← Book details Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 40

Sashe 30

Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daki takoma tareda saka katon hijab tare suka fitoda AK kai tsaye kan kujera ya nufa inda Aisha tabude ma doctor kofa cikeda gaisuwa gaba daya suka karasa parlon yayinda suka zauna, 'doctor sonake ka diba jinina aje a auna sannan ka diba jinin Yar'iskan chan, yafadi tareda nuna dakin leemah shima a auna inasan inga results da gaggawa please, batareda bata lokaci ba likita yayi abunda aka umarceshi inda Aisha ta nuna mishi dakinda leemah ke ciki kememe taki yarda a diba jininta babu yanda doctor baiyi ba, cikeda takaici AK yashiga dakin nan yaita ball da ita kamar yasamu kwallo yanayi yana zaginta dakyar Doctor ya kwaci leemah a hannun Sa inda Aisha na gefe daya tareda kallon fadan dayafi karfin ta, daga ummm sai uhmuhm kawai take cewa hakura leemah tayi ganin AK zai halakata daga daran jiya zuwa yau tunda take a duniya bata taba ganin Wanda akaima dukan mutuwa irin wannan ba gashi yau anmata kuka takeyi tana jamasa Allah ya'isa kasa kasa inda sai ihu takeyi ya kala mata sharri ya cire mata budurci Ga azabar budurcin daya cire mata Ga zafin ciwo damai zataji ga bugu ya akai yasan ba budurwa bace indai shima ba danawa yakeyi ba, a fusace yakara dosar dakin inda Aisha ta tareshi Abun yafara bata dariya ma, 'Ubanwa ya cire miki budurcin? Lallai yarinyar nan ki kalla tsabar idona ki raina mun hankali zanyi maganinki karyar rashin mutuncin kikeyi, Jan kafarta takeyi tareda dauko hijab da sauri da sauri ta wuce ta gefen Aisha sotake tabar gidan tun kafun doctor yadawo ta tabbata kashe ta kawai zaiyi idan yasan tana dauke da ciki, AK na ankare da ita wani wawan Mari ya Kara zabga mata Wanda yayi sanadiyyar toshe kunnanta saida taga taurari na yawo a sama dif kakeji tayi shame shame a kasan parlon kukanma yaki fitowa sai nishi takeyi Tareda danasanin Kaddarar dataja mata Auran AK bata tabajin labarin mugu irinshi ba baida imani ko kadan, Zaune suke zuru zuru kamar masu zaman makoki leemah na yashe a kasa, kitchen Aisha ta nufa ganin Dramar da akeyi da matarso a gidan nasu bamai karewa bane Hadaddan shayi ta hada tareda katon burodi da soyyan kwai, parlon takoma harda kunna TV tana karyawa tana kallo dukda ana neman karfe bakwai na safe ne ko karabin takansu batayi ba indata hade Ranta sama da kasa AK kuwa sai Satan kallon ta yakeyi ganin yanda take saka lomar burodi batareda wani damuwa ba ko alamar tayi babu dukda Kota mishi baci zaiyi ba, zaune suke a wurin Doctor yadawo tareda mikama AK sakamakon gwajin, hannu ya mikama AK tareda fadin, *Congratulations sir your wife is Three month pregnant.*
'Kallan shi AK keyi yakasa fahimtar abunda yake nufi inda doctor ya maida hannunshi daya gajida mikawa, What? Yimun magana da Hausa yanda zan fahimce abunda kake cewa likita, 'yalla'bai ina nufin Matarka Nada shigan cikin Wata Uku a takaice, 'wyyooooo ni halima wlh fyade akaimun.......'wait wait wai ciki? Ai kowa Nada ciki AK ya furta yana zare ido cikin tashin hankali, "yes sir kowa Nada ciki but nata na mutum ne Mai rai, Bby na Rayuwa a ciki harna tsawon Wata uk...... Kam bala'e what a ina? A gidana? Matata? Amarya? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, ya dinga maimaitawa babu Adadi Aisha kuwa kashe TV tayi tausayin shi dukya mamaye ta bakaramin firgita maganar taimata ba bata taba tunanin leemah zatayi haka ba, rarrafawa leemah tayi har wurin kafar AK dake zaune a kasa yayi zaman yan'bori rike kafarshi tayi da hannu biyu biyu, Kaimun Rai ka rufamin Asiri kamar yanda Allah ya rufama Wlh fyade akaimun mijina na tuba nabi Allah kuma nabika kallonta yakeyi cikeda kyama yama rasa mai zaiyi ya zaiyi? Taya zaifara? Dagayin First 9yt sai ace Amarya Nada cikin Wata Uku, tana nufin da cikin wani tazo gidanshi kenan kuma tasan da cikin ta Aureshi, hawaye daya nabin daya ya kalla doctor, 'yah kanjamau fa? Akwai ko babu? 'Alhmdlh babu wani ciwo tareda ku dukanku likita yafadi cikeda Al'ajabin abunda yake gani, shigowar mai'gadi neya katse musu shirun inda yake shaidawa wani yazo neman hajiya Amarya damai gidan a cewarsa yanada Ajiyar mutum sukutum a gidan, mahuta neya danno kanshi sanye da kananan kaya bakake wando da Riga fuskarshi daukeda murmushi inda yake shafa sajen dake fuskarshi, Halima gidan hutu dakin hutu diyar malamai mai tarin ilimin hutu a daki, ooops forgive my manners please, Assalamu Alaikum banyi sallama ba kasancewar ina cikeda murnar ganin unborn bby Dina dake kwance a dakin hutu, Mutuwar zaune limah tayi........mmmaaaa...huta tafadi cikin rawar murya, mai kakeyi a gidannan? Ya zakaimun haka? Waya kawoka waya nunama gidana? 'Sorry baby Sanin inda kike bamai wahala bane kawayanki suka kawoni yanzu haka nabarsu a mota Sunce ma in gaishe ki su meenah nake nufi, 'Malam uban waye kai? Maiya shigo dakai har cikin gidana wurin iyalina da izinin wa kato dakai? Calm down Yalla'bai Kwantar da hankalinka zanma bayanin kaina ai, sunana mahuta Saurayin halima uban babyn dake kwance cikin mahaifarta nazo ne inga lafiyar bby na jiya nakwana da zullumin cikina Allah yasa kuna ciyar dashi sosai,.......... karfin da baisan yanada shiba ya tattaro tareda kaima mahuta mugun naushi a baki nanda nan jini ya balle duka yake kai mishi tareda Alkawarin kashe shi da hannun shi, kwarto kwarto har gidana wlh dukanku mai rabani daku sai Allah babu yanda Mai'gadi da doctor basuyi ba ina sunkasa raba AK a jikin mahuta Wanda akaima jini da majina a fuska sai zare ido yakeyi dukya galabaita baitaba tunanin zai riske haka ba saida AK ya cire mishi hakori daya dakyar yasha inda yakwasa a 360 babu koh waige lallai AK baida hankali yayi dana'sanin zuwa gidannan Kan leemah ya dosa wacce tayi hanyar waje tana dingisa Kafa dakyar da sunan guduwa kiran mahuta takeyi ya taimaka ya rike mata hannu su gudu tare tabbas AK babu abunda zai Hana bai kashe su ba, ganin AK ya dosota kamar zaki tuni ta taka kafa tareda kwasa ana Kare har waje yabisu tuni mahuta yaja mota leemah kuwa ta kule tanata tikar gudu babu ko takalmi bare mayafi ko waige batayi, nishi yakeyi sama sama tareda kokawa da numfashin Sa kafun a Ankara tuni ya zube a kasa ihu Aisha tasaki hadeda kiran sunanshi tana kuka da taimakon likita suka sashi a motar likitan Aisha da Ak na baya kanshi akan cinyarta sai girgizashi takeyi, kada ka tafi idan katafi basuda asara ni sukaima asara ya zanyi Yaya AK kafi kowa sanin kaine farincikina Dan Allah ka kasance dani wlh bazan gujeka ba koda zaka dinga dukana kada ka mutu, kwantar da hankalinki madam bazai mutuba insha Allah inji Doctor daketa zuba gudu a titi, Kai tsaye dakin Emergency akayi dashi Dakyar aka Hana Aisha shiga wacce tagaji dacin kuka harta gaji.

"Baki na bude ni Mamie ganin yanda Aisha ta bankeni harsai Dana kai kasa a kokarina nabinsu Asibiti domin dauko muku rihoto inaji ina gani aka badeni da kura suka barni tsaye nida baba mai'gadi, kokarin shiga gidan nakeyi tsawa mai'gadi ya dakamun, 'toh uwar gulma masu gidan basanan mai zaki musu a gida kuma?Sakata yasa yabarni cikeda takaici na watsar da Alkalamina nayi cikin fushi 'muma mijinnan munada shi bare a karya mishi ni a banza😡da gudu nayi wurin My Rumah🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀naga kowa nashi yasani.

*Mrs Saddiq Rumah 💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

34

Bakaramin artabu akasha wurin daidaituwar numfashin nasa inda saida aka kwasa mintuna mai yawa sannan Aka samu nasarar numfashin Sa Kiran su Mamie Aisha tayi tana kuka ta shaida musu suna asibiti batareda bata lokaci ba Mamie da Daddy harda Abdulhakeem suka rankayo Auta bilki ma ba'a barta a baya ba Ramata kuwa cewa tayi zatazo da yamma duba jikin nashi, aikin lallashi bilki ta shigayi inda Aisha ke makale jikin Mamie yayinda take musu bayanin iya abunda tasani salati suka dauka gaba daya daddy na girgiza kanshi cikin takaici, maganin shi kenan ai duk Wanda baijin Maganar iyayanshi taya yake tunanin ganin mai kyau a rayuwar Sa yara ana nuna muku gabas kuna yamma tafi kyau Wanda baiyi sharar masallaci ba wlh harta tasha zaiyi ina amfanin irin wannan? "Haba Alhaji haba Alhaji kadaina yin furucin nan shin bawa na wuce kaddarar sane? Mudauki haka akan shine jarabawarsa Saimu rakashi da Addu'a tareda nasarar cinyewa, tausasa daddy Mamie keyi ganin yanda Abun yaimasa ciwo sosai ita kanta Mamie tausayin dan'nata neya gama rufeta doctor neya katse musu jimamin da sukeyi yana share zufa da farin hankacif cikeda gaisuwa yake sanarda daddy akan zaiyi mgn dashi a Office inda hali, binshi daddy yayi nan likita yafara bayani, " duk mai imani yakamata ya tausayama AK halinda yake ciki Wanda komai yafaru akan idona saidai muce Alhmdlh Allah ya takaita munyi iyakar kokarinmu wurin dawoda numfashinsa dake kokawa sanadiyyar bakin cikin dayake ciki Wanda zuciyarsa tafara kumbura da taimakon ubangiji tunda bayin mu bane Alhmdlh komai yana shirin dawowa daidai Dan Allah Alhaji arage bata masa rai kassncewar Sa mai zurfin cikin gaske shiyasa Ciwon yayi saurin tasiri a gareshi yanada damuwa tattare dashi ku taimaka mana dashi kanshi wurin kwantar masa da hankali tareda dauwamar da murmushi a gareshi, godiya daddy yayi cikeda tausayin AK.

Tunda mahuta ya figi mota bai zame ko'ina ba sai gidan iyayanshi inda tun'da mai'gadi ya bude mishi kofa ya watsama su meenah kallon banza wadanda suke cikeda gulmar sanjin abunda yafaru amma ganinshi a halin nan yasasu tsuke bakinsu dukda ba hakan sukaso ba amma ko banza sun huce haushi tunda sunsan bakaramin bomb Aka tadar a gidanba tabbas yakuma tashida dakin hutu.......uwar mai kukemun a mota kananan yan'iska ko bina gidan iyayena zakuyin? Jiki na rawa ganin yana shirin huce haushi akansu suka shafama kansu lfy inda Meenah ta leko da kanta ta windon motar, "dan Allah kabamu na mota wlh bamu fitoda jaka ba.......idan banci ubanda ya haifeku ba shege nake, kokarin bude motarshi yakeyi a kufule tuni suka kama gabansu ganin yana shirin musu tijara da sanyin safiya suna tafiya suna tikar dariyar murna harda hawayan farinciki inda basuda burin daya wuce na ganin leemah tareda sanin halinda take ciki.
Chapter 30 · 0% Book details