← Book details Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 40

Sashe 18

Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ranar da daddare suna waya da halima bai nuna mana komai ba, cikin dabara tasako zancen, 'Kasan menene?
A'a saikin fadi yabata Amsa, wlh Wata kawata ce wani Saurayin ta yaimata ciki abun mamaki ankusa bikin ta, 'tohfa yafadi shikuma Wanda zata Aura yasani? Yabata Amsa cikin jimami, 'hmmmm mu muka bata shawara akan ta gaya mishi idan zai iya Auranta a haka aikuwa yace ba matsala shi ita yakeso ba jikinta ba amma a zubar da cikin, aikuwa ana zubarwa ya Aure ta kuma xo kaga yanda yake Santa baitaba goranta mata ba.
'Gskia ya matukar burgeni lallai ya cika namijin gaske haka akeso ba karamin lada zai samu ba, 'Allah masoyi na? Ta Tambaye shi cikin zumudi, 'wlh kuwa, 'kai zaka iya mun haka?? 'Kwarai mai zai Hana? Tsakanina da Allah nake sanki a ba jikin kiba zan iya mana babu abunda zai hanani Auranki, ",ka tabbata tafadi har tana yar'dariyar murna, 'kwarai kuwa kina shakka ne??
" hmmmmm a'a nasan kana matukar sona, "eh wlh babu abunda bazan iya miki ba insha Allah.
"Aikuwa nimafa an taba, 'aka taba mai😳? Ya bata Amsa.
'Wlh wani yataba mun fyade munje bikin kawar mu wurin dinner ya yaudare ni har yaimun ciki😭😭

'Ciki? Amma wasa kikeyi koh? Cikin tashin hankali ya furta hakan, 'wlh wlh da gaske nakema.
'Karki damu nariga nasan komai ai tun kafun ince zan Aure ki nasan koke wacece amma ke nakeso, nan yafara gaya mata wasu daga cikin sirrin ta Wanda mahuta ya gaya masa, nan taita mamaki bata iya karyata shiba aiko nanta bude baki taita bashi labarin Abubuwan dabai Sani ba cikin ikon Allah kamar wacce aka matsa ma baki, inda taimasa karya akan sau goma kawai muhuta yasanta a mace, 'kanshi kasa daukar zancen yayi nan yace mata zai kwanta yanajin bcci duk yanda yaso ya nuna mata babu komai kasawa yayi kashe wayar shi yayi tareda tausayin Rayuwar mu ayau, shin wacece macen Auran? Haka Zamani ya Zama? Da Addini suke fakewa suna ta'asa a doran kasa? Halima tagama rikita shi nan danan tausayin Malam liman ya rufe shi dattijon Arziki.

*A' gurguje.*

Shiru kwana biyu babu Ahamad ba dalilin shi Kota kirashi baya dagawa inda dakyar tasamu ya Amsa wayarta nanta fashe mishi da kuka akan yadaina naimanta, 'maganar gskia bazan taba Auran mazinaciya bari muyi gwari gwari niba Dan iska bane babu wani boye boye kin bani mamaki bazan Auri mai fuska biyu ba kije ki aura mazinaci daidai ke Allah ya shirya ki yasa kigane ni kaina ba wayo na ko karfi na bane ya kubutar dani daga auranki illah Addu'ar da nakeyi da wacce iyaye kemun sai Ince Alhmdlh, 'babu irin magiya da Rokon dabata masa ba Sam yaki yarda ya shafama idonsa toka, 'Dan girman Allah ko Auran Dare daya muyi ko baka taba niba ka rufamin Asiri ka aureni koda baka sona, ko bakai mun komai ba, 'saboda me? Ya tambaye cikeda mamaki, "saboda in goge bakin fentin Dana kwasa zan biyaka konawa ne insha Allah ko Auran kwana daya ko biyu ne na yarda, 'kai tsaye ya gaya mata bazai iyaba.

" halima taci kuka badan tana San Ahmad ba saidan Auran shi rufin asirin tane mutane zasu shaida tataba Aure daga baya saita aura mijin da takeso mai kudin gaske inda zata huta ta kece Raini koya jita a bude ba matsala tunda yasan bazawara ya Aura, ko banda wannan ma kasuwar zaurawa tafi budewa manyan mutane sunfi San harka da bazawara sannan Abu na Uku dayasa takeso tayi Aure saboda ta tabbata Malam liman sai yamata Aure kwanan nan amma idan tazama bazawara zai sakar mata mara ta tsula tsiya a cewarsu tayi Aure tafito batayi dacen gidan miji ba jama'ar gari babu Wanda zai zarge tada wani Abu.

*Note:- labarin rayuwar halima Wanda nake badawa a yanzu wlh wlh yafaru da gaske babu abunda na rage bare in Kara*

*Mrs Saddiq Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Godiya ta musamman Ga masoyan littafin nan Wanda na Sani dama Wanda ban Sani ba, da bazarku nake taka rawa masoyana na Facebook dukda ban sanku ba ina gaisuwa.🙏🏼*

*Dedicated to sister Husnah*

23

Babu yanda halima batayi ba Sam Ahmad bayako sauraran ta daga karshe ya tura iyayan shi amso kayan Auran da akakai gidan su, ba karamin tashin hankali iyayan su suka shiga ba babu irin tambayar da baayi masa akan dalilin yin hakan ba Sam yaki fadi a cewarsa zai rufa mata Asiri, nanfa iyayan shi suka hau fushi dashi harta kai saida kanin Malam liman ya tarke shi duk yanda yaso ya gujema abun ya gagara kowa shi ake bama laifi itako banda kukan munafunci babu abunda takeyi inda ta dage akan bata masa komai ba, dayaga ba sarki sai Allah hakanan ya warware ma kanin babanta duk abunda ke faruwa inda abun ya daure masa kai sosai koda aka gayama iyayan ta Sam kin yarda sukayi a cewarsu za'a bata Ma diyarsu suna dama ba Santa yakeyi ba yaxo ne ya tozarta su Mamarta rantsuwa tayi saitayi shari'a da Ahmad babu yanda Malam liman baiyi ba akan abar maganar ina ta shafa ma idonta toka saida takai Kara police station inda aka tasa keyar Ahmad nan aka fara sabon case Wanda koda halima taji yana maida jawabin abunda yafaru kallon shi taita yi batace komai ba dakyar kanan Malam liman ya roka aka rufe case din a cewarsa koda anje kotu tozarci zai Zama a wurin diyarsu ko itace da gskia za'a bata Mata suna ne inda Ahmad kuma yace sai anyi sha'riar da gaskiyar Sa, dakyar aka rufe maganar kowani sashi na zagin dayan sashin inda iyayan halima keta lallashin ta Malam liman harda mata rubutun dangana ganin yanda tasa abun a Ranta basusan kawai basaja take masu ba, mahuta kuwa yafi kowa farinciki da hakan inda yakara riketa gamgam.

Wasan bera da mage aka shiga yi Aisha da AK tunda ya ganta tana rawa take gujema duk hanyar dazai hadata dashi
Tun rananda AK yaga Aisha cikin karamin 3quater da farar vest fa hankalin maza ya tashi, hmmm jiya ba yauba koba komai shekaru sunja duk yanda yaso yakice abun a Ranshi hakan ya faskara inda ko rufe idonshi yayi toh surar jikin Aisha kawai yake gani tana juya kugu tana rawa kamar zata karye Anya akwai mace mai irin zubin halittar Aisha kuwa? Idan ya tuno da shafaffan cikin ta da kirjin ta haka zaita juye juye akan gado tun yana daurewa har saida yayi jinya ciwon ciki mai matukar azaba ya turnike shi dakyar yasha saida yayi sati biyu tareda taimakon maganin da aka Dora shi akai inda likitan shi yabashi shawara akan yakusa halaka kanshi bakomai ke damun Shiva sai muguwar Sha'awa bakaramin takaicin likitan Yaji ba inda ya karyata hakan mai zaisa Yaji sha'awa? Toh Sha'awar wama zaiji? Cikeda mamaki likitan ke kallon shi, 'yallabai amma kanada iyali koh? Ya Tambaye shi, shiru ma Amsa ne yatashi ya cikama rigarsa iska.
Chapter 18 · 0% Book details