← Book details Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 41

Sashe 33

Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Hannu ta dagamin alamar na zo,cikin sanda na kaman wanda kwai ya fashemin a ciki na isa wajenta na durkusa.
Hannuna ta kama dukka biyun kafin tace,
"Duk da bansan wane hali kike cikiba amma nasan abin akwai wahala,saidai ina so ki sani duk da halin dakike ciki kar ki bari wuya ko kuma wani yanayi ya hana ki kusanci zuwa ga ubangijinki,tabbas nasan akwai abinda yah faru a daren dana badake ga ummanki hajara,amma nakasa koda abinda nayi lokacin barekuma mai ya faru,abinda nasani kawai shine idan nayi kokarin tuna mai yah faru nakan ji duk kaina ya juye ina kokarin fita daga cikin hayyacina,bansna mai ya faruba kwata kwata,har shikansa Abdulwahab bansan mai ya faru dashiba.
Sameemah muna cikin jarabawa dagani harke amma karki yanke kanki daga neman sauki a wajen allah ko kuma neman agajinsa,a duk inda kika samu kanki ki kasance mai mika lamarinki ga allah,a cikin dad'i harma da cikin wahala"
Wani irin rauni nakeji zuciyata tanayi lokacin da nake sauraron abinda yake fitowa daga bakinta,hawayen danaga yana zuba a cikin idonta ne yasani rungumeta a jikina kaman kar mu rabu.
"Nagode ummee inshaallah zanyi kokarin yin amfani da abinda kika fada min"
"Kici gaba da addu'a komai zaizo da sauki watarana sai labari inshaallah"
Daga haka tacigaba da yin lazimi ina zaune a gefenta,zaman wajen kadai tayarmin da hankali yakeyi amma haka dole na daure saboda naga farincikin a kan fuskarta.
Ranar na biyar da zuwana gidanne da rana ina kwance a kan gado naji ana kiran sallah,abinda ummee ta fadaminne yadawo min cikin kaina,saidai duk da haka ban taba gwada yin sallahr ba koda wasa,kenan ban dauki maganarta da kima ba koh,kuma ban kasance Y'a tagariba,bar batun wannan ya tsakanina da mahaliccina to,wanda shiya halicceni amma kuma nakasa bautamasa tsawon shekara da shekaru saboda bin umarnin wasu shedanu can,yanzu idan na mutu mai zancewa ubangijina,shin hujjar danake da ita na sun hanani yin ibada nikuma ban yi wani kokariba ta isa kareni daga ranar karshe??.
Wani saurin tashi nayi daga kan gadon hawaye na zuba a cikin idona,yayinda jikina yake rawa kaman an jonamin spring,tabbas akwai kalubale a gabana ba kadanba.
Hangar vandakin na nufa,duk da baraxanar bugawa da zuciyata takeyi amma haka nayi biris da ita na fara alwalar,yau na dauki alwashin gwada yaki da duk abinda yake cikin jikina.
Fitowa nayi na dauki hijabi a kan gadon ummee wanda take sallah dashi na saka,kafin na shimfida sallaya.
Tun daga hawa sallayar nakejin kaman nadora kafa akan wani abu mai zafi,amma haka na jure ina runtse ido.
Kabbara na tayar wanda ina ga ban tabsyin guda uku ba tsawon rayuwata,abinda yasa ban mantaba saboda anayinta a masallatai ne kullum.
Suratul maryam bakina yakama nafara karantawa,daga iyah aya biyu na yanke nayi ruku'u,ina jin kaina yana barazanar fashewa amma ban fasa abinda nakeyi ba,lokacin danakai sujjadane naji wata murya tansmin magana cewa,
~~Hakika kin Kaimu bango a yau,kina tunanin zamu sallamar da ruhin da anriga an yi mana kyautarsa,to hakan bazai yiyuba,daga yau zamu kasance mune zamu tinga control din gangar jikinki har zuwa nan da wata uku lokacin da zamu mallakeki ki rike matsayin dayake jiranki,idan kuma ba haka ba dole mu hallakar dake,yanzu ma dolene ki karbi hukunci~~
An gama fadar hakan naji wani zafi da kuma kara ya ratsa cikin kaina,hakanne yasa nima na zunduma tawa karar danima bazan iya zure azabarba.

💎*Sameer a madubin gani*💎
Chapter 33 · 0% Book details