← Book details Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 41

Sashe 30

Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Firgicine ya cikani da tunanin kar ya kashemin yah sameer shikenan,saidai dana daga idona sainaga razanar da take kan idon sameer bata halin ciwo bace,da alamun ni yake kallo.
Inda yake kallon nima na bi da nawa idon,sai a lokacin naga ashe kan kirjina bullet din ya Saita na dama.
Mayar da kallona nayi kansa cikin ajiyar zuciya ganin a kaina abin ya sauka,saidai hakan dayayi yah nuna baya son nayi masa afuwar kenan.
Zefar da bindigar hannunsa yayi yana zagayani yana cewa,
"Well well ki sumar min da yara kina tunanin zan barki haka,da alamun dai soja yaje yah auro mai kamar maza,ga shikuma ita mutuwar tsaye take yi,gaskiya ta cika sojan"
Lokacin daya gama juyawar ya dawo dabana ne na damki wuyansa ina murmushi kafin nace,
"Ba suman tsaye ba dai fakon tsaye nakeyi,da alamun kaine zakayi mutuwar tsayen,"
Har nayi niyyar kafa masa hakorina sai kuma na matsar da bakina,amma duk da haka dai na yakeshi da farcena akan wuyansa,danaga jini ya fito da alamun farcena ya garwaya da jininsa sai kawai na wanka masa mari shima yah fadi.
Duk abinda ya faru akan idon sameer wanda shikadaine kawai bai suma ba a falon,farouq na dauka da zuhra a kafadata nayi dakina da sauri jin karar shigowar sojoji,da alamun karar bindigar ne yajawo hankalin su.
Bansan ya aka kareba ina jin dai sanda aka suka shigo suna ta magana,nikuma na kwantar da zuhra kenan,sameer ne ya shigo cikin dakinnawa da sauri muna kallon juna,karisowa yayi har inda nake ya kama kafaduna tareda yage rigar wajen da mutumin yah harbeni,wajen ya koma ya hade amma ba sosai ba saboda bullet din yana ciki,dole saina nutsu kafin na cire.
"Miye hakan yake nufi iyee,yakamata kizo mu tafi asibiti"
"Ahah niba asibitin da zanje kuma ina rokonka karka fadawa kowa ni aka harba,hakan ba komai zai haifarba sai matsala na rokeka"
"Yanzu kina nufin nayi shiru kenan duk da abinda nagani?,shikuma wannan ciwon ki kwana dashi a haka,kuma kina tunanin sai nayi yanda kikace"
"Ciwona ba matsala bace zuwa gobema bazaka ganshi ba amma idan ka fadamusu abin bazai tsaya iyah gobeba,mutumin daya harbeni kuwa ku barshi yah tafi kawai ,da kansa ma zai mutu nan da kwana uku,idan kuma baka yadda ba ka biyoni bandaki ka gani"
Babu yanda na iya haka na jashi badakin domin nuna masa hujja,saboda nasan taurin kansa zai iya zuwa yah fada,dan haka na kwammaci shikadai yasan ya nake da duk mutanen barrack dinnan su sani.
Almakashi na dakko na saka a wajen ciwon yana kallo na burkulo bullet din kafin na saka hannuna na fitar dashi na ajiye,ina gama fitarwa na ajiyeshi a sink din da ruwa yake fita.
Wajen kuwa kaman jira yake yafara hadewa da kansa.
Dakko bullet din nayi daya wanke da ruwa tasss na mikawa sameer tareda cewa,
"Nasan zasu bukaci ganin bullet din koda kuwa kacemusu a jikin bango yake,dan haka gashi,yanzu ka gane mai nake nufi,idan kacemusu a jikina yake zasuce ina ciwon yake sannan a wane asibitin nake,toh banida wannan amsar shiyasa na bukaci kayi shiru please"
Hannunsa yakai inda na cire bullet din yana dannawa maimakon ya karbi bullet din a Hannun a DA nake mika masa,
"Har yanzu bazaki fadamin komai akan abinda yake damunkiba duk da wanda idona yaganemin,saima kokarin rufe bakina da kikeyi,ina kallon yanda idonki yasanja kala,sanann kuma kinyi kokarin cizonsa a wuyah sai kuma kika fasa kika yankeshi da farce mai hakan yake nufi?"
"Nayi niyyar zuke jininsane amma kuma Akwai dalilin dayasa na fasa kawai na saka masa guba a cikin jininsa kawai,duk da haka kuma banason ka tambayeni mai yah faru dan bazan iyah fadamaka ba,sannan kuma ka dunga nesan kanka daga gareni tunda kaga illar danake dashi ga rayuwarka,komai dazai fito daga jikina hatsarine yayi gauraya da jikin mutum har ma da sauran halittu,please kadunga yin nesa dani sameer idan kana so ka rayu ko domin yayanka ma"
Daga haka na barshi a bandakin na dawo dakin bayan na damka masa bullet din a hannunsa,shima fitowa yayi yah fice ya bar dakin zuwa waje.
Da safe danaje dakin saleemah bacci na sameta tanayi haikan.
Kwantar da zuhrah nayi a gefenta naje wajen kayanta domin na saka mata,tunda banida kayanta a wajena kaman farouq.
Ina cikin saka mata wando saleemah ta tashi,kalonmu take dason tunowa mai ya faru,daga gani ta tuna abinda yah faru daren jiyan daga yanda ta razana,karisowa wajen danake tayi da sauri ta dauki zuhra ta kankame a jikinta,nima ganin hakanne yasa na juya domin fita daga dakin.
Can kasan makoshinta tace,"nagode sosai ta kulamin da y'ay'a na da kikeyi"
"Basai kin him in godiya ba hakkina nne nima na kare iyalina indai ina da damar hakan,allah ya tsare gaba"
"Ameen ya Allah "
Daga haka nabar dakin na nufi nawa domin shirya farouq zuwa makaranta,saidai yanda jikinsa yake rawane yasa na cire masa kayan inyaso gobe sai yaje idan hankalinsa yadawo jikinsa.
Zaman gidanne ya isheni saboda yanzu na saba da zuwa aiki,saidai gidan dole yana bukatar mai dan lafiya,saboda saleemah tana daki yini tayi jikinta yana rawa,ga zazzabin da takeyi kumadu.
Can wajen rana ina kitchen sameer ya shigo da alama har sannan a wajen caae din suke,kitchen din yah shi go tareda kama hannuna yana kallon farcena,nima kallon sa nake da alamar mai ya faru,saida yagama kallon dan kansa kafin yah dago ya kalli idanuwana.
"Menene a jikin farcenki sameemah,jiya da daddare ina kallon lokacin da kika yanki mutuminnan a wuyansa,yanzu muna masa bincike mukaji yana ihu amma ba na horon da muke masaba sai dan abinda yake wuyansa. Mun kaishi wajen likitoci sun ce cell din cikin jijiyoyinsa ne suke mutuwa a kowanne bayan sakanni,wajen yayi baki kuma tafiya yake yama mamaye dukkan ilahirin jikinsa"
Sunkuyar da kaina nayi dan bansan mai zance masa ba,gashi nasan idan ba fada masa nayi ba zai barni ba.
"Nima bans an mai yake damuna ba haka na tashi na ganni,ummah ma tasani kafin ta rasu ita ce ta nunamin yanda zan boye halittata daga idon mutane ,duk abinda ya cijeni ko kuma ni na cijeshi ko kuma wani bangare na jikina yah shafi cikin jininsa to zai rasa ransa,sannnan duk ciwon danaji baya minti daya yake warkewa"
Zare ido sameer yayi shikadai yana nazarin wani abu wanda banida masaniya akai,dan murmushi nayi kafin nace,
"Yah sameer kana tsoro kar na halaka ku ko,wannan abin shikadai nake gudu a rayuwata sannna shine abinda yakasance tamkar bakar razana a gareni wanda nake kwana kuma nake tashi da shi.ko yaushe tunanina shine taya zan nesanta masoyana daga sharrina,a kokarin hakan dole sai na zamo Wacce suka fi tsana saboda munanan halinta,ta hakane kawai zasu kauracemin koh ban umarcesu da hakan ba. Burina shine kayi nesa dani yah sameer abinda kake tunanin bazai taba yiyuwa,bazan iya soyayya dakai ba mu yi rayuwar aure har mu haifi yara. Haka nake kuma bazan iya sanja hakanba koda ina da ra'ayin hakan,saidai ina so kasani bazan iya cutar da ahalinka ba koda inada bukatar hakan,akan haka na kwammaci na kasance cikin azabtarwarsu ko kuma su daukeni daga rayuwarnan kaman yamda suke da bukata"
Hawayene yake zuba daga idanuwana wanda kwannan nakasa gane kaina,abu kadan sai nayi kuka inda ina gaban yah sameer sai naji ina rauni. Abinda banyi tsammani bane ya faru,wato rumgumeni ya sameer yayi sosai a jikinsa kaman zai maidani cikinsa,nima hannuna na saka a bayansa na jagayeshi a jikinnawa kaman wata zata kwacemin shi.
Cigaba nayi da kukana a hankali ina jin yar nutsuwa tana shiga cikin zuciyata,shidin haskene a gareni da banaso nayi nesa dashi sai dai haakan ya zamemin dole.
Cikin muryar damuwa yacemin,
"Suwaye suke da niyyar daukeki daga gareni sameemah,kin kasa bani wannan amsar meysa haka?"
"Bazan iya baka amsar ba koda ina da bukata nima kayi hakuri"
Cireni yayi daga jikinsa zai share hawayen dayake fuskata,saurin rike hannunsa nayi danaga ciwo a hannun wanda mutanen suka ji masa,jijjiga kai nayi ,
"Ahah karka kai hannunka fuskata ,duk da ban taba gwadawa ba ina tsoron hawayena yayi maka illah yah sameer,bazan iya yafewa kaina hakanba idan ya faru"
Murmushin ya fahimta yayi min kafin yace,
"Yanzu kenan idan kikaji ciwo komawa yake ya dinke da kansa? "
Murmushi nayi masa kafin na dauki wukar na yanka a tafin hannuna,har yakai hannunsa zai rike sai kuma wajen ya koma yanda yake tamkar ban yanka ba.
Daga haka muka cigaba da hira ,duk da kowa zukatansu a cunkune yake da zullumi iri iri amma hakan bai hana mun turasu kasan zuciyoyinmu ba mun rungumi kaddara.
Chapter 30 · 0% Book details