← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 71

Sashe 2

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 4 min read

Babu kowa a hadadden palor stairs yahau da sauri yana atishawa ya bude wani hadadden daki da komi na ciki yakenan sky blue color, zama yayi kan Royal bed yanajin sanyi har cikin kashin shi hannu shi ya mika zaidau remote din AC dake kan pillow dake kan gadon wayarshi ya shiga ringing daukan remote din yayi ya kashe AC kafin yaciro wayan daga aljihu daure fuska yayi ganin sunan Dad, kaman wanda akace dole yay picking call din ganin wayar na neman katsewa ya kai kunnen shi yay shiru batare dayace komiba cikin kwantar da murya mutumin yace "yanzu fushi kake da Dadyn ka ko Gadanga na?" shiru yayi baice komi ba ahankali mutumin yace "haba Ali Gadanka gusar yaki, yaron baban shi tashi kadau rigan sanyi kasaka kaji Mr Aliyu Adult" dan murmushi yayi dan yasan cikeda tsokana Abban shi yafadi haka. "yauwa tashi to kasaka kaji" "uhm" yafadi yana sauka daga kan gadon yakarasa gaban wani mirror wardrobe dake bangon dakin yana kallon kanshi har hancinshi yay jajir sabida sanyi wani boturi ya danna kofar wardrobe din yabude ya ijiye wayan kan stool din wajen yaciro wata dark sweater mai kyau yasaka tamai mugun kyau yakara fito da hasken fatarshi, daukan wayar yayi yamaida kunenshi Daddy yace "kasaka sweater?" gyadamai kai yayi yace "eh" "yauwa ko kaifa kaga yanzu sanyin zai ragu, stop acting stubborn kaji Aliyu na, I know you sama d kowa, I know how fragile you are bakason iska dayawa, abu kadan mura mura, you need to take care of yourself okay saisa ma nace zakadawo Nigeria kawai ko hankalina ya kwanta" kaman zaiyi kuka yace "Dadddd" "common don't Daddy me my friend" cikin muryanshi mai bala'in dadi da taushi yace "Nigeria weather is super harsh Dad, I don't wanna come back please nika kyaleni" cikin Dan kakkausar murya Dady yace "nakiya, anki a kyaleka din" saikuma yay shiru kafin yadan sassautar da murya yace "haba Gadanga na, eh babana, mai sunan Abba, kafa gama project dinka kagama komi, I've missed you badly, kadawo gida lemme arrange everything idan akwai any available flight gobe kabiyo kadawo gida inda cibiyarka take, kana dawowa kaga saimu nema maka mata kai aure abinka ka ijiye iyali ko Son?" kwanciya yayi akan gadon yaja bargo ya lulluba tareda lumshe ido ya gyara wayan akan kunenshi yace "nikadena min maganan aure, idan shizakamin bazan ma dawoba, women are so lousy I don't think I can ever live with one" da sauri Dad yace "no, no bashi zanma ba, muma bar maganan, please kadawo kaji" ahankali yace "alright but not tomorrow akwai abunda zanyi saidai next tomorrow or rather on Friday kawai" "har Friday, yaufa Tuesday Aliyu, kana nufin nan da kwana uku, please on Thursday kadawo kaji Gadanga na" shiru yadanyi saikuma ya nisa yace "ok Dad" murmushi sosai baban nashi yayi har hakan yasa shima ya murmusa jin mahaifinshi na murna sabida ya yarda zai dawo. "kaci pancake yau kuwa?" yatsine fuska yayi yace "naay" "why? Maiya hanaka cin fav dinka?" kaman zaiyi kuka yace "bakai kabatamin raiba you ruin my day Dad" cikin dan tashin hankali yace "nizaka ma shairi Gadanga?" dan murmushi yayi batare dayace komiba. "karka damu idan kadawo akwai wani pastry shop dat makes d best pancakes, I can testify to that dan ranan danaci pancakes dinsu
saida tastbud din yay rawa zan aika a sayoma harda Valvet cake ma zakaci kaci har sai kaci kature yafi na California ku dadi I promise Nigeria yanzu mun cigaba muma" dan murmushi yayi yana lumshe ido, murya chan kasa agajiye yace "okay Dady" "you are sleepy ko wanan danaji muryanka chan kasa" gyadamai kai yayi yace "yeah" "alright Son, sleep kaji please allow your bodyguards to do their job kaji Son, am paying them just to take care of you, you are too fragile so kadena hanasu kula dakai, now sleep nima am about to enter Chamber, I love you" murya chan ciki yana kara nitsewa cikin gado cikeda gajiya kaman wanda yay dako yace "love you too Dad" katse wayar baban nashi yayi tsabagen gajiyan dayayi yakasa janye wayar daga kunenshi ya juya ya kara narkewa cikin bargo bacci mai shegen dadi yay awon gaba dashi.

_Suleja, Nigeria._
Chapter 2 · 0% Book details