafta ido tayi tana kallonshi kafin ta juya da sauri tama Rauda waving hannu tace "bye Friend" daidai lokacin keke napep na zuwa tareshi tayi ta shiga ciki sukai gaba dukansu tsayawa sukayi a inda suke sukabi keke napep din da kallo har yafita daga layin.
[4/5, 8:05 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

1️⃣0️⃣

_How to subscribe_

_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, you can also send MTN card ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting*_

_Free page_
Cigaba da buga kwallon yayi ko ajikinshi dudda dai yanajin yanda hayaniya ke tashi daga falon Dady amma ko agefen kumatunshi, sauran matayenshi Dady sai bude kofa suke suna fitowa suna tafiya falon Dady, tabe baki yayi yace "I hate this house with passion" cigaba da buga kwallon shi yayi yana wuwurgawa a backboard din dake wurin.
Chapter 13 · 0% Book details