← Book details Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 36

Sashe 15

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddyn Salma ne tare da Ja'afar a office dinsa. ja'afar yana daya daga cikin lauyoyi da Alhaji Abbas ya aminta saboda tsananin rike gaskia da Tsoron Allah da yake azuciyarsa, sau tari yawan idan zaiyi harkar canji da dollars ko euro yafi yadda da damk'awa jaafar takardun shaidan komai dan yasan bazai cucu saba.
Zaune suka suna magana akan wani fili daya siya a Kaduna, copy na takardu shaida da komai ya mikewa Jaafar, karba yayi yana dubansu
Daddy yace "ka adana su da sauran"
Hade takardun jaafar yayi cikin briefcase nasa sannan ya mike da niyan yimai sallama, dakatar dashi Daddy yayi hade da cewa "ya maganar mu ta kwanaki, naji shuru baka kara waiwayar zancen ba.."
Zama jaafar yayi had'e da kirkiro murmushi dole, shikam yama manta da zancen, shuru yayi yana tunanin zancen da neman amsar bawa Daddy, bazai yaudari zuciyan saba dan kuwa yana son Junaina, saidai kuma ba damuwa tayi dashi ba ga kuma Daddy da yakeson ya hada shi da Diyar shi dako sanin ta bai yiba balle ma yasota, shi kuma auran bayama cikin lissafinsa yanzu kokarin Nemo Ummi kawai yake dan farin cikin hajiyarsu kuma baima isa ya tunkareta da sunan yana son aure ba, ana takai wa yake ta kaya.
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhaji wani hazari ba gudu ba, maizai hana mu hadu da diyar taka, idan ta amicin dani saina yadda karya zamana ko tana da wanda takeso"
Farin ciki sosai ya lulube Daddy, kasancewar ta bangaran Salma ba matsala koda batason Jaafar yasan zata mai biyayyah, kuma ma baiyi tunanin Salma nada wani da takeso ba.
yace "ba matsala, gobe kazo gidana mu kara tattaunawa saika ganta
Yake jaafar yayi aranshi yace "Allah yasa karta aminci, afili yace "saidai yau nazo, saboda gobe da safe ina da aiki a Kaduna"
"ba damuwa, Allah ya kaimu zuwa dare" acewar Daddy.
Godiya yama Daddy sannan sukai sallama ya fice azama.

Tun ranar da Hajiya ta kira Mujahid tace yazo gida bai samu daman zuwa ba sai rana ta yau acewarsa aiki yamai yawa bacin kuma da gangan yaki zuwa.
Fuska ba yabo ba fallasa Hajiya ta tarbeshi, nan tahau mai fadan barin sa gida akan abunda baikai ya kawo ba, Mujahid kam shuru yayi yana sauraran ta dan ya kagara ta gama ya wuce aikinsa, tace "Bani hotunan Ummi dana baka kwanakin baya"
Sosa keya yayi alamun marar gaskia yace "mi zaai dasu, an ganta ne ?
Hajiya tace " baa ganta ba, kawai hoton zaka bani tunda ba nemo ta zakayi ba, tuni Jaafar ya dukufa da nemo ta kuma am sure zai samota aduk inda take"
Ware ido Mujahid yayi adan kidime yace "jaafar zaki bawa hoton ?
Mugun kallo takai mai, tace "ko babu hoto Jaafar yasan fuskan ta, kaida ba saninta kayiba yasa na baka hoton"
Gabansa ne ya fadi, fatan shi Allah yasa kar Jaafar ya hadu da Salma, nisawa yayi yace "Hajiya basai jaafar ya nemo taba, nida kaina zan kawota gidan nan very soon."
"Ka ganta ne" Acewar ta.
Kai ya girgiza alamun a'a, aranshi yace "ki bani time very soon zaki ganta amma saina koya mata hankali yadda idan ta shigo gidannan bazata yadda ki had'ata aure da niba".
Tashi yayi ya mata sallman zai wuce office ya fice waje, nan suka hadu da Junaina ta dawo daga gidan wata kawarta dan tuni sun gama Neco.
"Yaya kyan tafiya dawowa" ta fada tana dariya.
Tabe baki yayi yace, "ce maki akayi nadawo"
"Oh Allah, he will never change, ni ina can ina missing dinshi amma koya kula dani" aranta tayi maganar, Afili tace "yaya akwai abunda nakeso kasani, sumtin is going on in this house"
Kallon gefe yayi babu mai dubansu sannan ya jata gefe danjin wana abu ke faruwa, sau tari dama ita ke kaima rohoton abubuwan dake faruwa agidan dan ba zama yake ba.
Murya kasa kasa tace "bansan full story dinba, naji dai Hajiya na Waya da Aunty Bilkisu akan wani abu, i dunno ko kudi ne ko gida ko kuma ince sumtin is missing i dont really know, naji Hajiya tace tunda kai kaki nemo wa idan ya jaafar ya nemo shi zata
bawa ta fasa baka"
Hankalin sane ya tashi danya gane inda Zancen ya dosa, saidai bazai bari Jaafar yaga Salma ba much less ya yadda da auran suba.
Dakewa yayi yace "little sis kinsan mi zakimin"
Kur tayi tana kallon shi, yace "inaso ki sawa Jaafar ido, idan kinji yana waya akan wata mace ko bincike ki bani feedback kinji"
Kai ta girgiza alamun toh, murmushi ya sakar mata. "yauwa my beautiful sister, you know i like you alot"
Dariya tayi tace "nidai yaya kadawo gida plz, wlh i missed you alot".
"Karki damu nakusa dawowa"
Dadi sosai taji, sun jima yana biyeta sai shagwaba take zuba mai daga bisani ya lallab'a ta ta tafi ya koma motarsa yaja yabar gidan.
Tuki yake yana neman mafitan yadda Jaafar bazai hadu da Salma ba, idan yayi sake kuwa yanaji yana gani zaiga Salma a gidansu, dabara ce ta fadowa mai yadau waya hade da dailing no din Salma.

Alokacin kuwa had'e book dinta Salma tayi cikin jakarta sannan tabar dakinta, gurin Mom ta shiga ta mata sallama ta fito cikin sauri, library na skull takesan zuwa karatu saboda jibi ne zasu fara exams.
Kokarin bude motar tayi taga kiransa, murmushi tayi ta dauka.
Daga can Bangaran cikin sweet voice dinshi yace "Angel of my life, son kowa kin wanda ya rasa"
Dariya tayi kasa kasa, tace "ka fara koh, how am i even sure am your angel"
Yace "believe me, ba karya nake ba, idan ma baki yadda ba God knows it.
"Kaga ni library zani, inada exam jibi, kana ina?
Yaji dadi abunda tace, aranshi yace "perfect, nasan abunda zanyi"
Afili yace "ina driving, ki jirani nazo nayi picking dinki saimuje inda babu wanda zai dameki dan kisamu kiyi karatu, nasan ki da tsokana kar kije kiyi dambe da mutane a library" karashe maganar yayi cikin zolaya.
Shagwabe fuska tayi kaman yana ganinta, tace "nifah bani da tsokana, ko dambe ban taba yibaaa.."
"Hmm, kedin, ki jirani am coming" katse call din yayi, ta fita can bakin gate jiran shi, baafi 20 mins ya karaso ta shiga motan ya kama hanyar office dinsa, tagane hanyar, tace "lailai ma office dinka ne bazaa dameni ba?
Wani shumin kallo yayi mata da saida taji shi a kwakwalwar kanta, murya kasa kasa yace "duk wanda ya dameki cikin cell zan wurga shi..
Ware ido tayi adan tsorace, "cikin cell sai kaca a film"
Dariya yayi bai kuma cewa komai ba ganin yadan tadan tsorata, suna isa parking yayi, suka fito suka shiga elevator har zuwa cikin office dinsa, ita batama san akwai elevator ba kasancewar ta stair security yabi da ita kwana kin baya.
Office din babba ne mai shegen kyau can gefe inda Couch da center table yake takarasa ta zauna shi kuma yA karasa gurin table dinsa ya zauna kan kujerar sa hade da fara aikin danna laptop din gabansa, sosai yaci serious da abunda yake batare daya dubi Salma ba.
Itakam abunda take so kenan, bude handout dinta tayi ta dukafa da karatun General studies da suke dashi.
Bayan kaman awanni uku Mubarak ya shigo office din, ganin Salma yasashi dariya, zama yayi gurin mujahid yana zolayar shi murya kasakasa, b'ata rai Mujahid yayi, yafara magana cikin fad'a, duk ahankali suke magana, Salma bataji komai ba kuma bata damu dason jiba, sund'an jima sannan Mubarak ya fice office din.

Gyaran murya yayi, Salma ta dubeshi
Yace "bani labarin samarin ki ?
Dariya tayi
"Banda saurayi, infact ni bana soyayya"
"Miyasa ?
Ajiye pen din hannuta tayi hade da yin tagumi, amaraice tace "Sanadin So Ummata tasha wahalan rayuwa, daga karshe ma Abbana ya rabu da ita da tsowon ciki, bansan lokacin ba, bansan anyi ba amma ayadda naji labari yadda komai ya faru yasa kwata kwata na cire so araina"
Kallon tausayi yayi mata, tunda yake gida bai tabaji labarin Ummanta abakin Hajiya ba, saidai zaiso sani..
Kaman wanda baisan da rasuwan Umman ba yace "ina umman take ?
Kaman zatayi kuka tace "ta rasu, lokacin daban santa ba, i was 3years old tym din".
Maida dubansa Mujahid yayi bisa laptop din yace "bai kamata ki cire so aranki ba, tunda iyayan ki daban ke daban"
"Hmm, am sacred banso ayi breaking heart dina"
Shuru Mujahid yayi baice komai ba, bayason cikata da surutu, bari yayi sai kuma gobe ya kara jeho mata wata tambayar.
Cigaba da karatun Salma tayi, lokaci Sallah azahar nayi ya nuna mata toilet dake office din sannan yafice zuwa masallaci, bayan ya dawo ya tura aka kawo wa salma abincin take away, godiya tayi.

Karfe bakwai Daddy ya dawo Gida, nan ya tsarawa Mom batun zuwan Jaafar, sosai taji dadi da batun daddy dan kuwa ta kagara Salma tayi aure ko zata nutsu, nan daddy ya shaida mata bayan Sallah Isha'i Jaafar zaizo ganin Salma, dadi sosai taji, wayarta tadauka dan kiran Salma.

Bayan Salma ta idar da sallar Magrib, Qur'an dake ajiye a office din tadau ta karanta sannan ta ijeye ta cigaba da karatunta, lokacin Mujahid yafita masallaci bai dawo ba, kirar Mom tagani tayi azaman dauka.
Aladab ce ta gaidata, Mom ta amsa sannan tace "Salma kibar duk abunda kike kidawo gidan yanzu nan, Daddy zai baki wani Surprise"
Farin ciki ne ya kamata, tace "momy miye ne, dan Allah gayamin i cnt wait saina zo"
Dariya momy tayi tace "idan kinason sani kizo maza yanzun nan, kuma kiyi sauri" katse call din Mom tayi, cike da Murna Salma tahau tattare books dinta ajaka, Mujahid ne ya shigo, ganin tana hade komai yace "keda kika ce sai 10 zamu tafi, kin fasa ne ?
"Eh nafasa, kaini Gida" cigaba tayi da hade komai zuciyar ta fal murna.
Chapter 15 · 0% Book details