Sashe 37
Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Yanzu zaman mu da ummaruje babu yabo babu fallasa,an cire masa karfen dake kunkumin sa yanzu yana tafiya da kansa,ba said da wheelchair ba,saidai har yanzu wani abun sai a hankali tunda dama ba sona yake da farkoba duk da yanzu naga zuciyarsa tana karkatowa wajena.
Hajiyah mairo ma ta daina abinda take,dan idan na tura umaruje muka je falonnata hira har sai mukai sha dayan dare,wani lokacin harda salma ake idan jinyar cikinta ya daga mata.
Dan ba karamin wahala take sha ba,koyaushe cikin zuwa asibiti akeyi,wani lokacin ma hajiya mairo ce take kaita idan alhaji bayanan,yanzu ba karamin tausayinta takeji ba,dan dui mai guntun imani idan ya ganta zai tausaya mata matuka.
Ranar da umaruje ya fara tafiya har yar walima hajiya mairo da hada saboda murna da farinciki.
Gaskiya kam munyi murna sosai ganin cigaban da ake samu,musamman ma shikansa uban gayyar,yagaji da zaman gidan ba wajen zuwa,a ranar ne kuma alhaji bala yabashi takardar aikin daya sama masa wanda zai fara zuwa wani satin.
A zaune muke da daddare ina gyara kaya shikuma yana kan gado,hankalina ya tafi wani daban ban kulaba said jin hannunsa nayi a bayana,juyawa nayi ina kallon idanuwansa wanda suke dauke da yanayi kala Kala.
"Kiyafemin abinda nayimiki sameerah,tabbas ba shedar mutum daga farkonsa ko kuma daga waje said na zauna dashi,sannan baka gane mai sonka sai ka shiga wani hali,nikaina shaidane akan son dakikemin sameerah,fatana allah yabani iko nima na soki na baki farinciki kaman yanda kika sadaukar da farincikinki domin zama dani duk da kinsan bazan baki abinda kowane miji yake bawa matarsa ba na d'a"
Saurin saka hannuna nayi a bakin sa tareda cewa,
"Wayace naka baka bani farincikiba ,kaine ka bani farinciki tunda har ka yarda na zauna tareda kai,duk da kana da damar nesantani da inda kake,ba abinda nake bukata daya wuce muyi rayuwar farinciki kaman yanda kowane ma'aurata sukeyi,y'ay'a bayarwace ta allah ba akanmu aka fara hana haihwa ba kuma ba a kanmu za'a kareba"
Runugmeni yayi kaman zai maidani cikinsa yayinda nima nayi yanda yayi din.
Hayaniya mukaji a sashen su salma hakan yasa nasaka hijabina akan kayan baccina muka fito nida umaruje.
Hajiyah mairo ce rike da salma alhaji bala kuma yana binsu a baya.
Asibiti muka nufa inda akayi dakin haihuwa da ita da sauri.
Muna nan zaune har akayi sallah gari ya waye amma babu alamar sauki a lamarin,sai ihunta damuke ji kawai da nishi.
Zuwa rana su inna karima sunzo harda inna larai,dukkanmu kowa jikinsa yayi sanyi ganin halin da take ciki.
Ganin ana shirin kwana biyu amma babu alamar haihwar ne yasa likita ya nemi alhaji bala yasaka hannu ayi mata aiki kawai.
Hakan kuwa akayi muna gani aka wuce da ita dakin tiyatar ko motsin kirki batayi sosai,fargaba bazata fassaruba a wajenmu kowa yayi kozai kozai.
Muna nan zaune nurse ta fito da yarinya a hannunta an nannadeta a towel,katuwa da ita cikin koshin lafiya.
Karbarta nayi da sauri saboda nice a bakin kofar,kallon yarinyar nake wanda take kama da umaruje sak,mamakin hakan nayi saidai dana tuna kaman alhaji bala suke sai koma tunanin wani abu daban na ya halin da uwar y'ar kuma take ciki. Tun kafin nayi magana nurse din tace,
"Wacece sameerah,mai haihwar tana nemanki keda mijinta da kuma mahifiyarta"
Da sauri nabi bayan nurse din gabana yana bugawq saidai bansan mai yake faruwa ba.
A kwance take akan gado da kayan marasa lafiya a jikinta,karisawa wajenta nayi ina rike hannunta,murmushi tayimin na dauriya kafin tace,
"Anty sameerah kinga yarki dana haifamiki koh?,ban taba tunanin a duniya zaki kasance yaya a gareni mai son farincikina ba saida na samu kaina a inda ke kadai nake da ita,ina alfahari dake,to nasan Y'a ta ma idan yakasance tana karkashin kulawarki bazaki bari wani ya lahanta rayuwarta ba sai inda karfinki ya kare,dan haka ni salma nabaki Y'a ta dana haifa halak malak kece mahaifiyarta ban yadda ta nemi wata uwaba bayan ke.ki yafemin abinda nayi miki sannan ki taimaka wajen nema min gafara a wake duk wanda na zalunta"
Kuka nake son yi ko kuma zuciyata ce takeson tsayawa na kasa tantancewa,mai salma take nufi ai wasiyya takemin yamzu haka,ina kallom sanda ta daga kanta tana kallom mijinta da kuma mahaifiyarta wanda suma sun so daurewa amma sun kasa yin hakan.
Kai na narike wanda yake barazanar fashewa saidai babu yanda zamuyi muna kallon sanda numfashi na karshe ya fita daga cikin huhun salma,ta mutu kenan ta bar duniyar kamar bata taba wanzuwa a cikinta,saidai hotunan ta dakuma tunanin ta acikin zukatan mutanen da tayi rayuwa dasu.
Hannunta data rikeni ne ya shika yayi samyi kalau kaman ba nata ba.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun
Kullu nafsin za ikatul maut
Haka Muka fito daga dakin da take kwance babu mai cewa wani abu a cikinmu.
Gawar muka karba muka nufin gidan mijinta domin ayi mata sutura a can,kowa ka gani mutuwar ta bugeshi ba kadan ba ,musamamn mu da muke zaune da ita.
Ina runtime da yarinyr a kirjina ,duk duniya ji nake babu wanda zaizo yarabani da ita,idan kuwa yace dole sai yayi hakan to saidai yafara ta kaina tukunna.
Kwananmu uku muna karbar makoki amma sameemah bata zoba,iya yah sameer ne ya taho da kuma anty saleemah,sai wata mata itama mai kama da sameemah,nan ake bada labarin mahaifiyarta ce kuma kanwar mamar antu saleemah,har ma da rashin lafiyar da sameemah takeyi na bata gane komai,ni dama banyi mamaki ba dan ni kaina shaida ce sameemah ba ita daya bace,dan haka fatan samun sauki mukayi mata.
Abinda mukafi girgiza dashi shine ashe mahaifinta ne sanadi kuma tash wahala tun tana yarinya na kokarin boyewa da kuma halayyar da takeyi dan ta nesanta yan uwanta daga garets,hakika ta bani tausayi matuka,ashe duk abinda muke cikin duhun kai,bamuyi amfani da lokacinmu da muke tareda ta hanyar da ta daceba ,mun cutar da kanmu mun kasa fahimtar matsalarmu har saida mukayi nesa da juna lokacij babu wanda yake gani kowa kafin muka fahimci kuskuren da muka tabka na asarar lokaci.
Tare muke kwana da zainab wanda itama d'anta yayi wayo sosai,dayake suna jigawa wajen aikin mijinta sai sanda suka zo tukunna.da kuma anty saleema sai jinjira salma wanda aka maida mata sunan mahaifiyarta, duk kukan takemin bana gani sai ma kuka danake sakawa,sainaga kaman mahifiyata take nema,saida su zainab suka nusar dsni akan dole na jajirce daure damamrar zama uwa ta gari ,sanann na runtse ido na hukuntata idan batayi dadai ba nan gaba,ta hakane kawai zan yi mata tarbiyya sabanin yanda akayi mana.
Saida akayi sadakar bakwai kafin kowa ya watse ya barmu dagamu sai mu,ni kuwa nacigaba da rainon little salma dan ba a boyemata sunaba.
Shikansa umaruje yana zon yarinyar a ransa,dama jininsa ce yanzu kuma zai reneta tamkar yar sa..........
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎
*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*
💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}
💎45~46💎
💎*sameer a madubin gani*💎