← Book details Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 40

Sashe 16

Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakaramin rikitata gidan nata yayi ba ko'a duniyar mafarki bata taba gani da zuwa irin gidan nan Wanda harya gaji da haduwa ba bare kuma ace nata ne, ooh Allah kenan Dare daya yakanyi Bature, da Addu'a ta shiga gidan kamar yanda Ramata ta umarce ta, wani sanyi AC neya ratsa su yayinda gogan ke kwance nashe nashe yana shan madarar shanu mai kyau cikin kwanciyar hankali yake kallon American movie dinshi sanye da kananan kayan shan iska su matukar yimai kyau, mikewa yayi tareda gaishe da daddy cikin fa'raa da murna kamar bashi ba, shi kanshi daddy yayi mutukar mamakin sauyin AK, kodai ya dangana ne? Inji daddy, idan ma bai dangana ba dole zaiyi kuwa, a zuciyar shi yake fadi yayinda AK da Aisha ke zaune a kasa daddy nakan kujera, nasiha yayi musu mai shiga jiki tun bare AK yaita tausasa shi har saidaga karshe yatashi ya Mike tareda kallon Aisha, 'zan aiko miki da waya na tambayi mamarku tace bakida waya zansa miki number na a ciki, zan dinga jin yanayin zaman naku ko kallon banza yaimiki Wanda zuciyar ki bata amince dashi ba kiyi gaggawan sanar dani, Allah yaimiki Albarka yabaku zu'ri'a dayyiba, kaikuma ina jiranka ka aiko min da gawarta domin yanzu mun Riga Munsa kafar wando daya ni dakai, 'subhanallah daddy Dan Allah kayi hakuri nayi nadamar abunda naimuku kaida Mamie insha Allah babu Wanda zaiji kanmu katayani ba Mamie hakuri idan an kwana biyu zamuzo sai in Kara bata hakurin, cikin jin dadi Dady yace, 'a'a kuyi zaman ku kada kaje ko'ina ku huta Sannan kuzo, fita daddy yayi yayinda AK yatafi mai rakiya, tunda suka fita takara gyara mayafin kanta a cewarta angon ta ne zai yaye mata kamar yanda akeyi a Al'adance, shiko AK tun shigowar ta parlon turaren ta yagama susuta shi wani irin turare ne wannan? Kai waya bata? Gskia kamshin shi yamasa jiki a mace ya shiga parlon.

*Mrs Sadik Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

20

Tanajin motsin shigowar Sa takara natsuwa dakin shiya wuce kai tsaye Kota kanta baibi ba, inda shiru shiru babu ango babu labarin Ango kafarta harta fara tsamin gajiyar Zama gawata yinwa datake ji rabonta da abinci tun rana saboda zumudi batama wani ci sosai ba a cewarta yau zataci kazar amarci, har karfe sha'daya darabi shiru tana zaune a wuri daya inda sai a lokacin hankalinta yakara tashi toh kodai ya manta an kawo mishi Amaryar sane? Gashi taga yakara mata wani masifar kyau dukda ta cikin mayafi ta kalle shi, shiko gogan yana kwance nashe nashe akan gado sai chatting yakeyi a Facebook tareda frnds dinshi hankali kwance inda kamshin turaran ta daya shaka duk yabi ya hanashi sukuni, tsaki yaja a karo ba adadi tareda mikewa, gskia dole in nema matar mutunci in Aura mutum shi kadai kullum Ga Sha'awa hakurina yafara karewa shekara talatin da biyu ba wasa ba, ya furta parlon ya wuce ta inda ya dinga bin wutan gidan yana kashe wa haryazo kanna parlon, kashe kayan kallo yayi harya kashe wutan parlon ta Mike ganin baisan da halittar taba, 'Yaya AK, tafadi cikin hanzari ta Mike,Yaya..tasamu kanta dajin nauyin shi inda lokaci daya ya tsaya yana Kare mata kallo hadeda kunna wutan parlon, 'ya akayi? Menene? Jarabarki ta motsa ne?? Ooooh ba haka kikai tsammani bako? Kin saba jin namiji kwance akan cinyarki wace irin Amarya ce wannan? Banda iskanci harkin fara nema na uwar mai zan miki Wanda ba'a taba miki ba? Look bari in kankara miki warning na farko yafadi yana nunata da yatsa, nidai ba mazinaci bane asalima ko yatsar Wata macen ban taba rikewa ba ma'ana ni tsarkakekke ne tas Alhmdlh, sannan ni bantaba cin diyar Wata ba, duk Randa kika Kara mun magana kiyi kuka da kanki kada kisake kiyima kanki wani kallo na daban a cikin gidan nan, kisama ranki kinzo a lokacin bayi, rayuwar bauta zakiyi idan nace miki yar'aiki toh kinsamu promotion, noooo noooo ke baiwace black monkey kawai wawiya mazinaciya mai fuska biyu simi simi kamar mutuniyar Arziki idonshi harya fara rinewa yayinda Aisha kafarta Sam takasa daukarta hawaye daya nabin dayan jikinta na wani irin rawa yayinda zufa yagama wanke ta dukda sanyin AC, takowa yayi har gabanta murmushi kwance akan fuskar shi wuyanta ya shako hadeda dago kanta yana mata kallon kiyayyah, congratulations na tayaki murnar samun namiji Irina Wanda babu kamarsa amma kamar yanda zaki fara ganin babu kamana a mugunta, congratulations daga rana tayau kunyi bankwana da farinciki a duniyar ki, ina tayaki murnar sabuwar rayuwar bauta, kakari tafara cikeda azaba nan yayi wurgi da ita kan glass cup dinda yagama shan fresh milk bakaramin bugewa tayi a kanta ba, juyawa yayi sannan yakara dawowa, 'Akwai mai gadi na dattijon Aziki ina neman Alfarman kada ki bata tsohon mutane domin mijin marigayiya ne ance kefa jarabar taki har tsofaffi baki bari ba, kiyimun Alfarma iskancin ki ya tsaya a waje banda yan aikina wlh wlh zan iya kashe ki har lahira Randa na kamaki dawani a gidan nan, sannan inada masu bama flowers ruwa damai wanke mun mota, congratulations a dalilin ki kinsa sun rasa aikin su bazan barki da gattin samari masu jini a Jika a cikin gida ba kamar naba kura Ajiyar nama ne, 'kanshi yadaga Alamar yana tunani chan yadawo ya tsuguna yadago fuskarta da hawaye yagama wankewa, 'bazan taba baki damar kizama karuwar gida ba kada kazantar zunibin kiya halakamu baki daya, idan jarabar kita motsa kinsan inda zaki GA kwartayan ki, Wuceta yayi hadeda rufe bedroom dinshi harda Sa mukulli a cewarshi kada taimasa fyade tunda ankawo ta cikin maza babu abunda bazata iya ba.

Anan ta kwanta kanta dukya kulle tarasa abun yi inda sai wurin biyun Dare ta Mike taci kuka harta gode Allah taita shiga sauran dakunan harta gane dakin ta saboda ganin hadaddun akwatunan lefen ta, komai na dakin dark purple ne yayi matukar kyau amma Sam bai burge taba Yanzu dama ba Auran soyya tayi ba? Mai AK ke nufi?? Dukda taji matukar takaicin abunda yaimata amma soyyar shi nanan daram dam a zuciyar ta.

Tun daga ranar tafara aikin bauta a gidan, AK ya kori matasa masu gyara gidan a cewarsa ankawo kura cikin garkin nama kudin sallama yabasu sosai nan aikin gidan yadawo kanta mace da wankin mota harda gyaran flowers idan tatashi tun asuba bata Kara komawa bcci, idanko tayi lattin wanke mai mota ranar hmmm bakaramin duka zata Shaba, idan yadawo ya taddata tana bcci kuwa ruwan sanyi mai kankara zai dinga watsa mata tijara iri iri babu Wanda bata gani ba nan tasa mai suna *farin mugu na* ta tsani AK amma a iya bakin ta, kullum muguwar kaunarshi ke samun masauki a Ranta duk yanda tayi kokarin fito na fito da zuciyarta abun yaci tura, Babu Wanda yasan halinda take ciki sai bilki itama ranan tazo gidan ta taradda Aisha da AK a kitchen inda yayi fatali da indomie Wanda shine yasata dafa mai a cewarsa kanme zata dafa mai haka babu kifin gwangwani shiba matsiyaci bane shida kudin shi aita masa mugunta akan abincin dayake siyowa, batada aikin yi saidai taci ta cika Masai da kashi mai wari sai uban kiba datake narkawa a kugu,ana haka bilki ta shigo indai Ranta yai mugun baci har saida ta tanka mai, 'karya kakeyi ka kiramu da matsiyata tunda munada wadatar zuci sannan kashin ma ni'ema ce mutum yace shi baya kashi mana sai uban takama da iyayin Gayu kamar kaidin baka kashi...... Rufe mata baki Aisha tayi inda bilki ta dinga ruwan masifa, AK kuwa baibi ta kanta ba a cewarsa ita ba sa'ar yinsa bace wacce tasata ita zata girbe mata abunda tasata ta shuka mai, Aikuwa bilki taita masifa ta wanke Aisha Tass inda Aisha taita bata hakuri akan kada a gayama Ramata da garbati dakyar bilki ta yanda saboda rashin lafiyar da Ramatan keyi akai akai tun bayan Rasuwar babansu kullum yau ciwo gobe lafiya.

Haka AK da Aisha ke Rayuwa har ayau shekara Uku da Auransa, dawowa gida yayi da yamma misalin karfe biyar kamshin girkin Aisha dukya cika gidan tun a tsakar gida yabude kofofin hancin shi tareda shakar kamshin abincin daya gama Kara masa yinwar Sa dukda bayacin girkin nata sai idan taimasa shida Abokanan Sa Wanda saita jera abinci kala biyar duk ita kadai a cewarsa kada ta kuskura taba wani yaimasa girki tunda ya taba taradda bilki tana tayata ranan tasha azaba wai ana jagwalgwala masa abincin daya kashe kudi akai, dukda baci yakeyi ba saida ya gasa ta, 'Shigowa parlon yayi daidai da daukewar farin cikin daya dawo gidan dashi dalilin wakan da take rerawa mai matukar dadin gaske cikin muryarta mai sanyi da zaki yaji tana cewa.

'AK ne Raayina
"AK sona yakeyi yana bala'en jidani,.
" na rubuta sunan AK akasa ruwa aka goge wlh kosun goge basu goge sanshi a zuciya ba.......ido biyun da sukayi baki sake batasan sanda ta tsuguna tana bashi hakuri harga Allah batasan yadawo ba cikin mamakin Sa ya juya yatafi a ranar baimata komai ba, a cewar Sa hukuncin Laifin ta zai iya kashe ta saboda hakoran bakinta ya kamata ya banbare a cewarsa kada yafara kisa akanta shiyasa ya kyale ta saboda bata taba bata masa rai irin na ranar ba wai AK Santa yakeyi yana ba'laen jida ita kalmar Nance tafi komai kona masa rai inda Yaji Aishar tagama cutar dashi.

*Cigaban labari*

Leemah ce zaune gaban Malam liman yana shaida mata wani matashi anan bayan unguwar su yazo ya same shi akan yana Santa da Aure inda Malam liman yace bazai ma diyarsa dole ba amma yaje ya nemi soyyar ta yabashi izini, sanar mata yayi akan zatayi bako daga yau zai dinga zuwa da yamma saboda bayasan tadin Dare su daidaita idan yamata toh idan baimata ba kada ta cuci kanta babu mai mata dole, Amincewa tayi lokaci daya tun bataga bakon nata ba ta amince zata iya Auran shi saboda wani kudiri Wanda ita kadai tasan abunda ke ran nata.

*Mrs Saddiq Rumah 💅🏻*
[11/7, 11:43 PM] ANTY JM D ILYA: 🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?*🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

21
Chapter 16 · 0% Book details