← Book details Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 40

Sashe 39

Ustaziyya Ko Er Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Leemah ce keta mutsu mutsu gwanin ban tausayi dukta bushe ta jeme tayi baki tarame ga uban ciki, tun tana daurewa tana nishi da kuka kasa kasa harta galabaita ita kadai a daki da Alama nakuda takeyi bakaramin wahala tasha ba taci kuka harta gode Allah yayinda mama batasan Abunda ke faruwa ba kasancewar bata shiga harkarta gaba daya, Addua takeyi Allah ya dauki ranta kozata huta da azabar da take ciki inda takasa jurewa ta kwallama Maman kira cikin kukan azaba tana rokon yafiyar iyayan nata tareda nadamar abunda ta aikata, cikin hanzari mamar ta karasa dakin saida ta tausayama halinda taga diyar tata bakaramin azaba take sha'ba, wurin malam ta garzaya tareda amso rubutun nakuda Wanda yadade a ajiye, dakyar tasamu halima yasha kadan saboda tanasha tana dawoda rubutun ne ganin anata Abu daya har yanzu babu Alamar haihuwa hakan yasa malam ya dauko shatan keke napep aka sakata a ciki batasan inda kanta yakeba Allah ya taimaka unguwar babu mutane a lokacin babu Wanda ya farga da abunda ke faruwa, cikin ikon Allah Ana gafda isa asibitin halima tasaki wani uban ihu Wanda harta Mai napep din saida ya tsorata batareda bata lokaci ba Ashe yaron ne yayi mugun karata inda jariri ya sumbulo kasa salati mama tasaki ganin kashi jaga jaga a wurin da gudu likitoci suka karasa tareda gadon daukan Mara lafiya duk mai imanin dake wurin saida ya zubar mata da hawaye sakamakon karantan da jaririn yayi harya shafan mata wurin kashi,kai tsaye dakin tiyata akayi hanzarin shiga da ita inda mama keta kukan tausayin diyar tata bata taba ganin Abu irin wannan ba, katotuwar baby gal ta Haifa kyakyawan gaske Mai kamada ubanta sak kamar mahuta yayi kaki saidai bbyn farace tas, anyi ankin cikeda nasara saidai Halima tasamu larurar yoyan fitsari inda sai a hankali A hankali zata warke tareda shawarwari masu kyau daga likitoci hakan yasa suke zaune a asibitin tana jinya inda Malam yace tana samun sauki zataje Kano ta karasa jinyar gidan babban wanta saboda gudun surutun jama'a wadanda basuda gadonka Amma sunada gadon maganarka, Allah sarki halima bakaramin nadama tayi ba kullum batada aiki sai neman yafiyar iyayanta da Ubangiji a cewarta sakamakon zinar datayi ne take girba tun ba'aje ko'ina ba.

Mahuta uban duniya shida yammatan shi su meenah da finah kuwa kowa shagalinsa yakeyi suna holewa inda baa iyakar junansu kawai suka tsaya ba duk Wanda ya taya saisun bashi yammatan biyu kuwa meenah da feenah likafa ta cigaba domin yanzu har lesbianism sukeyi "Subhanallah" hakan yasa lokaci daya kuraje masu matukar wari da uban kaikayi suka Addabe suda wari da kaikayi tun abun nayi kadan kadan harya fara wuce hankali idan suka fara Susan jikinsu har saisun jima kansu ciwo ko'a gaban waye kuwa idan yafara musu saisun Sosa hakan yasa abokan iskancin nasu suka fara guduwa ganin yanda warin ke damunsu ga kurajan sun fara rashewa saboda uban Susan da sukesha hakan yasa meenah da feenah zuwa asibiti domin ganin wani kwararan likita ganin yanda ki Bcci sun daina samu saboda azabar susa su kansu warin jikinsu damunsu yakeyi, gwajin farko aka shaida musu dukansu su biyun suna daukeda cutar ciwon sanyi tareda hepatitis wacce tayi mugun tasiri a jikinsu bugu da Kari ga Infection daya mamaye su, fadin irin tashin hankalin da suka shiga bata baki ne atake akaba kowacce Gado inda suka fara Amsar kulawar da batada amfani sai uban kudi da suke kashewa, ganin abun bana karewa bane yasa suka sanarda mahuta saboda kudin hannunsu kaf yakare a magani da kudin asibiti inda batareda bata lokaci ba yazo ganin halinda suke ciki yama fisu shiga tashin hankali baiyi kasa a guiwa ba a lokacin yaje domin tantance jininsa cikeda tashin hankali da Adduar Allah ya kubutar dashi, "hmm su mahuta kenan Ashe ka Iya Add'ua, ya manta da Ubangijin sa na lokaci Mai tsawo ganin yana cikin tsanani shiyasa ya tuna Allah Wanda shi Allah ba'a masa wayau da dabara gwajin farko aka sanar dashi ya kira iyayansa domin bazaa Iya nuna masa sakamakon gwajin nashi ba saida wani babban jigon shi,babu yanda baiyi ba Kiri Kiri likitan yace saiya kira wani na jikinsa Babba, ganin babu mafita yasa yakira sanata da mommy inda cikeda tashin hankali suka karaso asibitin tareda uban bodyguard sai jiniya ke tashi a asibitin saikace shugaban kasa ne yazo, ganin result din kai tsaye sanata ya yanke jiki ya fadi Wanda hakan yayi sanadiyyar shanyewar barin dama na jikinsa gaba daya mommy ma baa barta a baya ba saida ta suma inda mahuta ke tsaye kamar mutum mutumi yakasa ko motsi sai hawayan dake bin idonshi.

Awani madaidaicin gida na Hango Hajiya Ramata da Alhaji Garbati Wanda ake shirin Auransa nanda wata biyu masu zuwa inda Ak yajashi jikinshi sosai tareda dorashi a wani sashi na kasuwancin shi, Alhmdlh kuma Garbati ya shiga da kafar dama kasancewar samai rikon gskia da amana inda AK ya siyan musu karamin gida Mai matukar kyau tareda daki hudu da sunan Aisha anan gaban unguwansu kadan inda dakyar suka koma saida Aishar tasa baki sannan dakyar Ramata ta yarda inda AK ya biyama Mai'unguwa kujerar umara adalilin Adalcin sa uwa uba shine Wanda yafara masu Eeashar sa sutura a garin Kaduna Wanda yabaka muhallin zama fiyeda shekaru masu yawa bakaramin masoyin ka bane kuma uwa uba mutumin bai taba goranta maka ba, Murna wurin mai'unguwa baa magana ganin shima yanzu za'a fara kiransa da Alhaji mai'unguwa matsayi akan matsayi inda Aisha bataje hajji ba sakamakon yanayin da take ciki a yanzu Mamie ce taje a madadin Aishar.
Aisha nagani zaune a kujerar parlor tareda katotan ciki a gabanta ta kumbura hancin nan yayi double fuskarta ya ciko sosai kafanta nakan cinyar AK Wanda keta tsokanarta yana kiranta da sabon sunanta " Orobo Maman iyabo"kukan sha'gwaba take masa tareda Alkawarin zata gayama mamien ta

*Mr's Saddiq Rumah*💅🏻
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie.*

*His Smile😌OMG, paradise💞 Alhmdlh for having u in my life, u are a great blessing from Allah SWA. I want you in my arm's, in my drmz, in Reality and in fantasy, U have Always been supportive My dearest hubby may Allah protect,👏🏻 Bless,👏🏻 Guide👏🏻 and prolong ur life for us👏🏻MAI'NI.*

*Dedicated to sister Husna.*

43

*END*

Shirye shiryen bikin Auta bilki akeyi babu sassauci tareda Angonta Abdulhakeem inda babu Wanda yakai Alhaji Muktar farinciki Mamie kuwa bakinta yaki rufuwa da murnar samun Nagartttun sirikai mata daga gidan mutunci marasa San abun duniya inda Hajiya Aisha tafi kowa murnar ganin yar'uwarta kuma kanwarta Kawarta sannan Aminiyar ta wacce batada kamarta zata Aura kanin mijinta inda taita godema Allah hidima akeyi bana wasa ba, Lefen leemah da Ak yayi Shiya kai aka chanza masa wasu daga cikin kayan tareda Kara masa da sababbin yayi inda aka chanza duka setin Akwatin kasancewar a wurin Abokin kasuwancin shi dama ya siya kayan ba'a wani sha wahalar gyara Lefen ba, Kaninshi yaba gaba daya kayan a cewarsa shine gudunmawar sa na bikin Hmm zokaga murna da gulma a unguwa masu kishi nayi masu bakin ciki nayi wasu har'cewa sukeyi asiri su Ramata sukayi saboda mallake iyalan Gidan Alhaji Muktar inda munafukai suka fara kananan maganganu irinsu Virus harda tunoda rayuwar Aisha nabaya, Ak baiyi kasa a guiwa ba inda aka tasa keyar virus magarkama a dalilin batancin sunan daya dade yanama su Aisha wasa wasa maganar saida taje kotu inda dama burin Ak kenan yanaso ya wanke Matarshi da marigayi sirikinshi daga karshe da wuya yayi wuya Virus ya warware duk kullin dayayi ma Aishar harda sharrin dayayi akan yaga ya'u da diyarsa na zina harda niyyan fyaden da sukaso yima Aisha Allah bai basu nasara ba, nan Ak ya bude Babban murya tareda shedama Duniya Matarshi Tsarkakkiya ce shine namiji na farko kuma na karshe a rayuwar ta nan kotu ta wanke Aisha tsaf daga zargin da ake mata, murna wurin Aisha kuwa baa magana Virus kuwa Tara aka cishi tareda horo Mai tsanani na tsawon shekara uku a gidan yari saboda samun shida laifuka masu yawa da akayi.

*A'gurguje*
*Bayan shekara Goma.*

Shekara hudu kenan da Rasuwar mahuta inda ciwo Mai karya garkuwan jiki yayi Ajalinsa wato *HIV* Wanda yasha jinya Mai tsawo cikeda nadama tun kafun ya rasu ya nema Alfarmar Amso mishi yarinyar sa a hannun leemah wacce Malam Babba ke rikewa yayinda leemah ta auri wani magidanci Mai mata uku itace cikon ta hudu ba laifi yanada rufin asiri suna zaune a garin Kano tareda yaronta daya wanda yaci sunan malam liman, Bakaramin soyyah iyayan mahuta kema Zainab ba diyar mahuta, saboda tausayi da soyyar da sukema mahuta ganin yanda suka hanashi tarbiyyah harda sakacin sune yakara jefa shi a rayuwar dayayi nadama ce sukayi Mara amfani domin mahuta tuni ya rigamu gidan gskia saidai muce Allah ya gafarta masa mukuma ya kyautata karshan mu👏🏻.
Chapter 39 · 0% Book details