← Book details Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 41

Sashe 22

Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*

💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}

💎27~28💎

Hakanne yasa na cika da bakinciki har na fara miki fada,banida niyyar sakaki cikin kadaici sameemah duk abinda yah faru yah fi karfina ne sannan ina baki hakuri akan rashin fahimatar dake tun daga farko"
Duk da bana kallonta amma nasan maganganuna suna shiga cikin kunnenta,samun waje ta samu ta zauna a bakin gado,yayinda nima na bita na zauna a gefen ta tareda jawota zuwa cikin jikina sanann na cigaba da maganar danake yi.
"Bazan tursasaki ki yarda da abinda nake fadaba,saidai ko wata rana zaki iyah bincike akan hakan,ki yafemin da barki cikin wannan halin,bazan gazaba waj en baki hakuri a koyaus Koyaushe ,idan bazaki damuba inaso naji mai yah faru dake har kikabar gida sannan a ina kika tsinci kanki"

💎*Sameemah a madubin gani*💎

Shiru mukayi daga ni harshi,ina jin yadda zafin jikinmu yana gauraya zuwa guda d'aya,
Wani irin yanayi nakeji yana shiga cikin jikina wanda na ji a duk lokacin da farouq ya matso kusa dani,duk da banason yanayin saboda yanda yake saka zuciyata yin rauni a lokaci da ya,amma kuma bazanyi karyaba yana sakawa najini kaman ina raye nima kaman sauran mutane,duk da cewa zuciyata bugawa take saboda ina tsoron kar na cutar dasu acikin kowanne irin lokaci.
Musamman danaji dalilin tafiyar yah sameer daga gida sai na tsinici kaina da son kai saboda kullum tawa matsalar nake gani ba matsalar wasu ba,hakan yasa nake kara ganin laifin mutane fiyeda abinda sukayimin.
Dago da fuskata nayi ina kallon fuskarsa wanda yasake matse jikina acikin nasa kaman zai maidani cikin nasa.
Haka kawai bansan mai nene yasami shiga cikin kaina ba na tsinci kaina da bashi labarin yanda nayi kokarin tafiyah birni aiki da yanda yan fashi suka taremu na cececi sauran yaran ta hanyar mika kaina garesu har zuwa yanda nayi rayuwata a kasar palastine da kuma kasar Brazil. Abu daya na boyemasa shine yanayi halittata da kuma dafin dayake kwance a cikin jikina harda kuma shaidanun danake magana dasu.
Wanda kuma nayi hakanne saboda lafiyarsa,dannasan idan suka tabbatar yasani to zasuyi kokarin hallakar dashine wanda hakan shine abinda har karshen rayuwata bazan yafewa kainaba.
Dora habar sa yayi akaina kafin yace,
"Kiyi hakuri da rayuwa sameemah hakika munga jarabawa kuma muna kan gani,saidai ko kusa ban fada rayuwar da kika shigaba,ke jarumace nasake fada ke jarumace sameemah,wanda ko cikin maza ba kowane zai jure abinda kika jureba,saidai ina fatan wahalar rayuwa yah tsaya miki iya haka,sannan kuma yah baki ikon karbar hakan a matsayin kaddararki,ina fatan nacigaba da zama dam uwa a gareki mai sharemiki kuka,sannan ina saka ran kasancewa miji nagari agareki idan kin bani damar hakan,sannan kuma uban y'ay'anki"
Gabana ne yah buga rigifff,saboda nasan abinda yake hasashe ba abune mai yiwuwa ba koda kuwa mun so hakan a tsakaninmu,yau daya a rayuwata naji babu dad'i kasancewata daban da irin rayuwar mutane,saidai cikin sauri na katse tunanin hakan daga cikin raina tareda cire jikina daga na yah sameer ta hanyar matsawa gefe.
Shima dayaga hakan light kiss yayimin a kumatu tareda da cewa "saida safe"

💎*salma a madubin gani*💎
Chapter 22 · 0% Book details