← Book details Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 41

Sashe 17

Wasa Farin Girki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina Shiga ban Bata lokaci ba na saita bindigata a kan ogannasu wanda yake zaune a bakin gado yah rude fuskarsa da wani bakin kyalle,kallonsu nayi ina cewa,
"Koh Ku dauke bindigarku daga kan yarannan ko kuma yamzu ku debi kwakwalwarsa a kasa"
Har sunyi niyyar ajiye bindigarsu naji yah buge bindigar dake hannuna da karfi yah rike wuyana tareda manna ni da bangon dakin dayake kusanmu,matsewar dayayimin nasan da ni mutumce kaman saura da idan ban mutuba toh zan shiga coma,
"Ke yar gida uban waye da namiji bazai iyah tunkara ta ba bare ke figyagygyiya dake?"
Muryarsa kadai ta isa ta bawa mutum tsoro yanda take fidda amo,murmushi nayi masa kafin nace,
"niba yar uban kowa bace saboda ba da matsayin uban kowa nake taka rawata ba,sannan babu mai sakani koh hanani sai na ga dama"
Nima nasa wuyan narike kaman yanda na rike nawa,wani yunkuri nayi muka juyah yazamo shine a jikin bangon ina rike da wuyansa sabanin da shine yake rike da nawa wuyan.
Kakarin amai yake yanda na rike masa maƙogaro a hannuna gam,kallon idonsa nake wanda yayi ja saboda rikona,
"Yanzu waye figyagygye tsakanin ni dakai,*bar raina allura karfece*"
Saida na tabbatar yayi laushi kafin na jefar dashi a tsakar dakin,kallon wanda suka dora bindiga akan yaran nayi amma sai suka kara manna bindigar jikinsu yah fara karkarwa,barazana suke min amma ban fasa isa inda sukeba,har saida dayah yah fara nuna ni da bindigar,banyi tunanin zai harba ba amma saijin karar shigar bullet nayi a kafada ta ta hagun.
Karar iskar shigarsa ce tasa na fada can gefe sannna na bugu da gado,gsnin hakanne yasa ogan yayi saurin tashi yana rike da makogaransa suka fice da sauri tareda sauran yarannsa,matarce tayi saurin matsowa kusadani amma na dakatar da itah,tareda cewa,
"Ki dauke yaranki tukunna,sune suke da bukatarki bani ba a halin yanzu"
Tashi nayi na fita daga dakin ina rike da inda aka harbenin,saidai ina fita waje na jefar da bullet din nayi hanyar gidanmu.
Shikuwa dama major nazeer tun sanda suka fita ya bi bayansu da guda lokacin da ya dauki bindigar dana shiga da itah.
Ina Shiga Gidan ban same KO inaba sai dakin sameer,dayake dama akwai key din kowanne daki a jikin na kofar shiga gidan ,wanda aka bawa kows idan ya dawo gida zai shiga.
Kunna wutar dakim nayi kafin na bude drawer kayansa,cikin sa'a kuwa na samu abinda nake nema wato kayan aikinsa,dauka nayi nasaka cikin sauri sauri,duba gefen kayannayi na dauko bindgarsa ita ma a wajen kayan amma a kasansu.
Gyara zaman bullet dinnayi,harda Murmushina danajita a cike da bullet gata kuma dama favorite ɗina kenan.
Kallon kaina nayi a madubinsa nayi murmushi danna fito sak raudah abdulsalma dina,saiya tuna min abu dayawa.
Fitowa nayi ina rataye da bindigar har haraba headquarter,anan na samu su major nazeer suna ta magana,tsitt sukayi dasuka ganni na iso wajen,musamman yanda nake tafiya kaman mamallakin kayan,tun kafin major nazeer yayi magana nace,
"Mai ake baza'abi bayansu ba har yanzu karfe hudu na asuba yah kusa"
Wani ne daga cikin sojojin yace,
"Eh wato ranki yadade ogah ne yace bazaiyiyu a bisu yanzuba saboda ba'asan mai suke dauke dashiba"
"Dole sai an bisu kuma yanzunnan,natsani naga mata suna tsoro bare maza,saboda shi iyalansa sunanan kalau ko?,na wasu ko oho,yamzu za'a bi bayansu kuma babu dawowa sai an karbo matan dasuka dauka,su basu ji tsoron zuwa daukar abinka ba sai kaine zakaji kunyar zuwa karbo naka abin"
Ina gama fadan hakan na nemi a kirawomin hackers da kuma tracker,suma zuwa sukayi gaba,hadasu nayi a mota dayah nikuma na shiga tsakiyarsu,saboda akwai wani abu danakeson yi a game da wanda suka tafin,shima major nazeer dayaga mun shiga mota mun fara tafiya sai yah hau mota suka biyimu a baya.
Wani abu na hada a system din da sauri sai ga hoton inda za'a saka yatsu yah fito.
Nawa hannun na dora sannan nayi search dinsa a area inda muka tafiya,cikin sa'a kuwa saiga hoton yatsan yah fito wanda yake wuyan shugabannasu a area wajen.
Kara gudu mukayi su major nazeer suna bin mu a baya har muka fita daga ainihin cikin mutane,wani jeji muka shiga inda hoton yake nunawa,har muka,zo inda mota bazata wuceba dole saidai mu tsaya a mushiga da kafa.
Ana zuwa wajen major nazeer yah daga hannu akan nida wanda suke tracking mu tsayah a wajen,harda ajiye mana soja guda dayah yah kulada mu,tunda nake na dade banyi dariyah ba sai a wannan lokacin,tashi daya kuma na murtuke fuska.kallona yake cike da mamaki ganin a halin da ake ciki hakan ma ina mace amma kuma bai girgijani ba.
Gyara zaman bindigar sameer nayi a hannuna kafin na wuce gaba,har shidin ma na barshi a baya na fara kutsawa cikin jejin,har yah bude baki zayyi magana nayi masa alama da yatsana akan yayi shiru kawai ya biyoni,bai yi musuba yah biyoni a baya tareda sauran sojojin, muna tafiyah muna duba inda zanen hannuna yake har muka zo bakin wani gida wanda akayi shi da ya jingar ciyawa.
A Hankali muka cigaba da sanda har muka iso bakin kofar gidan.
Wasu nayiwa alama da hannuna akan su zagaya,wasu kuma su saita taryar wanda zai fito,wasu kuma su yi shirin afakawa,a masu afakawar harda ni da kuma major nazeer,ina kallonsa yana min kallon mamaki ganin yanda nake bada umarni cikin kwarewa.
Kirga numbobi mukayi zuwa biyar kafin muka shiga da sauri.
Wayam muka gani babu kowa da alamun ansan da zuwammu.
Kara naji tana tahowar makami hakan yasa nayi saurin jan su major nazeer muka fadi a kasa,kifiyoyin kuma suka wuce a iska,kallona yake da taya akayi na sani,saidai ba lokacin tambaya bane yanzu,alamar karar mutane naji wanda idan an rufe bakin mutum take fita,nuna musu nayi tareda cewa,
"A can hanyar suke kuma ba a cikim gidannan bane saidai babu damar mu tashi tsaye saidai muyi rarrafe"
Basuyumim musuba haka muka fara rarrafawa har muka fita ta wata kofa a cikin gidan,wani jejin ne yayimana salamma irin na farko,kafin mu mike daga rarrafen muka ji karar wani abu a kawunan mu giffff,ina kallon sanda suka suma nima sai nayi suman karya domin na samu damar yin plan.
Suna ganin mun suma suka fara fitowa daga inda suke boye,ina kallon su ta gefen ido har suka kaimu wani waje inda sauran yara da matan suke.
Suna fita na bude idona, tashi nayi hannuna a daure har na isa wajen wata mace,wanda da alama tafi sauran jarumta dan ita bata kuka kaman yanda sukeyi,sunkuyawa nayi har zuwa inda igiyar dake hannunta take,wata karamar reza na fitar daga bakina na fara yanke igiyar a hankali har na yi nasarar hakan,tana ganin na kunceta ta daga hannun tana kallo,suma sauram mutanen kallon suke da mamaki.
Juya mata baya nayi da niyyar ta kwance min,cikin sauri hannunta yana rawa ta gama ciremin kafin tafara cirewa sauran mutanen da suke wajen,
Nikuwa ban dauki bindiga ba wani kulke na dauka mai fadi na nufi wajen da barayin suke.
Duk wanda muka hadu dashi saina saita murfin keyarsa nake sauke masa har muka zo inda ogan yake kwance a kan gadon kara an nannaɗe masa kai inda na bugashi a gidan major nazeer.
Kallonsa nake shima ni yake kallo da alama yagane ni,jefar da kulkennayi wanda yayi ja saboda jinin dayake jikinsa,tsalle nayi na hau kansa tareda kafa masa hakorana a wuyansa,saida na dade kafin na daga.
Murya na fara ji a cikim kaina ana shewa tareda cewa saura daya takk.
Kwata kwata na manta sai a sannnan na tuna saurana kaiwa biyu na kasance ɗaya daga cikinsu,kuma konaso zama da mutane a lokacin bazan iyaba,nadama ce ta zomin dan yanzu nasan control din danke kokarin yi zayyimin wuyah a yanzu dan a kowanne lokaci dada zama hatsari nake ga mutanen da suke kewaye dani.
Ina cikin tunaninne naji sautin tafiyar mutane,saurin goge bakina nayi tareda ture gawar mutumin daga kan gadon dan kar aga hoton hakorana a kan wuyansa.
Motocin da muka zo dasu har da na barayin muka hau domin komawa gida,kowa sai murna yake,nidai jinsu nake kawai dan na auka cikin kogon tunanin wannan juyayyar rayuwartawa.
Har muka isa na wuce gida babu wanda nakula a cikin masu yimin magana da tambayoyi dan bata su nakeba a lokacin.
Burina nayi wanka na kwanta sannan kuma nayi tunanin a wane mataki nake na rsyuwa a kusa da mutane.
Washagari da safe ko nace da hantsi dan sannan na nayi wanka na karyah saiga yaseer ya kawomin kwikwiyon da reza ta haifa,bakakene wuluk babu fari a jiknsu kuma gasu bulbul sunyi wayo,godiyah nayi masa na karbesu na kaisu garden inda iyayensu suke tun farko,dama bingone shikuwa yanzu ba zama yaje ba tunda yake zuwa wajen karen sojoji.
Chapter 17 · 0% Book details