← Book details Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 36

Sashe 13

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mubarak ne ke tuka Motan, fuskar Mujahid Murtuke cike da haushi dariyar da abokinsa yake, suna shigowa anguwan ya hangi Motar Salma ta fito daga gidan, can hanyar titin gabansu yaga tayi, tab'o Mubarak yayi yace "kai tsayar da motar gatacan ta fito"
Tsayar da motan Mubarak yayi, Mujahid yahau kokarin bude motar dan fita.
Mubarak yace "yaukam indai taki kulaka, ka shareta kawai for good" ln serious tone yayi maganar.
Shuru Mujahid yayi ya fita daga motan, Keke napep yayi saurin tarewa ya fada ciki hade damai nuni da yabimai bayan motar dake can gabansu.

Tuki take tanai bin wakar "Love will Remember" na Selena Gomez, fuskar ta fayau bata da damuwa, bata ankara ba taga keke napep a gefen ta yanai kokarin over taking dinta, tsaki taja ta kuma baiwa motar ta wuta, ta mugun tsanan ayi overtaking dinta, shikam Muhahid sai yiwa mai napep masifa yake akan yayi sauri ya shiga gabanta, wuta Sosai Salma ke bawa mota ayayinda Keke ke binta da Kero, Ranta ya mugun bacci, kwanar Babban high way tabi taga Mai keke baibar binta ba, afusace ta gangara gefen titin hade kashe motar ta fito afusace cin durun uwar sa, tsayar da Napep din yayi gaban motarta sann ya fita da sauri bayan ya biyasa.
Mutuwar tsaye Salma tayi ganin Mujahid, bata iya taku gaba ba, tayi sauri juyawa bakin motar ta bude murfin, nufota yayi da sauri hade da rike murfi.
Amarairece yace
"Salm plz ki saurarani, we need to talk"
Ko kallan shi batai ba ta dauke kai gefe, fuskarta ta daure tamau.
Hannusa ya daura bisa hannunta dake kan murfin motan, da sauri ta zame nata hade matsawa gefe,
Am sorry" ya kuma fada kaman mai shirin kuka.

Wata civic ce tazo wucewa, har tayi gaba tayo baya, maza uku ne suka fito suka tsaya gaban Salma, dayan su yace "Yammata lafiya kuwa ?
Kaman zatayi kuka tace ba "ba lapia ba, wannan mutumin ke takurani
Mugun kallo suka kaima Mujahid, yace "ba wani matsala kanwatace"
Ware ido Salma tayi tace "nikam bansan shiba, mayb ma dan yankan kai ne"
Tsorata Mazan sukayi, aikuwa suka janye Mujahid suka haushi da Duka.
Da sauri Salm ta fada motan hade da sauke ajiyan zuciya, shegen nacin tsiya ta fada aranta, kunna motar tayi ta maida dubanta baya danyin reverse, abunda tagani yayi mugun girgizata, duka sosai Mazan kema Mujahid kaman an aikosu, shikuwa baya da niyyyan guduwa balle tanka su, jibga kawai suke kaman an aiko su.
"Oh my God" ta fada cike da kidema, bude motan tayi da sauri ta karasa gurin su.
"Dan Allah kuyi hakuri ku bari, yayana ne" kaman zatayi kuka tayi magana.
Tsayar da dukan Mujahid sukayi hade da kai mata mugun kallo, dayan su yace "dama yayanki ne kika b'ata mata lokacin tsayawa dukan shi, toh kinyi kadan wallahi, sai kin biyamu dan ubanki"
Iya kidima Salma takai, dagudu ta koma mota tadau jakarta, 2k kadai ke ciki da sauri ta ciro ta mika masu, basu karba ma suka raina, hakuri ta basu fir sukaki yadda, wayar ta iphone 7 ta mike masu tace "kuyi hakuri da wannan, it worth alot of Money"
Tsaki sukayi, suka juyawa suka fada motan su suka ja.
Hankali tashe Salma ta nufi Mujahid dake kwance yana tarin wahala ga jini ta baki da hanci.
Akidime ta d'ago kansa bisa ciyarta, duk ta gama gigita tama rasa abunyi, rokon shi tahau yi akan ya tashi su bar gurin kafin maza su kuma dawowa, tari sosai yahau yi kaman wanda zai shid'e, mikewa tayi ta taimaka ya tashi sannan suka karasa motar ta, baya ta bude ta shigar dashin sannan ta fada gaba taja motar.
Tuki take amma gabad'aya hankalinta na kanshi. Murya sanyaye tace "miyasa baka gudu ba, inda sun kashe ka ya kenan ?
Yunkurowa Mujahid yayi hade da sakin dan kara, hannu yasa ya shafi gefen bakinsa dake jini, dakyar yace "i dont care koda sun kashe ni tunda ke kanki ba kaunata kike ba, gwara na mutu ki daina gani na"
Nisawa tayi tace "ko bana kaunar ka altleast kana da parent, siblings da friends da suke kaunar ka"
Tari ya kuma yi bai iya cewa komai ba.
Ta cigaba "am begging you, don't ever risk your life because of me"
Ciki ciki yace miyasa kikace haka ?
Share tambayan tayi kaman bata jiba, chemist ta tsaya, ta taimaka suka shiga ciki akamai treating ko ina hade da hadomai da magunguna, sun fito ta tambayashi gidansu dan dropping dinsa, can gidansa dake Louis house ya mata kwatance, bata damu ba taja suka kama hanyar gidan, sosai take tausayamai.
Sun iso gidan, ta rikoshi suka karasa ciki, tsoro ne yakamata ganin cewa shi daya ke gidan, dakewa kawai tayi ta zaunar dashi kan one Sitter dake gurin sannan ta ajiyemai ledar maganin gefen.
"Mai kake bukata ? Ta tambaye shi
Ruwa yace yakeso dan shan maganin, hanyar kitchen ya nuna mata ta shiga ta dauko bottle wara tare da glass cup, zubawa tayi sannan ta mika mai, hannun sune ya hade tayi sauri sakar mai da cup din, Murmushi yayi yace "ki zauna mana ?
Kai ta girgiza alaman a'a, bai damu ba yahau shan maganin hade da kurban ruwa, Salma kam kuramai ido tayi tana kallon kyakyawan fuskar shi, dukda some part sun kumbura bai hana kyansa fitowa ba, murmushi ta saki adaidai tym din daya kalleta suka hada ido, daburcewa tayi tahau fadin "xan shiga kitchen wanke hannu" da sauri ta juya ta fada kitchen hade da sauke ajiyar zuciya, saida tayi mintuna Uku sannan ta dawo palom, nanta iske shi yana kokarin mikewa tsaye, ganinta yasashi komawa ya zauna yace "na dauka ko bacci kike ai ?
Kaman marar gaskia tace "a'a ni tafiya ma xanyi" kanta na kallon hanyar fita tayi magana..
Yace "inda na mutu ya zakiyi ?
Sai sannan ta kalle shi, tace "ya zanyi kuwa ? Life goes on"
Kallonta yake saidai this tym around bai fahimci komai game da ita ba, yace,
"Amma miyasa kika taimake ni ?"
Tabe baki tayi tace "friends don't abandon friends".
Lumshe ido yayi yace
"Thank you"
You're welcome" ta fada, juyawa tayi takama hanya fita, bakin kofar ta tsaya sannan ta juyo tace "Get well soon" bata jira abunda zaice ba ta fice.

Mikewa Mujahid yayi da axama ya tsaya bakin window kallonta, saida yaga ta shiga mota taja sannan ya ciro wayarsa dake aljihu ya kira wata namba, bugu daya aka dauka.
Cikin masifar yace " wato kasheni kukai niyyan yi ko ?.
Daga can mutumin daya dauka yace "Oga kayi hakuri, amma ai kai ce muyi making komai ya zama real, thanks goodness yarinyar tayi intervening da wuri.
Dogon tsaki Mujahid yayi ya katse call din.

Typing din yau sai ahankali wlh, kuyi sorry banyi editing ba....

*#ZSAW*☄
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkar

*This page is Dedicated to my Cousin Sisto, Maryam abubakar Lamin (Maryeama Dasoorh), Love you so much, May Allah guide n shower you his blessings*

37 - 40

Bayan Kwana biyu da aukuwan lamarin sannan Mujahid ya fara fita office. Bai kuma bi takan Salma ba. Da azahar bayan ya fito sallah Masallacin su na office ya hadu da Salim tsaye yana waya, cike da farin ciki yake wayan, da alamun kuma da mace yake, Mugun Kallo Mujahid ya watsa mai sannan ya wuce zuwa office dinsa, zama yayi yana tunanin kardai da Salma yake waya, haushi ne sosai ya turnuke shi, Wayarsa ya fiddo ya lalubo lambar salma, son kiranta yake amma baisan abunda zaice ba asalima tun ranar yake saurara kiranta kodan tamai ya jiki, amma shiru. Dabaran Turo mata text msg yayi.
Salma zaune a kan kujerun dake ajiye gefen faculty dinsu tare dasu shehu da wasu yan ajin su suna tattaunawa game da wani course da zasu shiga test, wayarta ke kunnata tana waya da Salim, murya kasa kasa hade da dariya, katse wayan tayi, shehu yace "wannan dariya fah ?.
Tabe baki tayi, tace "yayana ne, lallab'ashi nake yakai min motata gyara ban iya jure shiga taxi"
Yace "kai yaune fah kawai kikazo da taxi, Yayan nan naki kodai dashi zaai ?
Wani mugun kallo takaiwa Shehu, ba shiri yayi azaman kama kanshi, lumshe Ido Salma tayi hade da kallon wayarta wanda tun ranar take tunanin zai kirata amma shuru, tanason sanin ya yanayin jikinsa yake, taso zuwa office din Faiza tambayar ta, saidai ta fasa gudun kar girma ya fadi kasa wanwas.. Karar shigowan sakone ne ya katse mata hanzari, tayi azaman budewa ganin Mujahid.
"Hi, kwana biyu, dafatan kin isa gida Lapia ?
Murmushi ta saki, aranta tace "sai yau ya tuna dani"
Reply ta rubuta mai, "ya jikin ka, kashe maganin?
Dadine sosai ya kamashi, baiyi expecting tamai reply da wuri haka ba.
"Am okay, when are you less busy nazo na maki special godiya for saving my life..
Gabanta ne yafadi, itakam bataso su kuma haduwa da daddare dan kuwa tsoron shi take, saidai kuma tana son ganin kyakyawan fuskan sa, tunani ta hauyi can dai tasamo mafita ta turo mai "ina skull yanxu, zamuyi cA test, kana iya zuwa kasame ni by 4pm"
Yana gani murmushi yayi, Mikewa sukayi suka tafi Hall kasancewar lokacin test din yayi.
Chapter 13 · 0% Book details