← Book details Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 36

Sashe 31

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daran ranar Mujahid bai samu rintsawar arziki ba, ta b'angaran Salma kuwa bata san duniyar da take ciki ba, Salim kam yafi kowa farin ciki ranar, kodaya koma gida kwanciyar sa yayi yana hagon yadda rayuwarsa zata kasance tare da abun kaunar sa.

Washe gari babu wanda ya lura da Salma bata gidan, sai kuwan azahar da Kulchumi mai gyara mata jiki ta shiga dakinta yi mata wanka turare, wayam tagani babu alamun Salma tayi kwanan dakin, bandakin ta leka bata nan ta fice da azama ta fad'i ma Momy rashin ganinta. Ran Momy ne yabaci, shiga d'akin tayi dan tabbatar da zancen kulchumi, mamakine ya kamata gasgata zancen, da sauri tahau kiran nambar salma da wayar dake hannuta, ringing take bamu mai dauka.
Fitowa tayi waje ta hangi motar Salma a parke, mamakone ya kuma kamata toh ina salma ta shiga by this tym, karasawa tayi bakin motar hade da lekawa ciki ta hangi wayar Salma ajiye kan seat, bude motar tayi tadau wayar hade da duba dawa tayi waya last, sunan Mujahid tagani, ranta ne ya kuma b'acci, atunanin ta ko Salma na gidan su Mujahid, afusace ta koma cikin gida, batare da bata lokaci ba ta kira wasu yan'uwanta uku suka shiga mota zuwa gidan Hajiya.

Mujahid kam duk ya figi dare daya, tun yana jiran Salma tadau kiran wayarsa harya saduda ya zubawa wayarsa ido karshe yanke zuwa gidan su yayi Abdul ya hanashi da cewa ba lailai ne ta saurare shi balle yanzu da gidan ke cike ana hidimar buki, kumai ai Salma bata fasa auran saba tunda har yanzu basu ji bayanin komai daga bakin hajiya ba. Da wannan kalaman Mujahid yadan ji sanyi aranshi.

Annah baki har kunne, Jallabiyo yi ne matsu tsada gabanta tana zaban nasawa yau adaran Arabian nights, dakin makil yake da wasu yan jikokonta da yan'uwan ta, sai zolayar ta suke tana masu tsiya, Hajiya ce ta shigo dakin adan birkice taja Annah suka fito haraban gida kasancewar ciki makil yake da bak'i yan buki.
Cike da kidima Momy tace "Annah kinga Salma gidan nan ?
Tsaki Annah taja tace "dalilin katsamin jin dadi kenan.
Mom tace "yanzu momyta ta kirani ta tambaye ni, nace mata bata nan, da alamun kuma ba lafiya ba"
Gaban Annah na yafadi, aranta fadi take "sabon tuggu kuma yaran nan suka kulla dan karna rakashe abukin nan, toh wlh baku isa ba"
Magana zatayi sukaga an bude gate motar su Momy ya shiga da gudu, parking tayi duk suka sauko fuskar su dauke da kunci.
Babu ko gaisuwa Momy ta dubi Hajiya tace "kun mamaki wlh, a tunanin na Salma bata da wata uwa data wuce ni shine zaku rabani da ita sannan kuma kice min ke baki ganta ba, kuma ni nasan tana gidan nan"
Tashin hankali ne ya mamaye Hajiya, nanta hau kokarin fahimtar Momy da kwatakwata ta kasa gamsu wa da kalaman ta, Annah kam binsu tayi da ido tana tunanin indai dagaske Salma guduwa tayi ko sace ta akayi ba lailane ayi buki budiri ba, itakam bazan lamunci a bata mata bojet ba ayadda ta shirya juya mazauni wanga bukin. Kamar an tsikareta ta fashe da kuka hade da daura Hannu akai, duban ta su Momy sukayi adan tsorace.
Cikin kuka Annah tace "Kuyi hakuri duk laifi na na, nice na tura Salma Kano amso min may an in ciwon idona, batayi niyyan zuwa ba saida nace idan bata jeba zan hanata auran Mujahid, ba shiri ta kama hanya batare da bata lokaci ba" kuka sosai Annah ta kara fashewa dashi.
Ran Momy ya gama bacci, kasa magana tayi ta juya tace da yan'uwanta su tafi, yaukam taga matsayin ta gurin Salma da danginta.
Kirata Hajiya tayi ko kallan ta batai ba suka shiga mota yaja. Takaici ne yakamata Hajiya ta dubi Annah da har yanzu kuka take, kasa ce mata uffan tayi ta koma cikin gidan. Dariya Annah tayi tare da debo rawan shoki tana fadin "yo ina dalili kura da daukan kayan kare dashan bugu, ai baima yuyuwa ne dan ita baa ganta ba nasan halin hajiya sarai sai afasa bukin".

Da bacin rai su Momy suka komo Gida, gurin Daddy ta nufa ta tsara mai abunda ke faruwa, shikam baidau komai da zafi ba yace ba komai karta damu aci gabata kudanar da buki, inayaso ranar da Salman ta dawo shi yasan yadda zai nuna mata rashin kyautawar sanar dasu da batayi ba.
Jiki sabule Momy ta amince da hakan, ba yadda ta ita tunda shi daya kawo Salman ma baiji haushi ba.

****
Da daddare aka fara shirin Arabian night, su Mujahid kam suna zaune tare dasu Abdul harda Mubarak ba yazo, hirar su suke basu da damuwa banda Mujahid dayayi sukuku dashi, yasan ko karan hauka ne ya cize Salma bazata fito arabian nights ba, wayarta ya kuma latsawa kira tana ringing ba'a dauka ba, babban matsalan shi ma yarasa wa zai tunkara da maganar dan yasan duk wanda yaji maganar a iyayen saidai kuwa afasa auran..wata zuciyar tace miye zaka damu tunda kaji shuru kila ta hakura ayi auran, murmushi yayi zuciyar sa nagasgata masa hakan.

Arabian nyt kam yayi shagali da maana, su Junaina da Jafar ansha kyau, jamaa sai tambayan Salma suke ba kunya Annah ke dankaro karya, hajiya kam ba wata walwala tattare da ita, sam bataji dadin Abunda Annah tayi ba, ganin Mujahid bai tunkareta da zancen ba yasa bata cemai komai ba, shikam gogan baisan da wata tafiyar Salma Kano ba.

****
Bayan Kwana Biu.

Tun Ranar da Salim yakai Salma Gidan bai kara komawa ba gudun kar a zargeshi, saidai yadda yaga anata cigaba da hidimar buki yasa shi mamaki, dabara yayi ya kira momy yace zai karbi mukulli mota a hannun Salma, ita kam bata kawo komai aranta ba tacemai Salma na Kano.
Dadi yaji yafara kiciniyar hada mata passport dan guduwa da ita Ghana.

Tsoron Allah ne yakama Annah bayan an gama shagalgulan Buki, daurin aure ne kadai ya rage daza ai gobe, kullum tambayar ta ake ya labarin salma saidai tace mai magani bai gama hada magani ba, Hajiya kam taso tagano Annah karya take saidai rashin damuwan mujahid yasa tayi tunanin bakin su daya, da Yamma Annah ta fita zuwa bangaran dasu Mujahid suke, gabanta sa faduwa yake tana tsoron rashin Mutuncin zai mata, ta window ta hango su zaune da abokai suna ta hirar su tare dashi kaman babu abunda yafaru, tace "kai Mujahid fito muyi magana"
Dafe kai yayi cike da takaicin mai matan nan takeso, fitowa yayi yanai aika mata mugun kallo.
Kamar munafuka ta sinne kai tace "dama batun Salma ne, baa ganta ba nace nina aiketa kano dan kar acinye min shagali, yanzu kuma naga buduri ya k'are yasa na gayama"
Agigice yake kallon ta dan kuwa bai gane inda zancen ta ya dosa ba, "wana kano taje, bata gida ne? Ya jaho mata tambayoyin.
Tsurewa tayi tace "bansani ba, kaje ka nemo ta"
Zare ido yayi in shock yace "Annah ina take ?.
Kara tsurewa tayi tace bansani ba, bata jira cewar saba ta rugu gida da gudun dani kaina bansan yar tsohuwa ta iya ba.
Innalillahi Mujahid ke ambata, bai koma palon ba ya rugu gurin motar sa yabude ya shiga, mukullin na jiki ya kunna yaja yabar gidan.

Salma bata farka ba sai washegarin daya kaita da daddare, juyi tayi taji ta tim tafado kasan, arazane ta bude ido, wani mugun ciwon kai ke dawainiya da ita, dakyar ta mike tsaye tana karewa dakin kallo, kasa gane dakin tayi ta dafe hannu jikin bango ta fito palon, tsoro ne yakamata bata gane komai na gidan ba, wani mugun jiri taji ta fadi kasa sai bacci.
Saida tayi kusan 4 hours a gurin sannan ta kuma farkawa, so take ta tuna wasu abu amma takasa, data fara kokarin tunanin saita yanki jiki ta fadi sai bacci.
The next day ne ta kuma farkawa, da sauri ta mike koma toilet din dakin, ruwa ta kunna tasha sannan ta kirkiro wa kanta amai, saida tayi amai sosai sannan ta dawo hayyacin ta abubuwa suka dawo mata, ya Salim ta fara ayyanawa aranta, wana mugun magani ne haka yabata daga ciwon kai, ita bataji saukin ciwo ba sai hallaka da magani yasoyi, tasan kuma shi kawo ta gidan, ranta ne ta baci ta mike wani jiri ya kuma dibarta, saurin dafe bango tayi, ga wata uwar yunwa nacinta, adaddafe ta fito kofar palo taji kofar a rufe kasa jure tsayuwa tayi ta rarrafa zuwa kitchen, komai na abinci akwai, tea na ruwan sanyi kadai ta iya hadawa tasha ta kuma rararfa zuwa dakin.
Sai sannan tahau neman wayarta ta tuna a mota ta barta, kwaciya tayi akasa tana tuna Betrayal din Mujahid bata sanda kuka ya kufce mata ba, agogon shi dake hannuta ta duba taga karfe biyar na yamma. Mikewa tayi ta koma toilet, dakyar ta iya watsa ruwa tayo alwala tamai da night wear din jikinta da hijab dinta tahau rama sallolin dabata yiba. Bayan ta ida ne kuma wani mugun baccin ya kuma sace ta.
Chapter 31 · 0% Book details