← Book details Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 41

Sashe 19

Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fitar da tunanin nayi a raina na wuce dakina damin nima nayi nawa shirin.
Kayan sunyimin kyau sosai a raina naji dadi sosai,ganin nasake samun wani aikin a karo na biyu.
Lokacin dan isa wajen da masu training din suke duk ansaka su cikin sahu na layi.
Dama daga gani suna jiran isowata ne dan idon su duk akaina lokacin da major nazeer yah ke gabatar dani,shima ina kallon dan alamun girmamawa dayake min,wannan al'adar sojane nuna girma ga wanda yafika matsayi.
Babu Bata lokaci muka fara abinda yah taramu wanda muka aiwatar dashi a wani fili na koyon harbin,dukkansu kowa ka ganshi yayi laushi kaman an yimasa duka,saboda aiki dani ba sassauci,kallon mugunta nayi musu kafin nace kadan ma kuka gani indai nice mai koya muku abu.
Direct wajen masu koyon tracking da hacking na wuce bayan na gama da masu harbin,zasuje wani ma yah cigaba daga inda na tsaya .
Sai wajen la'asar sukam muka tashi,domin aikin dana basu ba karami bane,kuma da gangan nayi musu hakan dan su san ba wasa ne yah kawosu ba.
Ina is a gida na hada gumi shirkiff ,wanka nayi nasaka kananan kaya kafin dare kuma yayi nafara nasu blacky dan zuwa yanzu suma sunyiwa sauran karnukan barrack zaryah tun daga yanzu suna kanana,dan jikinsu haryah fara murdewa irin na karnukan manyan yan daba.
Idan muka gama training kuma na barsu a jije su kwana suna maimaici,wanda bayyi ba kuma yakarbi hukunci mai tsanani,sannan bana barsu su saba da kowane mutum,daga ni sai yaseer,sannan abinci su koyaushe nama ne saidai a sarrafashi tah hanya daban yanda zai kara karfafa jikinsu.
Fitowa nayi daga dakin na wuce kitchen na hado custard,dan bana bukatar abinci a lokacin,farouq ne yah ganni kasan cewar babu islamiya yau yana gida,mikamin kofi yayi yana min kallon dolly irinna yara idan suna son abu,karba nayi na zuba masa dam ba lallai na shanye shiba.
Komawa falon mukayi muna kallo,wanda ni hankalina ma baya kai saboda duk cartoon ne,sai anyi abune yake taboni ya nuna min,ko banganeba to nake cemasa kawai.
Muna nan zaune har aka kira magriba,kallonsa nayi nace,
"Farouq tashi ka tafi masallaci an kira sallah maza"
Cuna baki yayi bayason zuwa,amma yana kallon fuskata yah tashi da gudu yah fita zuwa masallacin.
Jijjiga kaina nayi kawai bayan na kashe kallon,dan idan ban kasheba yazo yah gani bazai je lessons din dare ba yau. Kuruciyah da daɗi.
Lokacin daya shigo gidan dakina ya shigo da gudu har yana tuntube,kallonsa nayi da takaici,badama baya son zama waje daya kullum cikin rigima yake.
"Yanzu farouq bazaka tafi a hankaliba kaman ana binka a baya?"
"Aunty yi hakuri,dama sauri nake karki tafi wajen su blacky kibarni tunda kince yau kam zanje koh?"
Shiru kawai nayi ina tunani,kusantuwa ta da yaron kullum kara yin gaba yake,ina tsoron kar hakan yajawo matsala idan iyayensa suka dawo.
Sai nayi niyyar yimasa fada sosai ko nesan tashi daga saikuma na kasa,saboda kama da yakemin da sameer haka ummah tah,sannan bayan wannan inajin yaron a cikin jikina sosai.
Dan sunkuyawa nayi na kama kafadunsa kafin nace,
"Suna cizo sosai sannan kaga dare yayi ka bari gobe sai muje da yamma idan ka dawo daga makaranta koh"
Daga kai yayi alamar yah amince,sai kuma yayi murmushi,gyara masa gadon nayi yah kwanta bayan na bashi chocolate din dare,duk dan kar yah biyoni,dan nanny dinnasa wani lokacin ba gidan take kwana ba tana wajen mazan sojoji,kuma wai ita suka bawa tarbiyyar yaronsu,dan sati guda kenan bata gidan.
Zuwa yayi yah fadamin akan yana tsoron kwana shikadai kullum,wanda nima na kula da hakan.
Tun daga lokacin na dawo da duk kayansa zuwa dakinnawa,shima dayaga hakan murna yayi tayi,ko yaushe sai yah shiga yah fita,wai yah zama dan dakina.
Tun daga lokacin idan na tashi nayi abin karyawa sai na tasheshi na shiryashi nima na shiryah,idan muka gama komai saina fito na kulle gidan shikuma na kaishi wajen mai kaishi makaranta.
Idan ya dawo kuma sai yaje inda nake bada horo mutaho gidan tare,idan nayi mana abinci muka ci,saina shiryashi cikin kayan islamiyyah bayan yayi sallah,duk da bana takurashi amma yah sani idan yah yi ba daidaiba ina horashi yanda yakamata,dan banason sakalci ko kiyuwa ko kuma raini ga wanda suka fishi.
Shi ma daya ga haka yana kokarin kiyayewa,koda ya manta yayi da sauri yake bada hakuri idan yah tuno mai zai biyo baya.
Yanzu nakan barshi yaje wajen su blacky shikadai bayan na tabbatar sun dan saba dashi bazasu cutar dashi ba,dan karnukan sun sanja kama zuwa wani abu mai hatsari ga duk wanda yah gansu,saboda zaman cikin jeji da kuma bada horo mai tsanani.
*****
Zuwa yanzu nasamu wata guda uku kennan da karbar matsayin mai bada horo a cikin bori camp dake cikin porthacourt barrack.
Na sauya abubuwa da dama a cikin haron daliban,ciki harda kara tsawon lokacin yin train,sannan banda wasa ko shiririta,yanzu na zamo kusan duk taro da za'ayi a cikin wajen toh sai an turomin takardar gayyata,wani nakanje wani kuma nace bazanjeba,dan haka suke hakuri dani,bana nuna respect ga kowa,dan wannan dabi'ar ita kadai na rasa a cikin aikin sojan,wato respect ga na gaba dasu.
Watarana ne ina zaune major nazeer yah kirani,nayi mamaki daya nunamin wani office an kawatashi wai nawane,sun bani alhakin kulada horon sabin sojoji,sanann kuma ga kudi da,suka bani mai yawa,wanda kuma zasu cigaba da biyana wata wata,kallon office din nake har da motar da take bakin wajen mai paint din sojoji,kuma wai tawa ce.
Biki akayimin na hakan ,wasu manyan sojojin daga wasu jahar ma saida suka hallara,musamman dasuka ga irin aikin danayi da kuma sabon salon horo dana kawowa barrack din.
Gaskiya nayi mamakin abinda sukayimin ban zata zai kai har haka ba,sai ganina nayi na daukaka lokaci guda an bani matsayin mai bada horo da kuma saka hannu cikin tsaron wajen,zan iya gyara duk abinda naga dama a kuma lokacin danake so.
Yanzu daliban dana yaye a cikin wata hudu gwarazan da suke cikin su sune suke gudanar da wasu ayyukan,ni yanzu banida time sosai,koyaushe ina office.
Farouq ne yah shigo office din da sauri yana narai narai da ido,kallonsa nayi naga har hawaye yakeyi.
"Menene yah faru ka dawo da wuri haka"
"Ba .....ba cikina ne yake ciwo ba"
"Wani Abu kaci ko,bayan na hanaka"
"Ahah anty"
Ajiye aikinnayi na kira yaseer ya karisa dan yanzu shine mataimakina,kuma nina bukaci hakan,mahaifiyarsa takanas tazo tayimin godiya.
Daukarsa nayi dannaga harda sakalci yau yake ji daga gani.
Gida muke je na ajiyeshi a bakin gado,bandaki na shig na hada masa ruwan wanka,lokacin dana fito har yah cire kayan makarantar,koh magana banyimasa ba yah shige bandakin,dan zuwa yanzu babu abinda bai saniba na dokokina basai na fada da bakiba.
Fita nayi na hada masa abinci. Kallonsa nayi lokacin daya fito daga dakin sanye da gajeren wando irinna sojoji da kuma farar T-shirt.
Mika masa abincin nayi,yana karba yace,
"Nagode ummah"
Saurin kallonsa nayi jin sunan daya kirani dashi,daga haka bai sake cewa komaiba har muka gama cin abincin yah fita zuwa gidan major nazeer wasa,dan tanada son yara.
Har sannan kalmar mommy bata daina yawo a cikin kaina ba.
A satinne na kira meeting kan cewar bai dace ace an saka kaso na sojoji a bakin wani gida kawai dan tsaro ba,sannan kuma kamata yayi ace sojoji guda biyu a kowanne gida,shima kuma za'a dunga sanjawa wasu su tafi training wasu kuma suje wajen iyalansu.
Cikin saurin bukatata ta karbu dan hakan shine yah fi,a kofar gidanmu kam,duk sallamar su nayi nasaka iyah guda biyu da rana,idan dare kuma yah yi su blacky ne suke tsaron bakin kofar,ko kafi uwarka kokari baka isa ka wuceba sai sun baka dama,shima sai na yadda tukunna,ta hanyar ganin hotonka a camera kofar gidan,idan na yadda zan kunna green idan ban yadda ba sai na danna red,toh dole ka juya badan kanaso ba.

Tun daga wannan lokacin farouq yakoma kirana da mommy,dan a cewarsa yanzu babu wanda yake kuladashi saini,nima banyi kokarin hanashiba dan yanzu yaron ya shiga raina sosai.
Washagari da safe aka bada sananrwar dawowar general musa daga jinyar yarsa daya tafi yi a kasar Germany,hmm abin ma ba tsari ko kadan,tun wata biyu da zuwansu ta warke amma tace baza ta dawoba sai anyi mata aikin fata an cire duk tabon zanen bulalar dayake jikinta,wannan ne ya daukesu har tsawon wata hudu acan.
Nikuwa naji labarin dawowar tasu amma babu abinda nayi a ciki,tashi nayi kamar kullum na shirya farouq zuwa makaranta,nima na fita nawa aikin,a hanya duk sojoji sai sara min sukeyi,dayake yawancin dalibaina ne dana yaye wata uku da suka wuce,sannan su san bana wasa sanann bana mugunta ko zaluntar wani,da haka na kankaro mutuncina a wajensu.
Yau ban tashi da wuri ba,dan farouq ma daya dawo daga makarantar safe anan na bashi abinci yaci yah kawanta,sai la'asar tukunna na sabashi a wuyana zuwa gidannamu.
Dan zuwa lokacin nasan su yah sameer sun dawo,kuma da gangan na ki dawowa da wuri duk da nasan tahowar wajen azahar zasuyi.

💎*sameer a madubin gani*💎
Chapter 19 · 0% Book details