Sashe 26
Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Duk maganar dake fita daga bakinta ban saka su cikin madubin fahimta ba saida naga lagababbben jikinta yayi kaca kaca da jini akan kirjina,babu abinda nake maimaitawa a cikin raian sai innalillahi wa innna ilaihi rajiun,dan na rasa mai zanyi,babu abinda kwakwalwata take haskomin sai kokarin rasata da nakeyi bayan nayi kuma rashin ummah ta a baya.
Mika hannuna dayake rawa nayi na dauki waya ta,da kyar ma na samo number dake farkon call log dina na danna kira,saleemah ce ta daga tareda cewa lafiyay?.
Cikin magana a rarrabe nacemata,
"Salee......mah ddddakina.... Samee. ....mah ce"
Da sauri ta kashe wayar ta shigo dakin,yamda muke zaune ta rankwafo akan kirjina haka saleemah ta samemu ko motsawa na kasa yi.
Jinin da taga yana zuba a bakin sameemah ne ya razana hakan yasa ta koma da sauri dakinta ta dauko waya tareda danna number doctor maryam.
Ina nan zaune har suka shigo suka dagata daga jikina ita da doctor maryam din zuwa cikin mota.
Bayan sun tafi da wasu mintuna ne na tashi na bi bayansu,ko tunanin sanja kayan dake jikina banyiba,burina kawai bai wuce naga halin da take cikiba.
Tun daga bakin kofar shiga wajen doctor maryam ta kama hannuna ta zaunar dani tareda yin magana cikin kwanciyar hankali.
"Ahah bai kamata kashiga a haka na hakanma da wannan daren sameer,matarka tana da rai yanzu hakama mun saka mata karin ruwa saboda anyi sa'a jininta bai kai a kara mata ba,saidai akwai bukatar ta ringa cin abinci mai saka kujari.
Yanzu kai kuma kaje ka cire kayannan kasaka wasu in san samune ma sai gobe ka dawo,domin zamu kulada ita sosai.
Haka badan nasoba na juyo da baya zuwa gida amma hankalina gabadaya yana kan sameemah da kuma wane hali take ciki.
Haka na kwana banyi bacci ba ina kai kukana ga allah,da safe kuwa tun kafin garin ya waye sosai kama hanyar asibitin.
Murmushi doctor maryam tayi data ganni a wannan lokacin.
Dakin da sameemah take kwance ta rakani,a kwance take tana kallon silin kamar mai tunani,lokaci daya tausayinta ne yakamanni lokaci guda ,abin tashin hankain ma shine bansan mai yake damunta ba.
Karisawa inda take kwance nayi a hankali kaman mai sanda,juyo da idanuwanta tayi kana ta saukesu a kaina,kara mayar dasu tayi zuwa inda take kallon tun farko kafin shigowata dakin.
Hannu nakai zan rike nata wanda baya dauke da karin ruwan a jikinsa,amma sai tayi saurin janye hannun tanamun gargadi da idonta akan kar na tabata,banyi yunkurin sake tabata a karo na biyuba saima tambayar ta danayi yha jikinta.
Motsa baki kawai tayi kaman zatace wani abu amma batace komai ba.
Doctor maryam ce ta shigo dakim da tire a hannunta,ajiyewa tayi a gefen tiren tana cewa,
"Patient a ta shi a ci abinci ko tunda jiki yayi sauki"
Dago da idonta tayi ta zubasu a cikin na doctor maryam din,wanda hakan yasa ta dan ja da baya tana karewa sameemah kallo kaman mai nazarin wani abu,can kuma ko mai ta tuna sai kawai ta kawar da tunanin tareda mika hannun ta domim taimaka mata ta tashi.
Hannun doctor maryam din ta kama ta tashi,maimakon ta saki hannun sai ta,rikeshi gam kaman wani yana son kwance hannun doctor maryama din daga nata.
Matsawa kusada ita nayi domin rikota amma sai ta matsa jikin doctor maryam kaman zata koma cikinta,magana tayi cikin dashshshiyar murya irinta marar lafiyah.
"Yah sameer bawai ina gudunka bane amma dan allah ka bani lokaci tukunna matsowarka kusadani akwai matsala a halin yanzu"
Ina jin hakan na daga mata kai alamar na fahimta saidai hakan bai yimin dadiba ,itama ta fahimci hakan sannan nasan kaman yanda nake bukatar ta a kusadami koyaushe nasan itama tanajin hakan.
Alama doctor maryam tayimin akan na bata lokacin.
Cire karin ruwan dayake hannunta tayi kafin ta jata zuwa bandaki domim ta gyara bakinta,basu dadeba suka fito har sannan sameemah tana jikinta kamar wata karamar yarinya,abinne yaban mamaki domin nasan halin sameemah sarai,bata nuna ita yarinya ce sai a gaban ummah kadai,tunda ta rasu kuwa tafison komai tayi da kanta basai an taimaka mata ba.
Abincin ta saka a plate ta fara bata tana ci har taci da dan yawa,komawa tayi ta kwanta kaman yanda take a farko.
Fita doctor maryam tayi sannan tayimim alamar na biyota zuwa office dinta.
Muna fita wata nurse kuma taje domin kula da itah. Saida ta zauna akan kujerarta kafin ta nuna min waje akan na zauna.
Min dan samu sakanni a haka kafin ta fara yimin magana.
"Hakikanin gaskiya sameer bamuga komai ba gameda abinda yake damu matarka,da farko nayi mata gwajin ciwon zuciya amma sai na samu kalau babu wata matsala,sannan abin mamakin shine yanayin yanda ta zubda jini bakai ace ma zata iya rayuwa ba amma kuma da muka gwada sai mukaga jininta normal ne bayyi wani low sosaiba.
Komadai menene yasameta yanzu komai normal ne babu abinda yake damunta saidai dan gajiya kawai da tayi amma babu wata matsala,zuwa nan da yamma zamu iya sallmar ta.
Godiya nayi mata bisa kokarin da tayimana kafin na koma wajen sameemah,dan yau kam babu batun aiki.
Nursing din data ga shigowa ta fita tayi ta bamu waje nikuma na zauna akan kujerar da ta tashi din.
Banyi zaton zatayi magana ba amma kuma sai na ji tace,
"Yah sameer kayi hakuri da abinda yah faru sannan ina mai baka hakuri a gameda halina,saidai alfarma guda daya zan nema a wajenka ita ce dan allah karka tambayeni abinda yake damuna"
"Shikenan zan yi kokarin yin hakan tunda shine burinki amma ki sani badan nasoba zanyi kuma bazanyi miki karya ba hakan zai dameni matuka"
💎*sameerah a madubin gani*💎