← Book details A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 71

Sashe 16

A Tsakankanin Soyayya Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Suleja_
Motar datagani Honda pake kofar gidansu yasa taji gabanta yafadi ahankali tafito daga keke napep din taciro kudinshi naira dari tamikamai karban kudinshi yayi yaja keken yay gaba, ahankali take daga kafafun ta tana kara kakkabe hijabin dayay butu butu da kasa ta shiga gidan da sallaman ta, ahankali tana kallon tsakar gidansu da aka shimfida babban tabarma wasu maza magidanta guda biyu zaune kan tabarman duk sun kafeta da ido saikuma Ammi datagani zaune kan yar kujeran tsakar gidan abakin kofar dakinsu idanunta sundanyi ja sosai kaman wacce taci kuka tagodema Allah, ganin yanda Aneesan ta tsaya chak ita bata gaidasuba ita bata karaso cikin gidaba yasa Ammi tace "bazaki shigo ki gaida Baffofin kiba kin tsayawa mutane aka kina kallon mu kaman kinga dodanni" dan murmushi tayi akunyace dan yanda taga idanun Ammi yasa ta manta da kowama dake tsakar gida kanta akasa ta shigo har cikin tsakar gidan gaban tabarman su ta tsugunna tana wasa da bakin hijabin ta ahankali tace "ina kwana Baffa, ina kwana Kawu" mutanen duk kamaninsu daya saidai kana ganinsu zaka gane wa da kani ne daya yafi daya manyanta babban cikin ne wanda suke kira da Baffa wanda tunda ya shigo yake kallonta ahankali yadaura hanunshi saman kanta yana kallon fuskanta yace "Fatima, zauna dakyau" yay maganan yana kallon yanda ta tsugunna sabida karta gaji, gyara zama tayi ta zauna kan tabarman inda yake nunamata da kyau tana gyaggyara hijabi ganin ta natsu yasa yace "tuntuni mukazo mahaifiyar ki tacemana kinje kasuwa mun tsaya mugakine kafin mukoma kadunan, ya kike Fatima?" kanta akasa tace "Alhamdulillah Baffa ina lafiya" kunyanshi takeji sosai bana wasaba, murmushi yayi ya gyadamata kai yace "Allah yamiki albarka kinji ko," gyadamai kai tayi tace "Ameen Baffa, nagode" gyadamata kai yayi shima yace "ki kula da kanki kinji, ki tsare mutuncin ki, ga mahaifiyar ki nan kidinga mata biyayya kinji, in sha Allah zan kokarta nadinga zuwa akai akai ina dubaki ko dayake mun riga mun gama wanan maganar da mahaifiyar ki" dayan magidancin ya kalla yace "mikomin wanan jakan Sani" yar babban jakan dake kusa dashi magidancin yadauka yamikamai karban jakan yayi yabude ciki kwalin waya na Tecno pop2 yaciro yamika mata yace "ga wayanan nakawo miki kome kike bukata ki kirani kinfadamin kinji koda bandashi duk randa Allah ya horemin zanyi miki, sanan ga wanan" yasaka hannu a aljihun riganshi yaciro kudi yan dubu daidai har na dubu bakwai ya mikamata, ahankali tasa hannu ta karba yace "naji amfara registration din jamb kije kibiya muga ya Allah zaiyi kafin nan dawani tsayayye yafito mu aurar dake, kije kibiya cikin satinan dan naji ance idan kabiya dawuri ana turaka center a garinku ko Sani?" gyadamai kanin nashi yayi yace "eh hakane Yaya" kallonta yayi yace "masha Allah kije kiyi kinji, gakuma wanan" ya kara mata dubu uku yace "ki ajiye kidinga kashewa ahankali ahankali kinji Fateema, Allah yamika albarka, Allah yamiki albarka, dawata matsalan?" girgizamai kai tayi ahankali tace "babu Baffa, nagode Allah saka da alkahairi, Allah amfana" murmushi yayi sosai yace "bakomi kidena min godiya Fatima ni mahaifinkine so kidenamin godiya kinji, zamu tafi yanzu kome kikeso ki kirani kifadamin ga wayanki nan" ya kalli Sani yace "tashi mutafi Sani" mikewa duk sukayi Sani yasa hannu a aljihu, dubu biyu yaciro yamikama Aneesan yace "ga wanan ki kara kan wanda Yaya yabaki, ki kula da kanki kinji" akunyace ta karba tace "Allah amfana Kawu" wajen Ammi data zauna tana kallon su tayi tace "Ammi kinga abinda su Baffa suka kawomin" murmushi Ammi tace "akashe lafiya, jeki ajiye a daki kizo kirakasu" daki ta shiga Ammi ta dubesu kaman yanda suke kallonta suma tace "angode Alhaji, kuma kuyakuri idan abinda nace yamuku zafi yabata muku rai, Allah ya kiyaye hanya sanan agaida mutanen gida, mungode" tana maganan tabude kofa ta shiga daki, girgiza kai Baffan yayi yadubi Sani yace "muje Sani" sukai zaure, a falo Aneesa tahadu da Ammi tace "Ammi muje rakiyan ganinan na ijiye kayan a dakina" girgiza matakai Ammi tayi tace "yi maza kidawo ni ina nan" tsayawa tayi turus tana kallon Ammi ganin duk tayi wani iri, murmushin yake Ammi tamata tace "yi sauri mana kin tsaya kina kallona suna jiranki awaje" fita daga dakin tayi tai waje duk suna tsaye jikin mota murmushi tamusu takaraso tace "Allah ya kiyaye hanya, Allah yakaiku lafiya Baffa agaida kowa" gyadamata kai sukayi atare sukace Ameen, Baffa yace "wuce kikoma cikin gida, Allah miki albarka" Ameen tace tawuce ciki kaman yanda ya umurceta yayinda suka shige mota Sani ke tuki sukabar anguwan.

Da sauri ta shiga falonsu hijabin jikinta ta zare tawurga kan kofa tai wajen Ammin ta, zama tayi kusada ita tana kallon fuskarta tace "Ammi na menene? Maiya sami idanunki sukai ja? Kuka kikayi? Mesu Baffa suka gayamiki daya bata miki rai har kikai kuka?" tai maganan cikeda damuwa sosai, yatsa Ammi tasa ta dungure mata kai tareda kakalo murmushi tace "wayace miki kuka nayi eh uwar tsegumi? Toba kukanai ba kwaro ya shiganmin ido dazu saisa idanuna sukai ja, tashi ki dauko sabuwar wayar taki kisaka chaji kinga sun kawo wuta" murmushi tayi dudda tasan da abinda Ammi ke boyemata amma saita share taje ta dauko kwalin tazauna kusada ita tana bude wayan daga kwalin wayan tazauna gefen Ammi tana bude kwalin, fuskarta Ammi ta kalla idanunta suka sauka akan gefen bakinta daya kumbura, hannu ta takai ta taba wurin cikeda mamaki tace "maiya sameki anan Aneesa?" dan zaro ido tayi takai hanunta ta taba wurin sai a lokacin taji zafi shiru tayi takasa magana hakan yasa Ammi tace "maiya sameki anan? Fada kikayi a kasuwa? Eh ina magana kinyi shiru" dan matsawa tayi gefe kadan tana turo baki dan tasan bakaramin aikin Ammi ba ta maka mata duka tace "Ammi wata yarinya fa na taimaka" "kika taimaka wani irin taimako eh spider girl?" Ammi tai magamam cikeda tuhuma, shiru tayi tana zazzaro dara daran manyan idanuwanta dan lashe pink lips dinta dataji are so dry tayi tace "Ammi wani nefa keta janta akasa ya barka mata riga shine na shigan mata daga karshe ma yayanta yazo yako rama mata sanan nadawo" gyadakai Ammi tayi tanamata wani irin shegen kallo tace "aahh ba shakka Spider girl" kasa daurewa Aneesan tayi dudda fada Ammi take mata saida tai dariya sabida yanda Ammi tafadi spider girl din, tallabe mata keya Ammi tayi tace "nikike ma dariya inai miki magana" tabe fuska tayi kaman zatai kuka tana kallon Ammin, Ammi tace "wato saisa kika dade kenan ashe ko daman, Aneesa" Ammi ta kirata cikin kakkausar murya tace "banhanaki shiga shara ba shanu ba eh? Aneesa ina gujemiki matsala bakiji, baki fahimta, bakiji, wai yaya zanyi dakene iyye? Maisa bakijin magana na?" kaman zatai kuka tace "yakuri Ammi bazan karaba to" "yimin shiru anan haka kullun kike cewa, Aneesa karkije kajawo mana bala'i wataran, Allah duk randa kika kara Baffan ki zan kira nafadi mai abinda kikeyi dama sunce ban baki tarbiya mai kyau kinga saisuga balaifina bane" kallon Ammi take tunda tafara masifan hakan yasa tace "Ammi haka sukace wai baki bani tarbiya da kyau?" hararanta tayi tace "wuce kije kisaka waya achaji malama kizo kidaura abincin rana" gyadamata kai tayi ta tashi daga kan kujeran tawuce ta saka wayar chaji sanan tafita tsakar gida dan daura abinci awuta.
***

Ahankali yake bude ido shibaimasan lokacin da baccin gajiyan nan yay awon gaba dashiba, agogon dakin ya kalla yaga karfe biyar na yamman harda yan mintuna, tashi yayi ahankali yashiga bathroom alwala yadauro yafito ya shimfida dadduma akasa yay salla, yana idarwa yatashi gaban wardrobe dinshi yaje ya chanza kayan jikinshi zuwa kayan shan iska, wani brown 3quater da white short sleeve t-shirt yasaka daya kamashi tsamtsam, feffesa turare yayi yazura palm dinshi yafito, fita yayi daga part dinshi yay tsakar gida bayan yadau ball dinshi yana bubbugawa a compound dinsu shi kadai dudda he's missing Dad but baiso yaje side dinshi yaga matayenshi a palorshi, buga ball dinshi yake shi kadai cikeda kwanciyan hankali sosai yaji hanun nashi yadena ciwon kana ganinshi kasan he's so happy, horn din mota yaji anayi ba kakkautawa yasa ya daga kai ya kalli Gate dinsu dan yaga waye yacika mai kunne haka da ihun mota, yana wasa da ball a hanunshi soja yabude gate din motar ya shigo ayanda motar tai parking zaka gane ba lafiya, bubbude kofofin motar akayi aka fito Maman su Rauda ne data watsamai wani kallon tsana dawata mata mai bala'in kama da ita saidai tadan fita tsufa itama tafito daga motar takamo Khamis dake cikin motar tafito dashi ga wanan farin fuskan nashi yasha zanen bakin lalle radau idanun shi abude amma sunyi jajir yana sanye da dogon wandon shaddar shi ta dazu da farin singlet ajikinshi, fashewa yayi da dariya sosai ganin yanda fuskar Khamis din yayi looking so damn funny, yanda yake dariya looks so cute and adorable kasan cewanshi mutun that hardly laugh, dafa cikinshi yayi sabida ciwon dayaji yanamai sabida dariyan da yakeyi ahankali yace "dat girl is so naughty look at wat she did to him" yay maganan yana rungume kwallon a ciki yana kallonsu still yana murmushi dauke kai sukayi sukai falon Dady kana ganinsu kasan bala'i kecin cikinsu.

_Sannu Sannu bata hana zuwa, let's take everything daki daki dan nasamu na isar da desired sakona, love you🥰_
[4/5, 8:05 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

1️⃣1️⃣ & 1️⃣2️⃣

_How to subscribe_

_*zaki tura 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watdsapp number na 07012181461. For those da basu da account you can also send MTN card ta watsapp number na saina saki a group din danake posting*_
Chapter 16 · 0% Book details