← Book details Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 36

Sashe 26

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dariyar rainin wayo ta saki sannan kuma ta daure fuska tace "do you tink am stupid, if i could recall, kwanakin baya haka kazo kace you liked me, ka bukaci friendship dina nikuma i was dumb nayi accepting, at last miya biyo baya, you wanted killing me, tnkx to Allah nayi surviving but still saida kaso ka kaini prison, gayamin wannan so ne ko kiyyaya or is it part of your egotistical behaviour ?
Hannuta ya riko, yace "nasan baza ki yadda ba, kin tsane ni, but plz find a place in your heart ki yafemin"
Dogon Tsaki Salma taja.
"You're not serious" ta fada hade da kawar da kanta gefen, sam ta kasa fahimtar inda ya dosa.
Gani tayi yayi kneeling down, da sauri ta kalle shi hade da ware idano.
Black shade din fuskar sa yacire yace " ciwon ido zai zama ajalina, i dont tink zan iya kaiwa jibi da irin azabar da nakeji, bazaki bani tym ko kadan ba ?
Tsoro da firgice ne suka kamata ganin yadda idonsa yayi jajir suna zubo ruwa, runtse ido yayi da sauri dan bazai iya barin su bude ba.
Tsugunna wa tayi gabansa,
Cikin rawar Murya tace "yaya miyasa me ka haka?
Kuka ya fashe dashi "i dont know, mayb kuma shower gel dina yayi expire nikuma nayi using yayi affecting dina, koma. dai miye ne ya illatani dayawa coz i cnt see clearly".
Na shiga uku na kasheshi, Salma ta fada aranta, sai yanxu tagane dalilin buguwarsa a bango daxu. Kaman zatayi kuka tace "plz yaya tashi muje asibiti, i cnt see you liked this"
Kai ya girgiza.
"karki damu nariga nayi using wani magani na, kuma banaso Hajiya tasan ina cikin matsala zata iya shiga tashin hankali"
Hannuta ya riko gabaya, "just tell me kin yafemin ko zanji dadi araina"
Sosai yabata Tausayi, wani irin haushin kanta take ji da muguntar da tamai, tace "yaya na yafe maka dukdai ban rikeka araina ba, but plz kadaina cewa xaka mutu, you cnt leave me"
Ajiyar zuciya ya sauke, ya zauna akasa had'e da zaunar da ita yace "kinga no secret between us, nafada mike zuciyata, do you have something to confess ?.
Shuru tayi, gabanta na faduwa, tanason gayamai itace silan komai tana tsoro.
Ji tayi yace taimaka min mu shiga ciki, kinsan yanxu na zama makaho.
Mikewa tayi jiki sanyaye suka fara takawa ciki, sun kusa shiga Palo Salma ta tsaya tace "yaya karsu Hajiya su ganmu tare, miza muce masu ?
Yace "hakane ga wayata ki kira Faiza tazo, tunda na makance bakya so aganmu tare, nasan ita komin rintsi she wil stand by me"
Cire wayar yayi aljihu ya mike mata, kin karba tayi tace "wasa nake fah"
Aranta kuwa tace "wana hauka ya kaini kirama wannan bazawarar"
Ciki suka shiga suka ci saa ba kowa a palon sai junai da hankalinta gabadaya yana kan Tv, ahankali ta taimaka mai suka haura sama.

Masifa Annah tahau yiwa Hajiya adaki, akan yara sun girma har zasu tsofe taki aurar dasu alhalin ga yammata har biyu a gida, Hakuri Hajiya tahau bata tace "Annah so nake Mujahid da ita Ummi su shirya kansu sai ayi auran, nafison su tare akan da Jafar, da dukkan alamu kuma suna son juna"
Tasaki Annah taja tace "zancen banxa kenan, ina ruwan wani da shirin su ko boyayyar soyayyar su, ni Ummi tafi kwanta min da Jafar, baki gansu dazun ba gwanin shaawa sun dace sosai, kuma da bakinki kika cemin Marikin Ummi yafi son ta auri Jafar".
"Annah gaskia hakan baiyi daidai ba"
Ware ido Anna tayi tace "toh uwata saiki dakeni ai, kinsan dai na fiki iko da yaran nan tunda ni uwar uban suce".
Hajiya tace "hakane, duk yadda kikayi daidai ne"
Washe baki Annah tayi tace "Dadina dake saurin fahimta, tunda yanzu nazo gidan yaushe zaki tafi Maiduguri yi masu albishir din bayyanar Ummi da kuma batun auran, bana so adau lokaci, gwara ayi buki tunda karfi na ".
Mamaki ne yakama Hajiya, sai kace tace mata zataje Maiduguri, kodayake dama tana da niyyan zuwa.
Tace "sai wani watan na shirya zuwa"
Ware ido Annah tayi, tace "nan da wata daya, lailai salamatu bakya so naga auran nan, tab aikuwa hakan bazai yuyuba gobe zaki tafi Maiduguri, dan kuwa ba zama nazoyi a garin nan ba, Buki ya kawoni, ki shirya gobe ki wuce kafin ki dawo kuma zan nemi Daddyn Ummi mu tsayar da rana"
Hajiya kam bata iya cewa komai ba tsabar takaici, tasan zaman Annah gidan husuma kawai zata hada ta tsangwamawa yaran gidan.
Allah ya kaimu gobe" hajiya ta fada, barin daki tayi ta koma dakinta tahau shirya kaya a akwati.

Daki Salma ta shigar da Mujahid, zama yayi gefe godon yace "i really need some sleep"
Jiki na rawa ta yaye comforter dake gado, kwaciya yayi ta rufa mai comfortee din sannan ta zauna gefe sa tana kallon kyakyawan fuskar sa, idonsa rufe, yana fidda numfashi ahankali.
Ta jima zaune harta lura bacci yayi gaba dashi, da sauri ta mike tsadaf ta shiga bandakin sa, showee gel din tadauka ta fito ahankali ta fice daga dakin, duk akan idonsa, abun da yakeson Tabbatar wa kenan wato itace tamai mugun tar nan, yunkurowa yayi zaune hade da wrugi da pilo, dafe kai yayi yace "what should i do na huce abunda kika min, most annoying part shine ko kuka batayi minba ayadda taga condition dina"
Dogon Tsaki yaja, jin motsi kofa yasashi komawa ya kwanta hade da runtse ido, Salma ce ta shigo ta karaso da sauri ta zauna gefen sa, pilo data gani akasa tadauka ta runguma tanai aika mai kallon mai cike da so da kauna, batasan sanda bakinta ya furta I love you..., shuru tayi saurin yi hade da kama bakinta, Allah yasa bai jita ba tafadi aranta. Tafin hannuta tasa ta rufe fuskan ta.

Bude ido yayi ya kalleta hade da sakin Wani irin shuumin Murmushi wanda dashi kadai yasan maanar sa, lumshe ido yayi cikin jin dadin kamshi jikinta dayake shaka.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: ​Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May jannatul Firdausi be ur final destination.

59

Gidan shuru kowa lafe cikin turak'arsa, zuwan Annah sam bai d'ad'ara suba, ganin kowa ya batsar da ita yasa ta dunga saka da warwara rashin nasiha da zata shukawa yaran gidan.
Ta b'angaran Salam kuwa yuni ranar ita ta funte hajun Mujahid.

Washegari da safe yakama ranar da Hajiya zata tafi Maiduguri, zuge zip din akwatinta tayi sannan ta kalli Salma dake gyara gadon, kiran sunan ta tayi cikin wata murya bai abar tausayi, dubanta Salma tayi had'e da amsawa.
Hajiya tace.
"Mujahid ya tashi daga bacci ?
Kunya ce takama Salma, duk'ar dakai tayi k'asa sanna tace "bangan shi a palo ba, k'ila bai tashi ba"
Nisawa Hajiya tayi, ta karasa kusa gareta had'e da zaunar da ita kan gadon suna fuskan tar juna, tace,
"Salma burina bai wuce na had'aki aure da mujahid ba, dan Allah kiyi hakuri kuyi sorting difference dinku kafin nadawo, nasan kuna san junanku, i just dont know miyasa kuke nunawa juna k'iyayya"
Shuru Salma tayi tana wasa dayan yatsun hannayan ta.
Hajiya tacigaba.
"wani abu daya da mujahid ko yanasan abu hardly yake nunawa, saboda yadda ya d'auki kanshi yafi karfi ko wana abu, amma deep down he really carez, sometimes saiki kiga dan hakkin daya raina yana neman tsone mai ido"
Murmurshi kawai Salma tayi, ganin haka yasa Hajiya tadan ji sanyi aranta, fitowa sukayi Salma biye da akwatin suka shiga dakin Annah, sallama Hajiya tayi mata suka fita haraban gidan. Jafar da Junai tsaye bakin motar suna jiran Hajiyan, da ganinta Junai tahau kukan zata bita, dakyar dai Hajiya ta lallab'ata tayi shuru sannan ta shiga motar, Driver dake zaune ciki yajata suka wuce.
Sabon kuka junai tahau yi ayayinda Jafar sai bata baki yake tana k'ara tunzura da kuka shagwab'a, Salma kam murmushi tayi ta juya ciki ta barsu nan ganin abun nasu bana karewa bane.
Chapter 26 · 0% Book details