← Book details Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 36

Sashe 17

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsabar rad'adin da k'afar take mata dak'yar ta cillara ta fad'a band'aki tayi wanka ta fito ta kwanta gado, sosai k'afar tayi tsami haka dai ta daure har bacci b'arawo yayi awon gaba da ita.

Mujahid ne zaune office yana danna na'ura mai kwakwalwa dake gabansa, jifa jifa yakan k'yallarawa agogon tsintsiyar hannusa kallo, guntun tsaki yaja ganin k'arfe daya ta gota bata iso ba gashi kuma ya k'agara ya ganta.
Mubarak ne ya shigo office din tare da sallama, amsawa yayi ciki ciki ba tare daya dubesa ba, Dariya Mubarak yayi hade da zama yanai kallon office din tamkar wani sabon bak'on sa, duban Mujahid yayi, cikin zolaya yace "yau matar ka bata zo ba?
Sai sannan Mujahid ya dubeshi, murmushi yayi.
"Zata zo, na tabbata ma tana hanya"
"taku salon soyayyar daban take, wai ma yaushe zaka rama abunda tama ? Mubarak ya fada ba tare daya bar kyalkyalewa da dariya ba.
Nisawa Mujahid yayi, yace" abokina ina cikin yanayin, na rasa mai zan mata kuma ma bazan iya cutar da ita ba, koba komai yar'uwa tace ta jini, na hakura, yanzu so nake na sadata da Hajiya".
Dakatar da dariyan Mubarak yayi, yace "naji dadi ka gano gaskian zuciyanka, Hajiya kuwa sai tafi kowa farin ciki da kai, yaushe zamuje mu kai amaryar mu gidan sirika.." Cike da zolaya Ya karashe maganar, mugun kallo Mujahid yamai yamike ya fice tare kokarin gitmse dariyar data zomai.
Murmushi Mujahid yayi yadau wayarsa dan kiran Hajiya yi mata albishir, dailing nambar zaiyi, Salim ya fadomai cikin office kamar wani mayunwacin zaki.
Ajiye wayar yayi yabishi da kallon waya baka izinin shigo min office, cikin rashin damuwa da kallon dayake mai Salim yaja kujerar dake fuskantar sa ya zauna had'e da dora kafa daya kan daya, sannan cikin karaji yace "Sir ba batun aiki ya kawo ni nan ba."
Ran Mujahid yakai mak'walan baci, shuru yayi yana jiran abunda zaice.
Salim ya cigaba
"Salma tawace, tare ka fara ganin mu, tun kafin ta sanka muke mu'amala, dan Allah karka shiga tsakanin mu, muna matukar son Juna, adalilin ka yau ta zubar da cikana da take dauke dashi"
Mik'ewa Mujahid yayi, fuska daure, afusace yace "tashi ka fita kafin nasa a cilla ka waje"
"Kayi hakuri sir banxo da fad'a ba" mikewa Salim yayi had'e da risinawa sannan ya fice a office din.
Tsaki yaja ya koma ya zauna ranshi na k'una, ko kadan bai yadda da abunda Salim yace ba, yasan kafin su saba da Salma kallon marar kamun kai yake mata yanzu kuwa d'an zaman da yayi da ita ya tabbatar ba abunda yake tunani bane, kuma ma yasan ba yadda zaai Salma ta kaiwan shashashan yaron nan kanta, tsaki ya kuma ja yace "Salma tafi karfin ka, baka isa ka rainamin hankali ba, wawan banza kawai". Wayarsa ya dauka yahau kiran Salma, sau biyar ya kira tana ruri baaa dauka ba, ajiye wayar yayi zuciyar sa na aiyyana mai abubuwa, saurin kawarwa yayi ya cigaba da aikin gabansa.

Bayan la'asar Salma ta farka bacci da matsananci ciwon kai, dakyar ta yunkuro zaune taji kafar tai mata nauyi, wani irin juwa take ji, sauka tayi kan gadon ta rarrafa zuwa bandaki ta dauro alwala ta fito tayi sallah zaune sannan ta koma gado ta kwanta, daukar wayarta tayi taga kiran shi, da sauri tayi dailing no dinsa.
Kaman jira yake, yayi azaman dauka yace "kina Ina ?
Murya ciki ciki, kaman mai shirin kuka tace "ina gida, tuna dazu nadawo saidai bana jin dadi"
Bata rai yayi.
"Mike damun ki ?
Shuru tayi, tanason cemai kafar ta ke ciwo tana tsoron ya tambayeta sanadi, ga kuma kanta na ciwo, wahalalliyar ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "kaina ke ciwo".
So yage ya gasgata zancen Salim, yace "deme kuma ?
Zuciya daya bakinta ya furta "cikina"
Baice komai ba kuma bai jira abunda zata kuma cewa ba ya katse wayar, bata kawo komai aranta ba ta ajiye wayar hade da gyara kwanciyar ta.
Kasa gasgata zance Mujahid yayi, yanaso ya yadda da abunda Salim yace ya kasa, kalllon wayarsa yayi dake rike hannusa jiran ko zata kira shi yaji shuru.. Jiki sanyaye ya ajiye wayar aranshi yana fadin "Tabbas Biri yayi kama da mutum....

Masu korafin basu san ma'anar zuma sai da wuta, bara na maku bayani dalla dalla.

Shi sak'ar zuma baa iya daukan shi saboda Zuma🐝🐝 dake makale jikin sakar, komin yadda zaki ki kori Zuma bazata koru ba tsananin yadda take da taurin kai da kafiya maganin ta daya ce wato Wuta...kinasa mata wuta zata saduda ta gudu tabar sak'arta ba tare da bata lokaci ba.

Shiyasa hausawa sukace Zuma Sai da wuta.

Shin acikin
Mujahid
Salma
Salim
Jaafar
Da
Junaina waye Zuman waye wutan ??

Ina jiran Amsar ku....
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
®NWA

Vote me on Wattpad @Cutexarah

xarahbukar.wordpress.com

52

Da Magrib Mom ta lek'a d'akinta kansacewar taji shigowarta tun rana, ganin bata da niyyah fitowa ya sanya ta bibiyar ta, kwance ta ganta can k'arshe gado akudundune, k'arasa wa gurin tayi tahau tashin ta, bude ido salma tayi, jikinta gabad'aya k'yamar yake tsabar yadda zazzab'i mai zafin gaske ya cafketa, hankali mom ne ya tashi ganin yanayi ta, ba tare da b'ata lokaci ba ta taimaka mata tasa kaya suka fita waje, kiran Salim tayi yaxo yaja su zuwa asibiti, a mota sai faman yi mata sannu yake tamkar ba shine sanadi ba, bata iya amsa shiba har suka isa asibiti aka bata gado.
Koda Mujahid ya koma gida kasa zaune yayi, kalaman Salim ke yawo a kwakwalwan kansa. Kamar wani tab'abb'e yahau girgiza kansa yana fadin it cant be possible, yana son Salma kuma yayi trusting dinta, ba zai tab'a yadda da zance salim ba" wayarsa dake ajiye kan 3 sitter yadau hade da mik'ewa tsaya yayi dailing no din Salma, har kusan sau biyar bata dauka ba, nan take wani mugun haushin ta ya dirar mai, cilla wayar yayi kam kujerar sannan ya zauna kasa hade da dafe kansa. Atakaice dai ranar dakyar ya iya runtsawa, da safe bayan yayi shirin sa na office fita yayi, bai zarce ko ina ba sai gidan su Salma, ya jima yana horn daga bisani mai Gadi ya iske shi ya sanar mai babu kowa agidan sai Salim, hajiya da diyarta kuma suna asibiti, Alhaji dama baya gari.
Komawa Mota Mujahid yayi ran sa bak'in k'irin, zuciyar sa kuwa ta gama gasgatar mai da gaskian lamarin, wani irin haushi kanshi yake ji da tun farko yayi sake har Salma ta shigo mai rayuwa, yana son salma, she's the only gal da yasan he can die for, saidai bazai taba yadda ta raina mai hankali ba much less tayi deceiving dinsa with her cute innocent face, nambarta dake wayar sa yayi deleting hade da kunna motan, kallan gate din gidan yayi yace you're dead to me" afusace yaja motar sa yayi gaba.

"Wai yaushe hakan ta faru bansani ba" acewar Mom, zaune take gefe gadon da Salma ke kwance, kafar mai targade daure da farin gyalle, Yunkurowa Salma tayi ta jingine jikinta a karfan gado, Magana zatayi Salim ya shigo rike da flask da Mom ta aikeshi gida ya dauko, Harara Salma takai mai, yace "sannu sister, ya jikin ?
Atakaice tace "lapia" duban Mom tayi tace "ina tafiya nayi missing steps na fadi"
Mom tace "tsautsayi kenan baya wuce ranar sa, Allah ya tsare gaba, ya ciwon Kan ?
Da sauki" Salma ta amsa, tashi Mom tayi ta fita gurin Doctor, kusa da ita Salim ya karaso hade da marairece fiska yace "sis am sorry, duk nina jaza maki"
Tabe baki tayi
"Ba komai ya wuce, ni yanzu kawai gida nakeson komawa, nabar wayata kan gado" kaman zatayi kuka ta karashe zance, Mujahid ne aranta, tana son fadimai tana asibiti karya jita shuru.
Mom ce tadawo dakin tana waya da Daddy ya mike ya fice, mikewa Salma wayan tayi ta amsa yiwa Daddy magana.

K'ashe gari likita ya sallame su, suna isowa gidan wayarta tadau ka taga miss call dinsa, farin ciki ne ya ziyar ceta ganin yadda ya damu da ita, kiran sa tahauyi fuskar ta dauke da murmushi.

Alokacin Mujahid zaune yake office yana danna laptop dake gabansa, fuskar sa babu annuri, shi kadai yasan yadda yake jin zafi azuciyar sa, yana ganin kiran nambarta yaki dauka, har kusan sau goma takira bai dauka ba, karshen ma wulla nambarta yayi a reject list ya cigaba da aikin gabansa yana huci.
Chapter 17 · 0% Book details