← Book details Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 41

Sashe 12

Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ina jin sanda yah bugomin kofar da ƙarfi bayan ya fishe,ko ba a faɗaminba nasan yah ji zafin maganar danayi masa,hakan yanamin daɗi idan mutane suka ɗaukeni a wata siga da zuciyarsu ta raya musu ba tareda sunyi bincike akai ba.
Kayan baccina na saka tareda bin lafiyar gado,har sannan ban daina murmushiba da kuma tuno yanda yake bin jikina da kallo,wanda kuma hakan zai ganshi yah bari,dan bana kowa bane na wane ni ka kadai.
Washagari da safe ina tashi da feɗuwa na sauƙo daga kan gado,dan yau kam nakoma sameemah tah kuma,na gaji da waccar wacce bata yin abinda taga dama,kokuma ta dunga barin abu idan anyi mata.
A wajen saka kaya dama wani wando na samu jean irin mai ɗamewar nan,sai wata me ɗan tsayi,itah ɗinma saboda rashin mutunci ban barta hakaba saida na ɗaureta ta koma dadai inda wandon zai fara,facing cap na ɗauko irin rigar na nasaka sannan na sneaker suma masu adon pink.
A taƙaice dai na fito kaman wata mawaƙiyah a ƙasar turai dama kuma ga farina mai harkene sosai.
Fitowa nayi falon dadai su saleema suna karya wa ita da sameer a table,farouq ma yana gefensu yana cin taliyar yara.
Ɗago min hannu yayi tareda cewa,
"Hi anty"
"Ya kke ka tashi lafiyah"
Dariyah yamin irin ta yara yana ɗaga kai,kallon iyayennasa nayi tareda ɗaure fuska kaman banice nayi wa yaron murmushi ba.
"Ku kuma na tafi juggling na exercise kwana biyu ina zaune har na fara tara cholestrol.
Sameer ne dayakai shayi bakinsa yayi saurin zubarwa har yana ƙwaruwa kafin yace,
"Me......menaji kince,excercise?"
"Ashe kaji mai nace ɗin kake neman na maimaita"
"Toh bazakije da wannan kayan ba kam"
"Saikuma kayi ai wai karuwa taga mai wa'azi"
Juyawa nayi na fita hankalina kwance,dan tundaga cikin falon na fara juggling ɗin ban fitaba.
Hanyar dazai kaini jejin cikin wajen na nufah,dan daman dan yaganine nace masa cikin wajen zan shiga,amma dayasan yanda banason cikin mutane daya sau ransa a inuwa.
Bani na dawoba sai can wajen tara da rabi,dayake tun bakwai na fita.
Wanka nayi tukunna na fito falon.
Wayata ca tayi ringing ina ɗauka naga baƙuwar lamba,saidai nasaka a kunnena naji ashe wanda aka bawa saƙon kawomin karnuka nane yazo yana bakin barinki sojojin an hanashi shigowa.
Fita nayi zuwa bakin wajen,dayake akwai tazara na jima ina tafiyah kafin na iso bakin wajen,su bingo suna kallona suka fara ƙoƙarin ƙwacewa a hannunsa.
Alama nayi masa da ya sakesu,dan daga gani a tsorace yake dasu sosai.
Aikuwa kaman jira suke suka rufo da gudu kaman sunga nama,tsugunnawa nayi na taresu,sai kaɗamin jela sukeyi.
Maganar wani soja ce tah ɗago dani wanda yakeyi kaman mai koyon hausa.
"Hajiyah zakina biyamu kuɗin ƙarba saƙo fah"
”kudin me kuma ana zaune kalau,ba abinda zan baku idan kunga kuma zaku iyah toh ku biyoni gidanan ku karba"
Har zai sake magana wani a cikinsu yah raɗa masa abu a kunne,yana jin hakan yah yi shiru yana juyah fuska.
A hanyane muna tahowa na kulada yanda raze taƙi sauri shikuma bingo yaƙiyin gaba ya barta kaman yanda suke wani lokacin,tsayawa nayi ina ƙaremusu kallo,sai a sannan na kula da yanda cikinta yayi faɗi yai ƙasa,kallon bingo nayi mai kama da harara,saurin juyawa yayi yana shinshina bushasshiyar ciyawar da take wajen,shafa kanta nayi kawai kafin na ce,
"Allah ya sauƙeki lafiyah"
Da haka muna tafiyah har muka iso kofar gidannamu,wannan wanda yayi mana tambayoyine lokacin farkon zuwana gidannan,dan na kula a duk cikin sojojin da suke gadi yah fi kowa iyayi da taƙaama.
Chapter 12 · 0% Book details