← Book details Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 36

Sashe 30

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaran Salim Salma ta nufa ta iske shi yashe kasan tsakiyar palo, da ganin baya cikin hayyacin sa, karewa ko ina kallo tayi komai kaca kaca, ga uban emty bottles na barasa, gabadaya ya gama muzanta. Ranta ne ya baci ta tsugunna gabansa inda yake kwance, afusace tahau kiran sunan sa, bude idanuwasan da suka sauya launi zuja yayi ya sauke su akanta, adan zabure ya mike zaune atunanin sa ko imagination dayasaba yine.
Fuska daure tace "Ya Salim miye haka, why are you trying to useless your life ?
Sauri riko hannuta yayi tabi gemai hannun da karfin gaske tana hararar sa, murya raunane yace "Salma yazanyi da sonki, duk yadda kika ganni da kuma duk abunda nake Sonki ne Sanadi (littafin Jiddah Aliyu) na rasa ya zanyi da rayuwa ta" kuka ne ya kufce masa hade da sauri rungumarta, Haushi ne ya turnuketa ta turesa daga jikinta ta mike tsaye tanai mai mugun kallo tace "ya salim kabar bata lokacin ka akaina, cox i dont love you, tayama xaai na soka jibeka so useless and irresponsible, the only gentleman i love is your Boss, get that in your dummy brain" ahasale ta karasa maganar, shikam kuka yaci gaba, tsaki taja tahau gyara ko ina na gurin sannan ta fita ta barshi cike da tausayin so maso wani dayake mata.

*****
Washe gari ne Hajiya ta dawo gida da yan'uwa birjit na fara shirin buki. Annah kam baki har kunne zata aurar da jikoki, sunyi magana dasu Daddy an tsayar da rana one week kacal.

Su Junaina kam sai sabon iyayi daya karu an kusa shiga daga ciki, sosai take jin dadin yadda Jafar yake nuna mata so da kulawa, itama baa barta baya ba dama gashi ta iya shishigi da ladabi a soyayyan shiyasa sukafi dacewa da juna.
Su Oga Mujahid da Salma baa magana soyayyan sosai suke ba kama hannu yaro, wataran har Mamaki Hajiya take da irin son da Mujahid yakema Salma dan kuwa bata zata ba..

Daddy ne ya amshe zamewa Salma da Junai Uba game da komai na auren, kafin satin auran sukaje Dubai yin siyayyan abubuwan amfani masu shegu tsada sannan suka dawo.

Satin Buki.

Gidan su Momy ya cika sosai da jamaa, yan'uwanta ma sunyi kara sunzo saboda son datake ma Salma, wasu yan'uwan Salma na dangin uwa duk can suka sauka, masu gyaran jiki irin irin kusan goma Hajiya ta aiko suke gyara Salma anan gidan, Junai ma acan gidansu gyara sosai ake mata, saidai har yanxu ba wani shiri suke da Salma ba.. Event ma da suka hade kin Amincewa Junai tayi suyi tare cewa tayi kowa yayi nasa daban a inda yakeso, hakan Sosai yabawa Hajiya haushi sharewa kawai tayi ta barta ahanka, mazan ma baa barsu baya ba sai nasu shirin suke.

Three Dayx to Daurin aure, kuma gobe ne zaai event din Arabian night.
Su salma ansha murja dakayan Dilka da turaran kamshi, duk inda ta ratsa shining take da kamshi, tayi kyau sosai, kayan tsumuwa na mata (Aunty Guarantee) ba wanda baa bata tasha ba, na cushe cushe ne fir taki amincewa dasu dan bata yadda dasu ba majority ma ovary cancer suke sanyawa.

Around 8 na dare ta fito wanka sai kyalli skin dinta yake, zama tayi gaban mirror ta murje jikinta da turaruka masu dama sannan ta sanya night wear riga da wando cotton ta kwanta, agogon mujahid dake kan side drawer tadau tana shakar kamshinsa sannan ta makala a hannuta. kaman jira take taji wayarta na ringing, da azama tadau ka ganin wanda ke kira.
Daga can bangaran yace "Angel am dieing" cikin wata irin salo mai rikitarwa yayi maganar.
Adan rude ta mike zaune "My love you're killing me, plz talk to me, miyasa meka ?
Lumshe ido yayi "am sick, cronic ciwon kai ke damuna"..
"OmG" ta fada adan kidime, ta mike tsaye.
Tace "yaya kana ina
Murya wahale Yace "ina gida, apart din Baki".
Ajiyar zuciya ta sauke tace "yaya plz stay calm, i cnt sleep idan banzo naga condition dinka ba, am coming right away" katse wayan tayi da sauri ta suri Hijab dinta tadau mukullin mota ta fita dakin, mutane sosai tagani palo anata hira, ta kitchen tabi ta fita waje batare da kowa yaganta ba. Mota ta shiga taja tabar gidan at 360.

Dariya sosai Mujahid yayi bayan sun gama wayan, zaune yake shida wasu cousin dinsa guda biyu a palon bak'i, duk wayar da yayi da Salma a speaker yasan ya suka ji komai.
Dayan mai suna Khaleel yace "Mjay kaci saa yarinyar nan na bala'in sonka, jifa yadda ta rud'e, dama nice nasamu Babe haka" dariya sosai yake yana maganar.
Murmushi Mujahid yayi yace "nima ina bala'in sonta, i cnt live without her, she is my everything but some scores have to be settle, Salma ta mugun wahalar dani ba kadan ba"
Harara Dayan mai Suna Abdul yamai yace "miye amfanin settling scores tunda nan da 3 dayx she is all yours, koma dai miye ka barta kawai"
Mujahid yace "aiko mi nayi mata bazata ji haushi na ba, she is madly inlove with me"
Dariya Khaleel yace "babaa wai wana irin wahala kake nufi tabaka?
Mikewa Mujahid yayi yace ina zuwa" fita yayi can bakin gate yayi magana da mai gadi sannan kuma ya dawo palon ya zauna. Labarin tun farkon haduwan su da Salma yafara basu, jifa jifa kuma yakan kalli wayarsa.

Salma na isowa Gidan wani mugun Horn tahau yi, da sauri mai gadi ya bude mata ta cilla motar ciki da sauri tayi parking ta fito... Sauri sauri, gudu gudu tayi tafara karasawa part din Baki dake can nesa da main house, takusa daf da gurin taji ana kyalkyalewa da dariya, tsoro ne yakamata tafara takawa da sauri, daidai bakin Kofar taji Muryar Mujahid na magana cikin dariya, gabanta ne ya fadi ta daskare gurin ba tare data iya kwakwaran motsi ba.

Cikin dariya Mujahid yace "kasan most funniest part of the story, bayan munyi plan da abokina nayi kissing dinta still bata bada kai ba, saida nayi fooling dinta na aika wasu Maza sukamin Duka atiti sannan fah ta waiwayeni"
Khaleel yace "gaskia kayi fooling dinta dayawa, ni yaushe zan yadda nasha duka abanza"
Mujahid yace "bayan ta fara kulani i had to pretend loving her duk dan na shuka mata rashin mutunci, kuma nasan itace same Ummi da Hajiya ta isheni saina nemo, niku kuwa na share naki nunawa Hajiya nasan wata Ummi. The next tin kawai naganta a gidan nan, kasan kuma miya faru ?
Haushi ne yakama Abdul, Khaleel kam dama player ne, kuma dadin labarin yake ji yace "what next ?
Mujahid yace "Could you imagine, yarinyar nan tasamin attarugu a shower gel dina, nikuma arashin sani nayi using, ranar ko i felt like strangling her to death"
Dariya sosai Khaleel yakeyi, abu sai kace a film, yace "Mjay gaskia ka wahalu, ya kayi kuma?
K'wafa Mujahid yayi yace "ya kuwa nayi, fooling dinta bashi da wuya, tricking dinta nayi into biliving ina sonta, ita kuma tayi saurin bada kai as usual .."
Khaleel yace "amma fa Salma ta hadu, koba laifi zaka huta da jikinta.."

Kaaa cigaba da Sauraro Salma tayi, hannu tasa kan kunnuwan ta tana fadin "innalillahi wa Inna'ilaihi rajun" hawayan Bakin Ciki data jima basu zubo mata ba suka hau ambaliya a fuskar ta, kuka sosai take tafara ja dabaya tayi tuntube tafadi kasa, ihu ta saki cike da tashin hankali.

Jin ihun Salma yasa Mujahid mikewa akidime ya fito waje, ganinta yayi zaune kasa tana rusa kukan daya jima yanason Ganin hawayanta. Da sauri ya karasa gareta yana fadin "Habibty yaushe kika zo ?
Wani sabon kuka tafashe dashi, jin sabon yaudarar dayake shirin yi mata, mikewa tayi tsaye tana kallon yadda duk ya gigice, rikota yayi cike da kulawa, wani irin feeling yaji ya ratsa jikinsa, ga kamshi jikinta sai ratsa mai gabobin jikinsa yake gabadaya.
Murya kasa kasa yace "sweetheart mi aka mike, plz stop crying, your tears are breaking my heart" janyota yayi zai rungumeta tasa hannu da karfi ta turesa baya.
Cikin kuka ta nuna shi da yatsa tace "dont you dare lay your filthy hands on my body, banza macuci, dan iskA, Allah ya isa tsakani na dakai, i hate you..", kuka sosai ya kufce mata, rike kanta tayi dake mugun sara mata lokaci gudu.
Hankalin Mujahid ne yatashi baiyi tunanin Salma zata dau komai da zafi ba ayadda takeson shi.
Matsowa yayi kusa da ita tayi saurin ja baya, kaman zaiyi kuka yace "plz forgive me, i was only joking, nasan kinji komai wlh ina sonki Salma"
Wani mugun tsanan shine taji ya diru azuciyan ta, she has never been humiliated like this in her life, kuka sosai take cike da tausayin kanta, tarasa miyasa Mutane biyu nan Abbanta da Mujahid datafiso arayuwan ta suka fi kowa kuntata mata. Innalilahi kawai take ambata aranta.
Kallon shi tayi tace "ko kana sona ko baka sona i dont give a fucking damm about it, cox ko kaine autan maza na hakura dakai, na gwamma ce na kashe kaina akan na aureka balle na zauna dakai" sautin kukan tane ya karu ta juya da gudu ta koma gurin motar ta, binta yayi shima da gudu yana kiranta, bata saurare sa tashige motar taja ta wuce ta gabansa wanda kiris ya rage bata kwashe saba, bai damu ba yabi motar da gudu amma tuni ta fice daga gate din.
Hannu Mujahid ya daura akai cike da tashin hankali yace "Am died...
Muryan Abdul yaji abayan shi yace "in life you rather learn leason the easy way or the hard way, da dukkan alamun i don't think she will ever accept you back".

Kuka Mujahid yahau yi cike da haushi abunda ya shirya dan rama abunda tamai, gashi komai ya fado kanshi.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: ​​Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}

Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May jannatul Firdausi be ur final destination.

63
Chapter 30 · 0% Book details