← Book details Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 36

Sashe 18

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mamaki ne yakama Salma alamun da wayarta ya nuna mata nambarta is rejected, zama tayi tana tunanin lapia kuwa, bata saduda ba daddare tahau kokarin kirasan still abu daya yake nuna mata, hankalinta ne ya tashi, duk atunaninta ko wani mugun abune ya faru dashi. Kasa runtsawa tayi har garin Allah ya waye, da safe shiryawa tayi ta shiga motarta taja zuwa office dinsa, tana isa daga main entrance gate din wasu polisawa suka hanata shiga, mamaki ne yakamata dan kuwa sun santa duk zuwanta barinta suke, rokon su tahau yi da magiya, fir suka hanata shiga karshe ma ce mata sukai Ogan su yace karsu barta ta shigo.
Jiki sabule ta koma gida, kwata kwata batama san miya faru hakan ke faruwa ba, batai kasa a gwiwwaba saida tayi kwana uku tana zuwa basa barinta ta shiga, hankalinta sosai ya tashi, a kwana na hud'un ne ta kuma komawa, tana cikin rokonsu Mujahid ya iso gurin cikin motarsa zai shiga, ajiyar zuciya ta sauke ta nufesa da sauri, saidai mi, ko kallanta bai yiba yakara baiwa motan wuta ya shige ciki yabarta nan tsaye cikin tsananin tashin hankali marar mitsaltuwa, nan take zuciyar ta ya fadi mata somthing is not right, kai komo tahau yi agurin tana tunanin. Horn taji bayanta da azama ta juwa, tagane shi, Mubarak ne da take gani office din mujahid, karasa gurinsa tayi hade da gaidashi, yace "mai kikeyi anan, ki shiga mana".
Kai ta girgiza, tace "Mujahid ya basu order karsu bari na shiga, dan Allah ka taimaka ni, i need to talk to him".
Tausayi sosai tabashi, saidai yasan Mujahid da kafiya koda ya shigar da Salma bazai yadda ta shigar mai office ba tunda har yasa doka a entrance kar abari tashigo, ko miya hadusu kuma, duk axuci yake zancen.
Yace "why not ki hakura da ganinshi ki tafi gida, i dont tink zai kulaki"
Kaman zatayi kuka ta marairace fuska tace "dan Allah ka tamakeni, yaki kulani for d past 4 dayx, i need to talk to him, inason sanin miyasa yake ignoring dina all of a sudden"
Shuru Mubarak yayi yana naiman mafitan yadda hakan zai yuyu, ajiyar zuciya ya sauke yace "kinga abu daya zan iya maki, ki fadi inda kikeso ku hadu, ni kuma na maki alkwarin kawo maki Mujahid"
Nisawa Salma ayi, taji dadin abunda yace, hakan kadai zaisa ta hadu da Mujahid harya saurareta.
Risinawa tayi tace "nagode sosai"
Dariya yayi
"Baki fadi inda zan kawo miki shi ba"
Murmushi tayi tana tunanin peaceful gurin da yakamata su hadu, can ta tuna da plantation garden na Daddy, gurin nada matikar girma, kyau da shaawa uwa uba akwai flawowi da mayan bishiyoyi gwanin shawaa.
Tace "kasan A & M gardens na hanyar Dikkoh ?
Yace "uhhm nasan gurin, can kike so ku hadu".
Cike da farin ciki tace eh, dariya yayi yace ba matsala gobe by 4.30 zaki ganmu"
Godiya sosai tamai sannan ya wuce, motarta taja ta wuce Garden din.
Tana isa Baba nayaro ta iske, mai kula da shuke shuke gurin, gaidashi tayi aladabce ya amsa cike da fara'a, suna shiri sosai da Salma kasancewar yawanci idan damuwa tayi mata yawa gurin take zuwa shan iska.
Gurin da pink da yellow flowers suka fi yawa nan Salma tacemai ya gyara gurin yayi kyau dan tana da bako, so take idan yazo duk wata bakin cikin sa ya yaye, shikam Baba nayaro dariya sosai tabashi yahau zolayan ta yayi sirki.... Sun dan jima suna magana daga bisani Salma tamai sallama ta koma gida..
Salim ta tadda ya fito daga motar sa, da alamun shigowar sa gidan kenan, "Salma daga ina kike da yamma haka ? Ya fada cikin salon kulawa kaman gaske, deep down kuma so yake yasan ina taje dan kwana biyu baya ganin ta a office din Mujahid.
Ganin yadda yake mata kirki kwana biu yasa ta saki fuska tace "ya salim Ogan ka naban Tough tym, kwata kwata nakasa gane kanshi, yanxu baya kulani"
Murmushi yayi wanda shi kadai yasan maanar sa yace "kin manta The boss is always d boss, fadin Sakon ki saina kaimai".
Tabe baki tayi "no need gobe zamu hadu a Garden din Daddy by 4pm suprised visit zamu ma juna.."
Ware ido yayi in shocked, "yasan Garden dinne ?
Dariya tayi, tayi gaba tana fadin "a'a, gobe zai sani" tafiyar ta tayi..
Tsaye Salim yayi zuciyar shi na kuna, aranshi yace "muje zuwa, mahaukaci yahau kura", naushin iska yayi ya wuce part dinsa.

*****
Washe Gari.

*Kaduna*..

Jaafar ne tsaye bakin motar sa bayan su kammala shari'a da sukai tayi kusan kwanakin da suka shud'e a Supreme court. Bude motar yayi ya ajiye tilan takardu dake hannunsa sannan ya shiga motar, yaja komawa Birnin tarayya (Abuja).

*Abuja*

Tun Safe Salma ta birkice kayanta gabayada tanai neman wanda ya dace tasa, karshe dai white jean da pink top ta ajiye gefe sannan tadau Hoton Mujahid wanda tuni ta wulla a trash can kwanakin baya saidai daga baya tacire ta adana shi, daukon hoton tayi tana kalla hade da lumshe ido, daga bisani ta bude pink cluth bag dinta ta ajiye frame din ciki, wanka tayi ta fito ta sannan ta zauna jiran karfe hudu ta cika.

K'asa Zaune Salim yayi a office, duk mintina kallon agogo yake, yana fitowa sallah azahar, joint dinsu na yan shaye shaye yaje, saida yayi tatul sannan yahau kuka yana tunanin yadda zai raba Salma da Mujahid, rasa mafita yayi daga karshe ya yanke shawaran zuwa Garden din Kidnapping dinta kafin su hadu da Mujahid.
Karfe uku da rabi nayi Motar sa ya shiga yaja yanai wani reckless driving har ya isa Garden din, black Face mask daya siya na musamman yadau ya sanyawa fuskar sa sannan ya shiga Garden din cikin sadaf ya boye cikin wata bishiya.
Katon Scissors ne Hannu Baba Nayaro, sai gyaran wasu flowers yake cikin sauri yana duba lokaci kar Salma ta iso ta iske bai gamaba, aiki yake sosai yaji alamun saukar Numfashi daga ina yake, dakatar da aikin yayi yafara takowa gurin yana fadin "waye anan...?
Tsoro ne ya kama Salim, da sauri ya fito yakama wuyan Baba nayaro, yace "sshh kamin shuru karka kuskara kayi ihu"
Kokarin kwace kansa Baba nayaro yahau yi, yakasa, iya karfinsa ya take kafar Salim, da sauri Salim ya sakarmai wuya, Guduwa Baba nayaro zaiyi Salim yayi saurin rikosa hade da kwashe tsoho da mari, nan take fada ya kicibe tsakanin su, sukahau dambe, duka sosai Salim yama baba nayaro, ganin yana kokarin guduwa yasa ya dauki scissors din zuciya daya ya caka mai atsakiya cikinsa, ihu Baba yayi ya fadi kasa bakinsa na ambato kalmar shahada, tsoro da firgice ne yakama Salim ganin yadda jinin Baba ke bulbula, hankali tashe ya cire mask din fuskarsa yahau yiwa Baba sannu, nunasa Baba yayi da yatsa yace dama kaina....,
Tsorata Salim ya kuma yi da sauri ya ruga da gudu yabar gurin cike da tsananin fargaba.

Fuska dauke da seriousness Mubarak ya iske Mujahid, yace "Mjay tashi muje na nunama wani abu"
Dubasan Mujahid yayi kaman bazai kulasaba ganin yadda yaci serious first tym in his life yasa shi cewa "miya faru ?
Mubarak yace "it urgent, plz tashi muje banaso ka cikani da tambaya"
Kaman bazai tashi ba, daga baya kuma ya mike bayan Mubarak ya fice a office, "this is not good" Mujahid yafada aransa, atunanin sa ko batun wani crime ne Mubarak yakeso suje sugani, drawer na table din ya janyo yadau bindigar sa da Handcuffs yasa a ajihunun sannan ya fita, gurin mota ya iske Mubarak, shiga sukayi Mubarak yaja motar.

Hudu na cika Salma ta kammale shirin ta, jakarta da hoton ke ciki ta dauka sannan ta fita palo, dakin Mom ta nufa da sauri tai mata sallama akan zataje shopping sannan ta fito, bata dau motar taba acewarta kar Mujahid yagani bakin garden din yafasa karaso wa ciki, Fita waje tayi ta Tari Taxi ya kaita Garden din.

Tana shiga Garden din wani irin fresh air taji da farin ciki, fatan ta Allah yasa Mujahid yace yana sonta da sai tafi ko wace farin ciki.
Taku daya biyu zuwa uku tayi tafara ganin d'ison jini, bin jini tayi har inda Baba nayaro ke kwance, cike da tashin hankali ta tsugunna gaban sa takiran sunansa, jini sosai ke zuba saman cikinsa, hannu ta tasa ta tari jinin tana ambatan innalillahi wa inna'ilaihi rajun, jijji gashi tahau yi ko motsi baya yi, tuni hannuta da farin wandonta suka kwashi jini, ihu take tana kiran sunan baba.

Parking Mubarak yayi, kallan sa Mujahid yayi yace "wai miye zan gani anan ne, nifa ban ciki da wasan ka na banza.."
"Fito muje" Mubarak ya fadi, fito wa sukayi suka shiga Garden din, suna tafiya Mujahid yaji ihu, kallon Mubarak yayi yace "whats going on ?
Kafin Mubarak yayi magana sukaji wani ihu, atake maza suka rafta da gudu inda ihu ke tasowa.
Chapter 18 · 0% Book details