← Book details Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 41

Sashe 3

Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Shekara talatin da biyar suka wuce,lokacin ina matashin saurayi mai neman na kansa,duk da yayuna da kuma babana suna iyah kokarin su akan komai naci da sha, har ma da aure idan mutum yaso niyyar yi.
Saidai ni ban yadda da hakanba don nafison nakasance ina neman abin kaina bawai na dogara da abin wani ba.
Hakan yasa na yanke shawara inda na fara bin babbaan yayanmu mai suna ABDULLAHI,ana ce masa malam Audu,wato shine kawunku kawu audu wanda yah rasu tun kuna kanana,sanadiyyar ciwon koda.
Shikuma sana'arsa shine saida kayan fulani a garin bauchi a kasuwar wunti. Bayan wani dawowarsane nace nima zan bishi mutafi koh taimaka masa saina dunga yi,baiyi musu ba kuwa saima dadi da abin yabashi.
Lokacin da muka tafi saida nayi shekara d'aya kafin na zo gida,inda anan ne na hadu da innarku hajara tana kawowa fura daga kauyensu zuwa garin mu,da farko nasha wahalar shawo kanta saboda macece itah mai kunyah dakuma sanin yah kamata.
Lokacin da muka daidaita kanmune muka sanar da manyam suka shiga zancen,da yake aurene ba irin na yanzu ba sai an ja lokaci,wata d'aya mukayi sai gashi mun tare a dakin Da'aka yimana da kuma dan zagaye.
Zaman aminci da ganin darajar kowa mukayi har tsawon shakera biyu kafin hajara tah samu ciki,
DA take ni ba anan nake ba ina wajen Audu bansan me ake cikiba,ashe hajara wahala yake ji a wajen mahaifiyar mu kasancewar bata sonta,tafi son na auri y'ar kawarta aminyarta wato Ramatu,saidai duk abinda yake faruwa hajara tah toshe duk wata kofah da zansan abinda yake faruwa,har saida tazo haihuwa ne lokacin nazo akace bazata iyah haihuwa lafiyah ba saboda karancin jini da kuma rashin samun ishashshen abinci mai gina jiki.
Abinne yaban mamaki ganin babu abinda aka fi karfinsa ,tun daga sannan na fara zargin ba lafiyah na musamma yanda naga tah rame tayi baki,mata fara da itah amma tah koma haka.
Allah cikin ikonsa dayah dubemu sai hajara ta haifi d'anta na miji wata ranar juma'a bayan doguwar nakuda da kuma jin jiki da tayi,har masu karbar haihuwar suka ce bazata sake haihuwa ba ma saboda yanayin laushi da mahaifarta tayi.
Ranar suna aka sakawa d'a suna SAMEER,bayan an yanka masa rago.
Kasancewar ina nan nazo gidan saboda haihuwar matata,sai hajara taji dadi har tayi wankan arba'in dinta cikin walwala da kwanciyar hankali,duk da bata fadaminba amma nasan taji dadin jama danayi a tareda itah batareda na tafiba.
Tun da IYAH taji cewar hajara bazata haihuba sai zakaminta nasan na auro inna ramatu yah tashi,aikuwa tun kafin haajara tayi arba'in tashiga ta fitah saida tah kawo ramatu gidannan,duk da bana son auren amma nayi na'am da cewar hakan yana cikin kaddarata.
A zama na da ramatu babu inda na banbanta ta da matata hajara saidai sha'nin mata dakuma in sun samu daurin gindi daga wajen uwar miji,sai hakan yakara hura wutar tsiyar ramatu a cikin gidan.
Tun kafin hajara tayi arba'in ramatu da samu ciki,wanda itah bansamu damar ganin haihuwar ramatuba sai saƙon haihuwarta daya sameni kawai.
Ban tashi dawowa gidaba saida sameer yayi wata shida yayinda shikuma dan inna ramatu (manjo )yake da wata huɗu.
Aikimmu kam alhamdulillahi yana karbuwa sosai,dan yanzu shagonmu yah cika da kaya,har na samu hayar daki ɗaya wanda zan iyah tafiyah da matata daya muzauna.
Nan ma wani artabun aka buga ina na yanke shawarar yin wata shida da kowacce sai kuma tah koma wata tazo.
Bayan shekara goma muna kasuwanci sai ciwo yah kama mallam Audu inda ya barmin kasuwamcin nakeyi,saidai nima banyi wata biyu ba akayi godabara kaya suka ce ɗibemu a hankali.
Hakan yasa nayi niyyar komawa gida saboda komai yah kare,wannan zuwan da ramatu mukaje sai masifah takeyi wai an koma yin abinci marar daɗi,nida jinta kawai nakeyi dan banida amsar dazan bata a lokacin.
Da muka isa gidanma wani tashin hankalinne yasameni, domin a kwance na samu hajara a ɗakinta rai a hannun allah,wai laulayin ciki takeyi tun wata uku da tafiyarmu,gashi bayason abinci barkatai sai wanda tah zaba tukunna.
Nan nafara jinyarta gashi kuɗin hannuna bashida yawa sosai,ana cikin hakanne wata hajiyah ta turo saƙo akam idan inaso naje zata bani aiki na gadi a gidansu,kuma ta yaba da hankalina saboda ina yawan sayar mata da kaya,mun saba a wajen cinikayyah.
Abinda nayi tunani shine aikin gadi sai an zauna a gidan,sannan indai za'a zauna toh fah wata rana za'a bata,idan kuwa na kuskura na tafi da ramatu toh a ranar za'a koromu,sannan kuma bazan iyah tafiyah na bar hajara a wannan halin ba,kuma halin da take ciki tana bujatar taimako sosai.
Hakan yasa na yanke shawara babu wanda yahsani na cewa ramatu aikin dako zan tafi yi a wani ƙauye,kuma bazan iyah tafiyah da hajara ba bata da lafiyah,tsalle tayi ta dire akan bazata je wajen wahala ba saidai na tafi da hajara kk kuka nasan yanda zanyi,lokacin kuwa ta yaye ƴarta sameerah.
Baƙaramin daɗi najiba dana samu nakashe wannan wutar.
A ranar na fara yimana shirye shiryen kayan ita dai hajara kallona kawai takeyi,dan nasan idan zanyi shekara ina abu indai ba faɗamata nayiba bazata tambayeni ba.
Ranar tafiyarne na kaiwa iyah kayan sameer saboda yana zuwa makaranta shi,kuma ma yayi girma a tafi dashi gashi bamusan wajen ba muma tukunna.
Mun daɗe muna tafiyah a mota sai gamu a garin bauchin yakubu,hajara kam duk tah galabaita saboda jijjigar mota ,gashi dama koba mota amai takeyi inaga ta samu dalili.
Mai adaidaitah sahu muka ɗauka zuwa anguwar rail way inda tayi mana kwatancen gidan.
Shima kansa mai adaidaitan baisha wahala ba saboda gidan ba a lungu yake ba,kan hanyane inda kowa zai gane.
Kuɗin na bashi kafin na ranƙwafo da hajara zuwa jikina muka fitah zuwa bakin gidan.
Duba takardar ta take hannuna nakeyi sannan kuma ina sake duba gidan,"anya kuwa shine?" nafaɗa a raina,dan gaskiyah giraman gidan bayyi kama da wanda za'a gayyaci kamanni cikinsaba.
Ganin ba sarki sai allah ga kuma matata tana bukatar taimako ne yasa kawai nayi shahada da tunkari kofar gidan,saboda mun riga mun zo kuma ai babu batu komawa.
Wasu inyamuraine masu kayan sojoji suka buɗe mana kofar gidan,saboda tsabar tsoro bansan lokacin dana mika masa takardar hannu na ba,saboda dama tace idan nazo nabawa ɗayah daga cikinsu,zasu barni na shiga.
Hakan kuwa akayi ina mika masa yabani hanya wuce ina mamakin toh wane irin aiki kuma zanyi,danni a iyah tunanin gadi nakawo da tace zata ban aiki a cikin gida kuka zan iyah zuwa da iyalina,toh kodai ba nan bane,dan nan kam suna da mai gadi,wanda koh kare bazai nuna masa gadin ba ,dan ga ganinsa a fuska ma zaka tantance.
Nidai ban sare ba muka cigaba da tafiya a hankali saboda yanayin tafiyar hajara da bata sauri saboda rashin karfin jiki.
A bakin wata kofah muka tsaya saidai itah karamace amma dai tafi kofar shiga ɗaki girma,da wata yarinyah muka,haɗu tah yimana iso zuwa ga matar gidan.
Shiga mukayi tareda itah bayan tah dawo tacemana mu shiga.
Tabbbb danƙari wani kayan sai amale aradu,ai ina arba da inda aka shigo damu na saddaƙar da cewa ba'a Nigeria nake ba kawai,dan wajen badai ado ba kam.
A ƙasan wajen muka samu waje muka zauna inda mai aikin tacemana mu tsaya.
Bata daɗe ba kuwa sai gata ta shigo bakaman sauran masu kuɗiba da zasu iyah barka a zaune har awa guda.
Sallama tayi mana tareda nuna mana kujera akan mu zauna,nidai duk hankalina bai kwanta da zaman kujerar ba saboda kar mu bata musu,amma kasancewar ƙasan da sanyi ga kuma yananyin jikin hajara sai muka koma kan kujerar.
Har ta gyara zama zata fara magana sai kuma tayi saurin kiran wata a cikin gidan,saida ta bayyana naga ashe wacce ta rakomu ce,
"Yawwa blessing kawo musu abin sha da abinci mana,kinga har na fara cikasu da surutu kafin na bansu wani abu(juyar da kanta zuwa ga inda muke sannan tah cigaba da cewa).
Afuwan malam umaru,naga mai ɗakinnka ma kaman batajin daɗi sainaga kaman ma ƙaruwa zamu samu,yamzudai bari na saka akaiku ɗakin dazaku zauna kuci abinci ku huta daga baya sai muyi magana koh?"
"Toh shikennan babu matsala duk yanda kika ce ranki yah daɗe"
"Kacemin madam kawai,itah kuwa tah kirani da sunana Maryam,allah bamu ikon zama na fahimatar juna"
Daga haka ta tashi tayi hanyar wan beni,itah kuwa hajara tun gaisawa da sukayi bata ce komai ba sai murmushi da take kawai,duk wanda yaganta yasan akwai alamun gajiyah a tareda itah.
Ɗakine mai matsakaicin girma amma yah ƙawatu kam matuƙa,gashi an shareshi tasss sai ƙamshi yake fitarwa mai daɗi da kuma sheƙi.
Wacce hajiyah maryam ɗin takira da blessing ce tasake dawowa ɗauke da kayam abinci,godiyah nayi mata na ɗawainiyha damu kafin tah fita a ɗakin.
Kallon hajara nayi wadda samu bakin gado tah zauna tana ɗan riƙe ciki.
"Ciwo cikin yakeyi ne"
Batayi magana ba sai jijjiga kai da tayi,nima bansake tambayarta ba nayi hanyar banɗaki domin ganin menene babu,saidai da mamakina naga komai yana inda yake gashi na zamani,dan ma allah ya taimakeni nasan yanda ake amfani da banɗakin zamani da hakan sai yaban wuyah.
Ruwan mai ɗan zafi na haɗa mata a bahon wanka,wajen cin abine dai saida aka kai ruwa rana tukunna.
Muna cikin hakanne kuwa blessing ta sake dawowa,ɗauke da magani inji hajiyah maryam na masu ciki,dayake itama cikinne da itha kuma bai girma sosai,dan zayyi wata ɗayah dana hajaran.
Ina bata maganin kuwa tah fara baccin farin ciki wanda rabonta dashi har tah manta ma.
Kwanan mu uku a gidan kafin hajiyah maryam ta nemi ganina a falon baƙi.
Gaisheta nayi tah amsa batareda dogon jawabi ba tah shaidamin cewar aikina shine bayin fulawa safe da yamma da kuma kula dasu akai akai.
Mamaki abin yabani jin ɗan karamin aikin da zanyi kuma aka bani muhalli da kuma albashi ga uwa uba abinci mai rai da lafiyah,dan kwanan mu uku har mun murmure daga ni har hajara,wanda yanzu tah koma kaman ba itab saboda. Magananin da ta ke sha da kuma samun abinci mai gina jiki.
"Nasan zakayi mamakin ganin karamin aikin dana baka,amma bakomai bane dama nayi niyyar taimaka maka,kuma bai kamata mutane masu amana da rike mutuncin alƙawari su ƙare ba,kayimin abinda bazan mantaba nima,inshaallahu dama ina da niyyar buɗe shago toh zan baka ka riƙemin nan gaba,amma a halin yanzu wannna shine kaɗai hanyar dazan tsimaka maka"
Farin cikine haɗi da jin daɗi suka kamani har na rasama da wanne irin baki zan gode mata irin kyautar da tyimin haka.
Itama ganin na diriricene yasakata saurin barin falon tana murmushi,da alamun bata son godiyar tawa kenan.
Nikuwa hakan bai wuceba dan dana koma ma na faɗawa hajara tun kafin na rufe baki tace zatayi mata godiyah tsakanin itah da itah.
Chapter 3 · 0% Book details