← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 71

Sashe 26

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ciki ta shiga ko ina dalibai da kyar tasamu taje gaban kanta daya daga cikin ma'aikatan ta gaida tace "malam dan Allah nazo registration ne yaya zanyi?" zufan daya cika goshin shi ya goge dan wajen is so crowdy dudda akwai manya manyan fankoki amma kaman bakomi wani takarda ya nunamata yace "keji ki rubuta sunan ki, za'ayi ta kiranku according to numbers ne" gyadamai kai tayi tace "nagode" tawuce da sauri wajen paper dataga wasu dalibai na rubuta sunansu tsayawa tayi abayansu suka gama sawa sanan taciro byro daga jakanta ta matsa tareda daukan paper number 178 anan zata sa suna, kambu mutane har nawa agabanta itada awa biyu madam tabata sunanta tarubuta kaman wacce ke tsoron paper duk tunani ya kasheta. "Fateema Rufa'i Mai Kwato!" da sauri ta daga kanta jin ankira full name dinta ware ido tayi ganin wani malamin su daya koyar da ita tun daga SS1 a makaranta har zuwa SS3, shine malamin further mathematics dinsu, Malam Auwal Mazimaziz haka yan makaranta suka radamai ko maganan shi ake idan kace Malam Auwal baza'a taba ganewa ba saidai kace Mazimaziz kokuma kace dy/dx daga wani bene taga yake saukowa rikeda wasu takardu da yawa a hanunshi yana kallonta dogon namiji ne handsome black dashi yana sanye dawata faran yadi kanshi da hula yana kallonta murmushi tayi sosai tana kallonshi harya karaso mutumin data tambaya dazu yaje wurinshi yabashi takardun sanan yakaraso ta inda take akunyace tace "good morning Malam" murmushi yayi shima yace "good morning Fateema" murmushi tayi tace "Malam dama kananan" dan hararanta yayi yace "look at you tunda kukai waec da Neco muka sallameku kin kara waiwayan school kizo kidubamu ne? Inda kinzo aida kin gani ai mara zumunci kawai" a kunyace tarufe fuskar ta da Hijabi ita tai mamaki ma dayake mata fara'a haka Mazimaziz ai shine the most wicked Teacher a makarantan su, ko sajent saiya sallama mishi a iya duka, gashi ko test dinshi kafadi saiyay duka sunci dukanshi a makaranta kaman ba gobe. "jamb kikazo siya?" tambayar dayayi ya katse mata dan tunanin dataje da sauri ta gyada kai tace "eh nazo ai registration amma mutane nice number one hundred and seventy something" dan murmushi yayi yana zama akan kujeran gaban kantan yace "banda abinki ai da sassafe ake zuwa dan dalibai nada mugun yawa anan" dan zaro ido tayi kaman zatai kuka tace "bansani ba ne wlh" dan shiru yayi yana kallon fuskarta yanda tai kaman zatai kuka tana kallon wajen yanda aka cika ko ina. "Fateema" da sauri ta juyo ta kallai mikewa tsaye yayi yace "lemme see you off, kizo gobe da sassafe as early as seven zansa wani yay miki, ko yanzu ma aiki yamai yawane danasa yay miki but kizo gobe as early as seven fa kina jina" gyadamai kai tayi tana binshi abaya suna kukustawa dan fita daga wurin tace "okay sir" fitowa sukayi tana biyeda shi wani irin mummunan faduwa gabanta yayi Aliyu tagani tsaye yana sanye da jeans black dawani sky blue shirt yadan bude boturin kirjinshi idanunshi sanye da bakin glass ya rungume hannunshi a kirji dayake rikeda wayarshi Samsung galaxy fold, yana facing cafe din, yan matan premises din Cafe sai kallonshi suke dan yay bala'in yin kyau kaman bature, da sauri ta dauke kai daga kallonshi kirjinta na dukan uku uku ya akayi yasan tana nan? Ya akayi yabiyota? da sauri zuciyata yace a'a bake yabiyoba hala yakawo wanan kanwar tashine itama tai registration din jamb bake yabiyoba, dan ajiyan zuciya ta sauke. "Fateema kinajina kuwa?" Malam Auwal yamata tambayan da sauri ta dago kai ta kalleshi tace "sorry sa banji mekace ba" dan murmushi yayi yace "hayaniyan dalibai ne yay yawa but gobe idan kinzo ina jiran amsan kinji" da sauri tace "amsan mene malam?" dan shiru yayi yana mata wani kallon daza'a iya kirada naso yace "Fateema, tunda kikabar school I've been looking day and night for a way dazan hadu dake, from the first time dana taba shigowa ajinku a SS1 dan daukan ku further Maths Allah ya jarabceni da sonki Fateema, na yaba da natsuwanki ainun, kinada baiwa daba kowane zai iya sanin hakan ba, burin kowani kamilin namiji shine yasamu mace irinki a matsayin mata ya killaceta a gida a binshi babu mai ganin mai ita, tundaga SS1 nake rainon sonki har zuwa yau saisa kikaga nafi tsananta miki a aji kan kowa, in duka ne kece tafarko kuma alhamdulillah ina alfahari dan kin kasance daya daga cikin dalibai na dasuka fi kowa iya further maths a makarantan nan" tunda yafara ambato kalaman son nan ta saukar da kanta kasa dan wani kunya ma taji yabata aranta tace kagamin mugu yagama cin uban nawa a makaranta ne yanzu kuma yake sona. "Fateema" da sauri tadago kanta ta kallai tareda dan kakalo mai murmushi yace "bakice komiba" rasa mezata ce tayi sotake ta kalli inda Aliyu yake kuma har wani shakkun kallan wajen take zatai magana yadanyi dariya yace "don't worry nagane nagane, bani wayanki kiga nasa number na" rasa yanda zatayi tayi hakan yasa tazamo jakanta daga kafada ahankali ta zage zip din jakar tana kokarin ciro wayar kokadan batason ta bashi number kuma tarasa yanda zatayi, wayar taciro tadago kai ta kallai yanda yasakin mata murmushi yasa tadanyi mai murmushin yake tamikamai wayan ahankali.

Tunda yake baitaba undergoing wat he's going through a tsayen nanba ganin yanda Aneesa takema wani kato murmushi yasa yaji zuciyar shi tamai wani irin masifar daci, internally jikinshi ke rawa ganin tadauko waya ta mikamai yasa taji wani zuciyan dabaita bajin irinshi ba yataso azuciye ya shigo cikin premises din cafe ya dumfaro su.

_*duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafeba, in kinason book dinan ki tuntubeni ta WhatsApp number na kaman haka 07012181461*_
[4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

1️⃣8️⃣ & 1️⃣9️⃣

_how to pay your access fee to IN BETWEEN THE LOVE_

_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting. Zaku iya turo katin 300 MTN for those dabasu da account*_
Chapter 26 · 0% Book details