← Book details Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 40

Sashe 34

Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A' Asibiti kuwa Ansamu Malam liman da mama sun farfado amma an rikesu a cewar likitoci sai sunyi kwana biyu saboda tabbatar da lafiyar su Wanda Malam din bai damu ba ko kadan baisan dawani ido zai kalla jama'a ba, taya zaifara? Taya? Tabbas yasan hakan na cikin jarabawar shi dukda ganganci da sakaci irin nashi dasai yanzu yake ganin gudunmawar da suka bada wurin bata tarbiyyan diyarsu nan yaita kuka yana neman gafarar ubangiji Wanda ya jarabceshi ya nuna masa duk tarin ilimin shi ba shine zai Hana Allah jarabtar bawansa ta inda bai zato ba, nan ya kudiri Aniyar idan komai ya daidaita zai karbi halima da hannu biyu baya cikin iyayan dake gudun kuskuran su zai Amsa kuskuransa da hannu biyu tareda kulada cikin jikinta har Allah ya sauke ta lfy koda kuwa jama'ar gari zasu koreshi akan yana rainon cikin shege duk zaginda za'ai mishi zai toshe kunnan Sa barna ce anriga an tafka hannun ka baya rubewa ka yanke, inda labari yagama bin gari duk inda ka waiga maganar diyar Malam akeyi karya da Gskia haka mutane keta ruruta lamarin har kasashan ya'da labarai saida akasa domin yazama iznah ga iyaye Wanda wasu da biyu sukeyin hakan domin tozarta malamin masu zagi da takaicin leemah nayi, masu ganin ganganci da Laifin su Malam nayi, harda masu Allah Kara, nidai nace kanku akeji.

Ta fannin mahuta kuwa Lauyoyin Dadyn shine suka bashi shawarar janye karar da yake shirin makawa kotu ganin duk yanda ake daukan lamarin tohfa ya wuce nan, Ranka shi Dade wannan ba maganar kudi akeyi ko matsayi ba duk abunda akace akwai idon mutane a ciki gaba daya Al'ummah sun karkata akan case dinnan kasancewar ta diyar babban Malami a ganina fa barin sha'riar nan itace hanya mafi sauki kada Allura ta tono garma babu abunda mutane ke jira illah iyaka Susan Wanda yaima halima ciki ya kake ganin za'ai idan muka fito da kanmu tareda tona kanmu har a'kasan Dan gidan babban dan'siyasan da yayi suna shine ya banka ma diyar babban Malami ciki ya kake ganin makomar siyasar ka? Goge zufa daddy yayi dukda baiso hakan ba amma Yaji dadin Sha'awar nan Allah yaso shi dayayi tabargaza garin neman gira arasa ido hakanan yanaji yana gani aka rufe case din Inda sukayi luf sukayi shiru suna kallon yanda Abun zai kasance.

Mahuta kuwa tuni aka saka mishi hakorin Roba a wawulan bakin shi inda ya kudiri aniyar nanda wani lokaci zaibar kasar domin haduwa da manya manyan likitoci asan yanda za'ai dashi bazai yiwu babban guy kamarshi ba Dan kudi yakarasa Kuruciya babu hakori a bakinsa ba, yawa ne indai kudi na aiki tohfa komai yazo da sauki tuni yakoma kan network inda ya hada duka kawayan leemah meenah da feenah ya ajiyesu gida na musamman babu ko kunya aka dasa daga inda aka tsaya a cewarsa Gari dayawa maye bazai taba cin kansa Sa Ga mata jaga jaga wasu ma koda kudinka saida rabon ka, sukuwa ko kishin kansu basayi tunda rufin asiri suke nema kuma mahuta ya sake musu kudi wani Kishin namijin bariki zasuyi Wanda baida tabbas?

AK ne zaune a parlor sai safa da marwa yakeyi misalin karfe goma na Dare Wanda tuni Aisha tadade da Danna ma dakinta sakata, sai sake sake yakeyi yarasa abunyi, dakin limah yashiga nan yafara jido akwatinan lefenta daya hada mata kaf saida ya hadasu akwati dozin da manyan jaka guda biyu, dukda ta dinka wasu bai damu ba, akwatin dankunne yabude tareda Addu'ar Allah yasa gold dinda yasa mata a lefe yananan, aikuwa yana dubawa saiga dankunne da sarka da zoben gold nan yaita kinkimar kayan yana jerasu tsakiyar parlon dakyar ya karasa dukya gaji, kai tsaye dakin Aisha ya nufa yaita buga mata kofa sanin bazai taba dainawa ba harsai ta fito yasata bude kofar fuska a hade sanye da Riga da wando masu taushi blue color sunyi kyau sosai sai kamshi takeyi tana yamutsa fuska, "yadai? Bcci nakeyi lafiya ka tasoni cikin daran nan? My Aeesha magana zamuyi ki sameni a parlor, yafadi tareda Kare mata kallo yakoma parlon, kai tsaye ta bishi kanta babu Dan kwali tsayawa tayi trus tana mamakin uban hadaddun sababbin akwatin da suka cika parlon nasu kallonta yayi, " zauna mana sarautar mata, yayinda yake nuna mata kusada shi, kan hannun kujera tadan zauna nesa dashi yayinda ta kalle shi tareda kauda ido, ehm ina jinka tafadi Alamar kosawa, "Aiishaa, yafadi in a husky voice, duk kayanda ke nan wurin ki kwasa na mallaka miki idan akwai abunda bai miki ba kibada idan akwai abunda kike bukata ki gayamun, kallon kayan tashiga yi daya bayan daya cikin Al'ajabi da mamakin jin furucin shi cikin tsohon daran nan wannan kyautar dukta mecece? Shin maiya kamata tayi? Ta Amsa kokuwa? Mai zatayi da uban kaya haka?, "ya mai karatu kuba Aisha shawara shin ta Amsa kyautar da AK yaimata kokuwa??

Gogan kuwa Rokan Allah yakeyi yabashi Hanyarda zai lallashi Eeashar Sa, " Shin wazai ba AK shawarar yanda zai lallashi uwargida?.

Ina jiran comments dinku domin samarma ma'auratan mafita ku taimaka ma AK da kalaman Soyyah kunsan fa sai a hankali ta fannin Soyyah a play class yake👯🏼‍♀💃🏽
Eh:- "Kodai yace yake mintin zuciyata na tuba ki yafemun idan bake ba sai lahira🤣😜

*Mr's Saddiq Rumah*💅🏻
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to Sister Husnah.*

39
Chapter 34 · 0% Book details