← Book details Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 40

Sashe 4

Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahuta Dan gata ne gaba da baya irin sangartattun yaran yan siyasa Wanda babu kwaba babu tsangwama kusan duk abunda yakeyi wurin babanshi ya gada barewa bazatai gudu danta yayi rarrafe ba baban shi babban mazinaci ne hakan yasa shima ya haifi magaji a zina babu abunda basu mallaka maiba najin dadin Rayuwa dukda baban nashi yana samun labarin ta'asar da yaronsa keyi jefi jefi amma bai damu ba ganin hakan shine wayewa, mahuta bakaramin manemin mata bane kuma Dan kwaya domin baya kananan shaye shaye har cocaine sha yakeyi.

*Mr's Sadik Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Yah Allah ka zaunar mana da kasarmu lfy👏🏻kaduna people how market?🤣ya gajiyar zaman gida? Wannan doka mun gaji da ita😭 ya Allah ka dauwamar mana da kwanciyar hankali a kasar mu👏🏻.*

*Dedicated to sister Husnah*

8

ko lekawa dakin su meenah da suketa ramokon bcci batayi ba dayan dakin tasa makulli tabude ta shiga kassncewar two bedroom flat ne sai katotan parlor a tsakiya tareda toilet Uku, kowane daki da toilet sai daya a parlon ko'ina tsaf tsaf gwanin ban Sha'awa yasha furniture's ba laifi gidan baida wani hayaniya, dakinda yake mallakinta ta shiga saboda babu mai shigar mata nan take sauke mahuta da sauran samarin ta yayinda dayan dakin kuma mallakin su meenah ne.
Cire kayan jikinta tayi batabar komai ba saidan pant da bra ta bararraje tafara sharara munshari.

Kiran sallar asuba neya farkar da Zainab duk nauyin bccin da takeyi tohfa ana fara kiran farko cikin ikon Allah saita tashi, nan ta Mike tayi salla tana zaune a wurin tana lazumi har gari yafara haske sannan tashiga bayi tayi wanka, kwalin plaster dinda ke garkame akan madubin dakin ta bude tareda daukan guda biyu, ta manna daya a goshin ta daya sace amma yabar karamin ciwo, daya kuma a gefen bakinta ta manna, blue material Mara nauyi ta dauko wacce akai mata simple dinkin doguwar Riga ba hayaniya simple make-up tayi tareda feshe jikinta da turare nan tafito Ras abunta dinkin ya amshe ta sosai dukda Zainab masha Allah kamar yanda AK yace she fat for back she fat for front tohfa haka yake a cike take taf tareda taimakon shafaffen cikinta dake tona asirin kyawun halittarta ya kwanta ya lafe kamar ba hanji a ciki, irin dogayan matan nanan ne amma ba fara bace bakuma baka sidik ba black beauty ce skin dinta mai tsada tanada kyau mai tsayawa a rai hmmmm *'nasan zakuso kuji wacece Zainab ku cigaba da kasancewa da Yar mutan katsinawa*

Saida ta kyara ko'ina na cikin gidan dukda girman gidan amma yauda gobe tasaba bata wani ganin wahalar hakan kasancewar tun Dare ta wanke kwanukan da akai Amfani dasu tareda goge kitchen din, hakan yasa turaren wuta kawai tasa ko'ina yadau kamshi masha Allah, ragowar ferfesun jiya ta dumama tareda Juyewa a cooler sai sandwich datayi tareda dafa ruwan tea Wanda Yaji kayan kamshi kan dinning ta jera komai da komai cikin rawan jiki tafito makeken harabar gidan nasu wurin jerun motocin AK ta nufa guda Uku masu kyau, 'dattijon mai gadin gidan nasu ne ya matso wurinta tana hango shi ta gaishe shi nan ya Amsa mata cikeda fara'a da mamakin ranarda zata daina wankema AK motoci kusan shekara Uku Abu yakici yaki cinyewa ba karamin tausaya mata yakeyi ba hakan yasa har Addu'a yake mata Allah yakawo mata karshe wahala wurin uban gidan nashi, a iya sanin shi baitaba jin AK ya dagama wani murya ba kokuma ya zagi wani sai matarshi hakan yasa yake cikeda zumudin San jin tarihin rayuwar su dukansu idan da Hali, sanin babu halin shiyasa ya hakura yaja kafarshi tareda komawa bakin aikinsa, 'motocin ta shiga wankewa sauri sauri gudun fitowar shi, hakan yasa tagama dawuri ta wanke su duka tas tareda gogesu ciki da waje a gajiye take lis ko wankin motocin wani katon aiki ne sanin ko kura yagani cikin motar tohfa ta shiga Uku, tana gamawa ta dauki abun gyaran flowers ta nufi flowers dinda ke zagaye da gidan nasu, dukda ada akwai masu aikin gyaran flowers din harda mai wanke mai motan tun farkon Auran suya sallame su duka a cewarsa kudinsa ya huta an kawo mishi jakar mai Aiki, cike da sabo da kwarewa tashiga gyarawa tagama komai nan ta hau sharar tsakar gidan nasu dakyar ta gama saboda girman gidan, shiganta cikin gidan yayi daidai da fitowar shi daga dakin shi sanye da dakakken suite milk color yasha necktie black da zanan milk ya tsuke fuskar nan a murtuke dukda haka yayi matukar yin kyau gawani bakin gashi daya zagaye fuskar nashi hakan yakara fito da madarar kyan shi, dogon Namiji ne fari tas Tubarkallah masha Allah, shagala tayi da kallon Sa kaunarsa na Kara ruruwa a ruhinta ji take kamar tayi tsalle ta makalkale shi, ganin batada niyyar daina kallon nashi yasa shi watsa mata Wata shegiyar harara a cewarshi kada ta shafa mai bad luck da sanyin safiya, russunawa tayi tana gaishe shi, 'ina kwana ka tashi lafiya? Kamar kullum wuceta yayi kamar tana magana da dutse kallon dining yayi yaga ta jera abinci kotakan abincin baibi ba, dama baci yakeyi ba sai ranarda tayi matukar Sa'a idan kuma batayi ba wani sabon tashin hankali ne, duk Randa tayi gigin mai tayin abinci kuwa a jikinta yake Juyewa duk zafin shi.
Tanajin fitar shi gidan a gurguje tashiga daki Kara gyara jikinta tayi tareda chanza kaya duk sun takura ta, ta matse cikin kananan kaya gajeran wando jins blue da farar vest, masha Allah ita kanta tasan Allah ya kawata surar ta, shiyasa ta dinga fuskantar matsaloli ada saboda hakan kan dining ta nufa nanta kwasa girkin ta yayinda ta koshi daki ta koma ta zumbula dogon hijab sauran abincin ta juye awani cooler Wanda yake mallakin mai gadi ne, mika mai tayi tadawo tareda kunna TV takamo Arewa24 kwantawa tayi akan doguwar kujera tanata kallo har wurin 11 taji tsamin jikinta ya dame ta baya mata dadi ko kadan, tashar ta chanza aikuwa ta kama Wata tashar wakan turawa sai karkada jiki sukeyi, nan danan ta Mike wai itama zata gwada kozata danji karfi karfi a jikin nata idanta jijjiga jinin jikin ta dukda maganin datasha a banza, rawan ta shigayi tana botsarewa sai bankare bankare takeyi tana juya cikin ta kamar yanda taga sunayi , tayi Akalla kusan minti 10 cikin nishadin data dade batayi ba ganin takoma saikace yarinya yar shekara sha Tara, karan Abu taji hakan yasa ta waigo da sauri abun mamaki AK tagani tsaye kamar gunki ya sankare yana Kare mata kallo ko kyaftawa bayayi baki a bude aikuwa a 360 tabar wurin tareda garkama makulli a dakin nata, wayarshi daya Saki ya kalla a kasa domin tunda tafara rawan ya shigo da niyyar Amsa waya haryasa a kunne yanaji ana mai magana cikin wayar amma yakasa tabuka komai............yanzu abun Aisha harya kaiga haka? Tuno wani littafin sanin sirrin mata daya taba karantawa idan bai manta ba malamin cewa yayi duk macen datake yawan mika ko bankarewa toh tana cikin tsananin bukatar Namiji, *Innalillahi wa inna ilaihir raji'un* ya furta cikin sanyin jiki.

*Shin wakesan yasan labarin ma'auratan nan masu ban Al'ajabi?* duk maiso ya daga hannu💁🏻‍♀

*Mrs Sadik Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

7

Bakaramin San halima mahuta keyi ba inda ya kudira a Ranshi idan lokacin auren shi yayi zai iya Rayuwa da ita dukda yakai munzulin auren amma a cewarshi bayaso ya tsufa abunda ya lura Aure na saurin tsufar da mutum tun bare idan yafara Tara yara gara nanda kamar shekara 45 ya daure yayi, suko iyayan shi ko'a kwalar rigar su Dan suma American style sukeyi basa takura ma yaro a cewar su rayuwar shice yanada yancin yin komai, duk cikin bebs dinshi bai hada leemah da kowa ba a cewarshi saboda tana nishadantar dashi yanda ya kamata, kullum jinta yakeyi zamzam ko kadan bata sakaci da maganin mata hakan yasa yake mata duk abunda takeso gudun kada ta naima a waje abunda baisani ba Yammata irin halima basuda Alkawarin rike saurayi daya tunda zata iyama iyayanta basaja shi awa? yanda cikin takun ta take kula Gayu sosai tareda basu kanta jinta takeyi bazata taba Rayuwa da namiji guda daya a rayuwar taba saboda karfin Sha'awar da takeda shi hakan yasa kullum saita samu mai debe mata kewa inda take abunta cikin kwarewa tareda taimakon maganin Hana daukar ciki, tunda tataba yin ciki kusan sau biyu dakyar tasha inda a lokacin Mamarta keta zuzuta yanda tayi haske dakara cika aiko nan ta sanarda mahuta sukaje asibiti aka burge shi bakaramin wahala tasha ba hakan yasa aka daure mata bakin mahaifa, dayake Allah ba'a mai wayau saiga wani Alamar cikin a jikinta a lokacin su meenah ne suka farga cikeda tashin hankali suka koma Asibiti Ashe mahaifar budewa tayi ba karamin wahala tasha ba inda har jinya saida tayi a gida amma ankasa ganewa mama tadage da dafa mata huntu da ararrabi a cewarsu shawara ce taimata mugun kamu hakan yasa duk Wata saitaje an duba lafiyarta a Asibiti saboda ba kowani maganin planning ke amsarta ba shiyasa yakara cika ta dam dam harta fara losing shape ba tareda ta farga ba.
Halima tana cikin jerin mata masu matsaikacin tsawo itaba gajera ba bakuma doguwa ba, tanada haske farace amma ba Sol dinnan ba dirin jikinta ma babu laifi saidai batada cikar kirji sannan basuyi Kanana sosai ba, yar madaidaiciya yayinda hancin ta Dan daidai yadan bude kadan baiyi tsini sosai ba saidan karamin bakin ta tareda ido masu Dan girma, baza'a kirata mummuna ba tanada kyau mai sanyi, tareda zubin halitta mai kyau saidai kan nan nata ne toh masha Allah kamar kwallon goriba😕a takaice dai irin gashin sister Husnah gareta🤣🤭 amma tareda taimakon karin gashi wanda dorawa kawai takeyi akai bata yarda aimata kitson shi saboda tsaro shima tana gama abunda zatayi take tunbuke shi saidai kan nata dukda bawani gashi a tsaftace yake zaka ganshi Ras da kitso maiban Sha'awa kwarjinin ta shike Sa manyan Gayu ke mutukar kaunarta duk kankantar ka indai zaka zube mata kudi toh babu abunda zai hanata budema kafa a takaice dai *The definition of halima is fake*
Chapter 4 · 0% Book details