← Book details Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 36

Sashe 9

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaman minti biyar Mujahid yayi ba alamun fitowar ta. Wani guard dake guri ya tambaya yacemai ta jima da tafiyA. Bai damu ba yaja motarsa yayi gaba, atunaninsa tabi motan friends dinta, office ya wuce abunshi.
Dakyar junaina ta dawo hayyacinta bayan wasu tsuntsaye data ga suna lilo bisa kanta tsabar rad'ad'in marin, nan take tsoron ta yadawo sabo sai sannan ta ankara da tuni sun daure ta da igiyar ajiki wata bishiyar kwakwa dake gurin.
"Welcom back" Salma ta fad'a daga inda take hakinci kan dutse dake gurin, maza biyun na tsaye bayanta rike da hangbag dinta, fuskar ta daure tamau babu annuri.
Kuka sosai Junaina ta fashe dashi, farar fuskar tuni ya sauya launi zuwa ja, ga wata uwar yunwa dake addabarta ko breakfast batai ba tafita skull..
Gyara zama Salam tayi tace "gwara ma kibar kuka, cox i wont spare you, ina da Unfinished business da yayan ki"
Cikin shesheka Junaina tace,
"koma miye kuyi settling tsakanin ku, dan Allah ki barni na tafi gida, ina da exam gobe"
"Okay, lemme c if yayanki zai dau call dina" jakar dake hannu guy ta amsa ta ciro wayarta sannan tahau dailing no din Mujahid.

Yana ganin Call din Salma tsaki yayi, bai dauka ba yacigaba da aikin gabansa, saida ta kira sau kusan hudu ba respond sannan ta kalli Junaina, dariya tayi tace "it seems today isn't your lucky day"
Adan tsoro junai ta ware ido, Salma ta cigaba "nan da 3 hours idan baiyi picking call dinaa ba i won't hesitate blowing your brains out" karashe maganar tayi tanai mata nuni da bindigar.
Junai kam ta gama firgita, kuka sosai take, tashi Salma tayi ta koma mota ta zauna zuciyarta na radadi, tana ji ajikinta sumtin is not right saidai bata san miye ba, ayanxu burin ta kawai ta rama abunda Mujahid yayi mata, kwantar da Sit tayi ta kwanta hade da sanya earpiece kunne tahau sauraran wakar freedom ta Akon.

****

Shuru har karfe hud'u Junaina bata dawo ba, shiga dakin ta Hajiya tayi taga wayam.
"Ikon Allah, har yanxu bata dawo ba" ta fada, nambar junai ta kira taji ta ajiye kan dressing mirror tanai ringing. Daya daga cikin mai aikknsu kande ta kwalawa kira, tana zuwa tace "kikace da mujahid junaina ta bar gida da safe"
"Eh" kande tace.
"shuru dai bata dawo ba, bari na kira mujahid"
Kira nambasa tayi, shikam alokacin ma ya fito masallaci sallah la'asar, office xai koma yaga call din hajiya, dauka yayi tace
"kuna tare da Junaina ?
Cikin rashin fahimta yace
"Yaushe?
Hajiya tace "bata dawo gida ba, tun bayan daka fita da ita"
Bata rai yayi. "nifah dropping dinta kawai nayi a skull...
"Toh kaje ka dauko ta" kaste call din tayi batare data jiran cewar saba.
Guntun tsaki yaja, aransha shi yana fadin yaran biyun nan fitinar su bata karewa, i dont have time for their nonsense" wucewa office yayi.

Ta bangaran Salma kuwa bata kuma trying no din Mujahid ba, haka tayi ta zamanta a mota daga bisani ne ta fito gurin Junai, ganin yadda ta galabaita yasa ta tura Tk cikin gari siyo mata abinci take away da drink, bayan ya dawo ba yadda batayi ta bawa Junaina abincin, fir taki karba taci banda tsine mata data dunga yi tana kuka.
Yammace ta doso, hakalin Salma yafara tashi, tunanin kar dare yayi masu gurin, uwa uban idan mujahid bai dau call dinta ba batasan ya zatayi da Junaina ba, tsoro ne yakamata kar yarinyar mutane ta mutu a hannu ta...wayarta ta kalla ta hau turama Mujahid Text msg.
Kaman bazai duba ba sai kuma yafasa ya bude sakon "pick d damm call before i murder your stupid crying sister".
Gabansa ne ya fadi, hankali tashe ya mike tsaye cikin rawar jiki yafara neman nambar ta, saida tayi ringing sau biyar sannan ta dauka..
Cikin fusata yace "dont tell me dagaske kike
Tsaki taja.
"do you take me as a joke" kusa da Junai ta karasa hade da riko gashin kanta, ihu junai tayi cike da azaban rikon da tai mata, wayar Salma ta dasa mata akunne, muryar Mujahid taji akid'ime yana cewa "Auta ki kwantar da hankalin yanxu zanzo..."..
Maida wayar salma tayi kunnan ta sanna tace "kaji ai da kunnan ka".
Ran sa yagama baci, cikin daga murya yace "What did you want, say your price ?
Harara tayi kaman tana ganinshi, tace
"If you keep yelling at me i wont negotiate, so better calm yourself muyi magana like gentle people".
Kaman ya shaketa yakeji, kwantar da murya yayi.
"Duk abunda kikeso xan maki kuma zan baki ko miye, but plz leave my sister out of this"
Shuru tayi tana tunanin mai takeso gareshi, can ta tuna da abunda ya faru a Qrand Square, k'ala mata satan 50k da yayi saita tatikeshi hamsin sau goma.
Murmushi tayi tace "500k nakeso,
Iya k'uluwa yakai yace "aini ba ubanki bane dazan dauki 500k na baki, su kananan kwari da kike bi miye amfanin su"
Dariya rainin wayo tayi sannan ta bata rai tace "idan banga alert nan da 10 minti ba, forget you i have a sister" dif ta kashe call din.

Hauka ne kadai yarage Mujahid baiba, kaman wani zaki ya hau huci a office din, yasan Salma is a bitch saidai bai taba tsammanin she can stoop so low tayi kidnapping Junaina ba much less tayi demanding makudan kudi haka ba, tsoronsa daya karta gano Gidansu tunda har ta iya sato Junaina, Allah kadai yasan a ina ta gano shi as yayan Junai.
Karar shigowan text msg na account no dinta ne ya katsemai tunani, da sauri yadau ipad dinsa ya shiga yi mata transfer din kudi, amma a zuciyan shi yayi alwashi karbo kudin sa dan kuwa bazai bari taci bulus ba.

Salma naji alert tasa Su Tk suka kunce Junai, dakyar ta iya takawa suka karasa mota ta shiga abun tausayi, kallon su Tk Salma tayi sannan ta zaro 20k ta basu tace "aikkn nan bashi da amfani ku kama sanaa koda wanki da guga ne".
Sukam godiya sukai sosai cike da murna, dama rashin nasha da ci ke sanya su yin wani abun.

Shiga motar Salma tayi taja, Junai na zaune tana sauke numfashi wahala, hawaye take zubarwa, kanta dauke gefe tanai kallon waje.
Kiran Mujahid tayi, da azama ya dauka tace "ka fito tsakiyar cikin gari" katse call din tayi, yakuma kira bata dauka ba, saida ta iso National stadium sannan tayi parking, ta turamai text din inda take, kallon Junai tayi tace "kina iya sauka"
Kaman jira take ta bude motar, zata sauka taji Salma tace "am sorry idan kinji haushi na"..
Da karfi Junai ta rufe kofar batare data tsaya sauraran taba, saidai kalmar idan kinji haushi da Salma tace ya mugun kara bata mata rai, "wana kare xaa ma cin kashi haka yak'i jin haushi, itama dai tasan abunda tayi can never be forgotten or forgive" azuci junai tayi maganar, can gefe ta zauna akasa jiran Mujahid.
Cikin rashin damuwa Salma taja motarta tayi gaba.

Baafi minti 20 ba Mujahid ya iso gurin hankali tashe, da sauri ya sauka ya riko ta suka shiga motan yaja, ba abunda bai tambayi Junai ba fir taki magana har suka iso gida, Nan suka iske Hajiya da Jaafar shima alokacin ya dawo aiki yaga hankalin hajiya tashe, fitowa neman junai zasuyi sukaga motar Mujahid ya shigo..
Kafin ya tsayar da motar Junaina ta bude kofar ta fito, da gudu ta karasa gurun jafar hade da fadawa cikin sa tanai kuka mai tsuma zuciya.
Tambayan miyasa meta jaafar yahau yi, bata iya bashi amsa ba sai kuka, yajata suka shiga ciki.

Mugun kallom Hajiya tama Mujahid dake tsaye bayan ya fito motar, kaman marar gaskia haka ya koma.
Fuskar hajiya ba annuri tace "ina ka kaita, mai kayi mata..".
Shuru yayi baice komai ba, tsoron sa daya kar Junaina tama hajiya Description din Salma, yasan Hajiya dason bin diddigi.
Wayar hannuta Hajiya ta danna hade da kiran Aunty Bilkisu, fitowan ta kenan daga NNPC clinic inda take aiki. Hajiya tace da ita ta biyo ta gida Junai ba lapia.
Hararan Mujahid tayi sannan ta kama hanyar komawa ciki.

Zaunar da ita Jafar yayi kan gadonta yanai kara tambayan ta, jikinta gaba daya rawa yake, cikin muryan tace "wata yar Mafia ce ta saceni, kuma da alamun tana da wani Dirty relationship da yaya kuma fah her face looks familair i just dont know ina na santa"
Riko hannuta yayi yana lallashinta yace "ko Faizan Umma ce.
Kada kai tayi "Aunty faiza is too naive, ba ita bace wannan fah so pretty gata black beauty saidai zuciyan ta ba imani, i was so scared, kiris yarage bata harbe ni da bindiga ba" duk cikin Kuka take maganar, fuskar ta gabadaya ta kumbure.
Hankali jaafar ne yatashi, yau kam sai yayi confronting yayan shi, Hajiya ce ta shigo, ba tambayar da batai ma Junaina ba, taki gaya mata komai, sai cewa tayi b'ata tayi sunje gidan kawarta.

Aunty Bilki na karaso wa ta duba Junai hade da bata pain relief, sai sannan hankalin Hajiya ya kwanta atunanin ta ko wani abu mugun abu Mujahid, dakyar Junai ta iya tashi tayi wanka tayi alwala sannan ta fito tahau jera salloli.
Chapter 9 · 0% Book details