← Book details Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 41

Sashe 38

Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Hakika lokacin da mutuwar salma ta doki kunnen mu ta gigizamu matuka.Tabbas mutum ba a bakin komai yakeba ,duk abinda kake allah yana kallonka.
Shirin da muke na kaiwa sameemah wajen magani muka bari domin zuwa gida gaisuwar mutuwar salma.
Tunda muka je kullum said nayi waya na tambayi ya jikin sameemah,saidai maganar daya ce kullum saukin bahaushe.
Bayan sadakar uku muka taho saboda kowa yasan halin da muke ciki na jinyar sameemah.
Bamu muka iso garin porthacourt ba sai wajen karfe takwas na dare,a lokacin na ajiye saleemah a gida na nufi wajen sameemah,itama saleemah bani gaisuwa tayi akan na kaiwa sameema duk da tasan ba amsawa zatayi ba.
A zaune na sameta a dakin da ake killaceta ta sunkuya kaman wanda tayi bacci,tausayinta ne ya kamani musamman ganin kayan dayake jikinta tun wanda nasaka matane kafin mu tafi,banyi mamaki ba danna san bazata bari wani ya matso kusada ita ba,ga duhu da kuma sauro,wannan bai sa na damu ba saboda nasan ba cizonta zasuyi ba.
Karisawa nayi gavanta na tsugunna,dagowa tayi a hankali tana kallon fuskata kaman mai nazarin wani abu,can kuma sai ta rungumeni da karfi,da alama tayi kewata dayawa,hakan yayimin dadi ba kadanba,duk da halittunta da siffarta sanjawa suke da kadan kadan amma hakan bai sa kida da rana daya naji kyamar matsowa inda takeba,saima tausayinta dayake kama zuciyata.
Cikin dabara kaman ko yaushe na tsaftace mata jikinta kafin nasaka mata rigar ta,banyi niyyar barin wajenta ba dan na kudiri niyyar gobe zamu kaita wajen malamin da aka turamu wajensa.
Washagari da safe nayi nayi taci wani abu amma taki kulani,nima nasan bazata ci ba kawai gwadawa nake ko za'ayi nasara wani lokacin,muna cikin hakanne su ummee suka zo tareda su alhaji musa,har da inna ramatu wacce ta biyo baba umaru dan taga jikinnata.
Suna hada ido da sameemah tayi kanta da sauri tareda kaman kafarta da garzamata hakoranta,ihu take tana kara amma bata sauta ba saida muka hadu tukunna.
Lashewa bakinta take wanda yayi ja da jinin inna ramatu kuma tana murmushin mugunta,kokarin komawa takeyi amma su baba umaru suka dauki inna ramatu zuwa asibiti dan suma tayi dan wahala.
Ba karamin rauni sameemah tayi mata a kafa fa hadda cire mata naman cinya.
Dukkan mu mamaki mukayi da abinda ya faru,sai a lokacin na kula ba abinci take bukata,so take ta dunga cizon mutane amma kuma ta kasa cizon wanda suke masoyanta.
Wani ruwan magani aka sake yi mata wanka dashi wanda zai saka jikinta ya shika kaman bata da laka,sannan akasaka wani sasari a hannunta da kafarta nikuma na daure karshensa a kunkumina. Da haka aka kinkimota zuwa cikin mota kowa sai bugu kirjinsa yake.
Driver alhaji musa ne yake tukamu sai alhajin a gefensa,a baya kuma nida ummee ne sai kuma sameemah da take cinyata a rike. Motar da take binmu kuma su baba umaru ne a ciki harda malamin da yayi mata magani,ba yanda ba ayi na baba umaru ya tsaya a wajen inna ramatu amma yaki yarda,a cewarsa likitoci zasu kula da ita.
Tafiya Muke a hankali har mun kusa kauyen mun fita daga cikin gari,mutsuniya naji sameemah tafarayi kaman wanda ake tsikararta,saurin dubawa nayi naga idonta a bude,saidai bakikkirin suke kaman an zuba gawayi a cikinsu,wani rin mika tayi tareda yin wata kara saida muka rufe kunnuwanmu dan karta bata mana dodon kunne.
Jijjigar datake ne yasa dole saida driver ya tsayar da motar,saboda tana koarin jawo muyi hatsari,kofar da take kusada mu ta banke da wani irin karfi tafita da gudu.
Jana take saboda hannunta a daure yake kuma sarkar tana kunkumina,tirjewa nake tana jan mu yayinda suma malamin suke binmu a baya,gashin kanta ya tattashi sai gurnanai takeyi ,danni kaina kallon naci amanarta take min,dabarace ta fadomin ganin bazan iya tsayar da ita da haka ba saina nannade sarkar a jikin wata bishiya ina numfarfashi dannima a matse nake a jikin bishiyar sosai.
Wani mutumine mai dogon gemu da cikar gwarzini yazo inda muke,kallo na karemasa dannasan ba malamin da muka zo dashi bane,kara tirjewa take tana ja da baya tareda sake daga sautin kukanta lokacin da mutumin ya tunkareta,wani abu ya shafa mata a goshinta take ta yi wata mika ta fadi a wajen kaman ta mutu.
Motar muka koma domin karisawa gidan babban malamin,sai a sannan na kula aahe shine wanda yazo wajenmu a jejin,gidannasa babu nisa dan mun iso garin ma ashe.
A wani dakin kumadu aka saka ta saidai wannan duk jikin dakin rubutun Qur'ani ne,hadda wasu addu'oin da baka sansu ba ma.
Muna isa aka kaimu masauki domin muyi sallah azahar dan a ranar za'ayi mata rukiyya basai gobeba,dan yawan jingirtawar da akeyi yawan kara mallake jijinta da sujeyi .munayi sallah bayan munci abinci,dan abincinma dabawa mukayi saboda tashin hankalin da muke ciki.
Kafin mushiga dakin da take saida ya kafa shaidu tukunna. Banda wacce take haila,banda wanda yakeda aljanu a jikinsa,haka kowa sai yana da alwala,kuma bakinsa bazai daina kiran sunann allah ba har a gama.
Haka muka amince da duk sharadinsa kafin muka zauna a wajen,sameemah tana tsakiyar wajen an saka mata wata doguwar riga fara,bayan mun zauna ne malamin ya umarci wani a wajwn akan ya sinceta daga sasarin da take daure dashi.
Mudai muna ganin ikon allah har yagama sunceta amma bata ko dago kaiba bare ta motsa daga yanda take.
Karatu aka fara yana amsa kuwwa a cikin dakin,kadan kadan jikinta yafara rawa kaman ana jona mata shokin,bayan an dan dade da karatunne ta fara ihu tana yagar jikinta da karfi.
"Kai Wai miye kuke hakane,ba dama ku barmu mu zauna lafiya mai muka muku haka,dan mutum daya bazaku barmu mu dauka a matsayin namu ba?"
"Badaku nake ba kananan shedanu ,so nake shugabannaku dayake turoku yazo da kansa,ku fada masa shine ke nema,ku kuma idan nan da wasu mintina baku fitaba to sunan ku matattu"
Cigaba tayi da ihun bayan ta tayi magana malamin yabata amsa,can kuma sai tayi shiru alamar abun ya lafa.
Ganin malamin yafara karatun dayafi na farkone yasa muma muka fara babu tsayawa,fatar jikinta ce take sauyawa zuwa baka,ga farcuna da duka fito sunfi na farkon kafin zuwan mu nan,tsorone yashiga zukatanmu saidai bamu daina karatun da muke ba har saida mukaji ta fara gunji,malaminne yatashi da sauri ya debi wani ruwa a kofi ya watsa mata,bayan ta gigicene yasake diban wani ya zuba a cikin bakinta ta hafite da sauri tana kama makogaranta tareda sakin wani ihun dayafi na farko,magana ta fara cikin wata babbar murya,
"Ka bukaci nazo amma kuma kana cutar dani ai ba haka mukayi da kaiba ko,zancen na sauta kuma bazai yiyu ba dan itadin muna tareda itane tun tana shekara uku a duniya"
"KO tare aka haifeku da ita yau zaka barta,sannan kuma ka dawo mata da kuruwarta daka dauka,wacce kasaka mata a jikinta kuma yanzu zan fitar da ita ko kana so ko bakaso"
"Ahah karka cire ruhin mu dayake jikinta ka fadi duk abinda kake so zamu baka,bakasan tsawon lokacin da muka dauka muna rainansa a cikin jikinta bane,saida lokacin tashinsa yazo sanann zaka bata komai,zakayi mana asara dayawa,dan haka duk abinda kake son a duniyar nan zan baka matukar zaka bar ruhin dayake jikinta lafiya,har nata ruhin ma zamu dawo mata dashi indai zaka bar wannan baxaka fitar dashi ba"
"Eh shikenan na yarda da yarjejeniyar da mukayi dakai,zaka bani wani abu,sukuma yan uwanta zamu mantar dasu,amma da sharadin ruhinta ma zai zauna a jikinta kafin daya bak'in ruhin ya tashi"
Mai kunnuwana suke jiyomin,ai malamin ya yadda da abinda shedanin ya fada kenan,har na tashi zanyi wani abu sai naji nakasa tashi daga inda nake ,murmushi fuskar sameemah tayi wanda daga gami ba ita bace wannan.
Can Bayan wani lokaci muna zaune mun zubawa sarautar allah ido,vanda kiran sunan allah babu abinda nake a cikin raina,wani haskene yashiga jikin sameemah kafin ya bace kamar bai shigaba.
Hakan yana faruwa malamin yayi sauri yah watsawa sameemah wani ruwa dan kadan dayake cikin wata jarka,wani kara tasaka kafin tafara cewa,
"Ka cucemu ka yaudaremu saida muka dawo mata da ruhin ta sanann zaka juya mana baya,mai yasa zaka kafe ruhinta ta yanda bazamu iya kara dauke shiba bayan kasan munyi yarjejeniya akan bazaka cutar da ruhinmu dayake jinkinta ba sanan........."
Saurin yin shiru tayi sanadiyyar wani ruwan da malamin ya zuba a bakin sameemah sannan ya matse bakin saida ta shaye shi,wata addu'a ya cigaa dayi kafim yayi mana alamar mucigaba dayi,muna cikin yine mukaga ta fara rike cikinta can kuma sai ta koma rike makogaro,shakewa muryarta tayi tafara kokarin amai.
Wani bakin ruwa ta fara amarwa can kuma saiga kan wani abu kaman maciji bakikkirin,zuwa lokacin kadan daga cikinmu ne suke iya bude bakinsu suyi addu'a ,ciki kuwa harda yarannasa idon su yayi wuri wuri.
Cigaba tayi da kokarin amai abin yana fita dogo dashi har ya kare fitowa daga cikin bakinta,motsi kadan abin yayi kafin yadaina motsin can kuma malamin ya zuba masa wani abu kaman farin gari nan da nan ya bace kaman bai daba wanzuwa ba.
Kan sameemah dukka muka nufa wanda ta fadi tun lokacin da abin ya fita daga jikinta.
Ru wan mag an in ya cigsbs da shafa mata,yana addu'oi kafin ya kalleni .
"Mashaallah in allah ya yarda an samu nasara,saidai banida tabbcin tashinta,dan da kyar idan bai yi mata lahani a cikin ta ba lokacin daxai fito,musamman ma daya dade a jikinta,shine yake sakata komai sannan da dafinsa take amfani wajen kisa da kuma bada kariya ga kanta badan komai ba dan yasamu kariya jikinta har zuwa lokacin da zai mamaye jikinta.
Yanzu munyu nasarar fitar dashi dama dashi suke iyah nemota har su san inda take,sannan kuma sun dawo mata da ainihin kuruwarta,dan haka ku gaggauta kaita asibiti a duba lafiyarta,sannan ga wannan ruwan shi zata dunga sha daga lokacin data farka har na tsawon sati guda,idan kuma ta manta wani abun kar a tursasa mata,in ma kuma babu matsala shikenan,zaku iya tafiya allah ya kiyaye ya kuma sawwake ameeen"
Kinkimarta nayi da sauri muka nufi mota domin kaita asibitin,su alhaji musa da kuma baba umaru sai godiya suke masa,har sannan hankalin su bai dawo jikinsu ba sa abinda suka gani.
Bamu wani dadeba muka iso asibitin cikin barrack din kasancewar gudu muke a motar ba kamar lokacin da muka tafiba.
Muna zuwa ummee ta saka kayanta na aiki,duk da jikinta har sannan a sanyaye yake daga ka ganta kasan ba karamin kokari takeba kawai.
Dakin taimakon gaggawa aka shiga da ita,inda aka shiga bincikar ina ne yake da matsala a jikinta,babu wani rauni a jikinta saidai duk ilahirin halittar cikinta ta gaji sosai wanda hakan yasaka ta shiga coma saboda shock din da jikinta ya shiga.
Duk mun ji dadi da babu rauni a cikinta amma shiga coma din ma bai mana dadi ba sam.
Dakin kulada ita aka mayar da ita,duk an manne hancinta da wayoyin dazasu dunga kai mata abinci zuwa cikin jikinta.
Kasan cewar akwai ummee dazata dunga kulada ita sannan kuma akwai wasu nurse wanda suke shige da fice sai yazamana ba sai mun zauna tareda ita ba saidai mu dunga zuwa dubata kawai.
Duk da cewa hankalin mu ba tashe yake kaman da ba amma kuma ba a kwance yake ba sam,domin yau kimanin sati biyu kenan da kawai sameemah wajen mai magani amma ko motsi batayi,saidai na'ura da take nuna cewa a tana raye ba ta mutuba.
Tunda sameemah tashiga sati biyu da shiga coma hankali na yafi na kowanne lokaci tashi,saboda gani nake kaman bazata tashi ta dawo gareniba,a bakin kofar na tsaya ina kallonta yanda take kwance,ita da matacce basuda maraba,karisawa nayi a hankali har zuwa onda take kwance na zauna a kujerar da take gefenta,kama hannunta nayi na rike wanda karin ruwa yake shiga ta cikinsa,muna nan zaune har na kara kaina da katifar da,take kwance akai,can kamar a mafarki naji kaman tana motsa hannunta dayake cikin hannuna,basarwa nayi danna san bazai wuce gizo takemin ba kaman yamda ta sabayimin acikin mafarki,cigaba tayi da motsa hannun wanda zuwa lokacin kuma abin yawice gizo,yafara zama kaman gaskiya ,kodai da gaskene kai itace take motsi ???......
Chapter 38 · 0% Book details